← Book details Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 59

Sashe 54

Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi guda idanunsa suka sauya launi,sunansa dayaji inno ta kira ne yasa shi dawowa hayyacinsa ya dago dakansa a hnkli yana kallonta, kallonsa take sosai tana fahimtar sauyawarsa murya a hnkli tace" me aka rubuta a jikin jaridar" jirin ya soma ji yana dibarsa cikin dabara yyi saurin neman saman turmi ya zauna yq kalli inno yace" shi wannan wani dan sarki ne a nahiyar larabawa wannan kuma mai kama da khadija matarsa ce" saurin kallonsa inno sai kuma ta amshi jaridar tana kuma kallon jaridar tace" kace shi wannan balaraben dan sarki ne kuma ita wannan matarsa ce?" daga mata kai, tace" amma ita wannan din tayi kama sosai da qanwarka khadija shiyasa na ajiye jaridar nace zan nuna mk yanzu daka ce wannan din dan sarki ne daga nahiyar larabawa kuma wannan din matarsa ce nasan ta bakin malam ne ba qanwarka bace wannan yanayin su ne dai daya, ina khadija ina auren dan sarki kuma jinsin larabawa" lamido shiru dai kawai yyi shima zuciyarsa taqi amincewa wannan macen bimbii ce, kallon inno yyi da sauri yace" ina sauran shafikan jaridar suke ina son krt cikakken labarin ne kodan albarkacin wannan mai kama da qanwata" inno tace" kayy,ashha wallah iya wannan shafin dake dauke da hoton kawai na cire na zuba qosai a sauran shafikan" miqa hannu yyi ya kuma amsar wannan shafin yana qara kallon hoton,zuciyarsa na kuma dokawa amma har yanzu yaqi barin zuciyarsa ta aminta wannan bimbii ce taya ma hk zata faru, dayake jaridar ba cikakkiya bace babu cikakken labarinsu saidai kawai highlights, inno komawa tayi gindin murhu tana hura wutar da zata dora tuwon dare don magriba ta soma kunno kai, ninke jaridar yyi ya cusata cikin aljihun wandonsa ya miqe yace" inno ni zan wuce gdn yadikko" dago dakai tayi tana kallonsa tace" haba mn baka tsayawa kaci tuwon dare kafin ka tafi can din" murmushi yyi yace" karki damu zan shigo bayan isha'I" tace" toh shikenan saika shigo din ka gaida mutan gdn" yace" zasu ji" fita yyi duk jikinsa wani irin tunanin hoton wannan mace dake wan ga jarida yake kamarsu da bimbii har ta 6aci saidai kawai wannan tana da hasken fata fiye da bimbii" duk da wannan tunanin dayake still zuciyarsa na gauraye da shakku da kuma tarin rudani kan wannan abu hk, tafe yake yana zancen zucci har ya qarasa gdn mahaifiyarsa yadikko, qiris ya rage yaci karo da dattijo wato mahaifinsa, fitowarsa kenan daga cikin gd hannunsa riqe da buta zeyi alwala don ana gab da kiran sallar magriba, sauri yin qasa yyi ya gaida mahaifin nasa, kallonsa dattijo yyi sosai don yanyinsa ya tabbatar masa kamar ba daidai yake ba amma be masa mgn kan hkn ba sai ya amsa gaisuwar kawai ya tsuguna ya soma alwala, miqewa lamido yyi shima ya shige cikin gd don dauko buta ya gabatar da nasa alwalan, tare da dattijo suka tafi wuce masallaci, ranar komai cikin sanyi yake don zuciyarsa ta kasa dena kawo masa tunani 2kala..........

***

Washegari bimbii ta shirya ita da yaranta sunyi masifar kyau da kwalliya kalar birgewa, israt, khulood da sumayya dukkaninsu suna riqe da ammar,adeel da areef tare da rakiyar wasu bayin nata suka take mata baya zuwa yankin sarauniya don ranar sarauniya take gudanar da biki na musamman kan title din da masarauta tayi mata na *UMMU BURHAM* bimbii ta shirya tsaf don halartar wannan qasaitaccen taro da aka shirya wanda ya qunshi manya jiqaqqun mutane dake taqama da izzar sarautar masarautar burham har ma da baqi na musamman mariyatul qifdiya na daya daga ciki,
duk ta inda suka qetare cikin wannan gd bayi zubewa qasa suke suna miqa gaisuwa gareta sai ta wuce suke miqewa,kunsan dai salon takunta mai yanayi da na qasaita a hk ta qarasa yankin sarauniya tare da tawagarta, suna zuwa wajen babban hall din taron, bayin dake tsaron kofa sukayi saurin wangale musu kofa suka taka cikin qasaitacce dakin taron, jinin izza kowa na zaune kan mazaunin alfarma bimbii ta shiga bayi uku na take mata baya dukkaninsu riqe da babies a cikin fararen towels sauren bayin nata kuma sun dakata daga kofa, tunda bimbii ta shiga wurin kowa yyi tsit tamkar sarki dakansa ne ya shigo,prince dake daga kujerun sama kusa da mahaifiyarsa sanye yake cikin wasu fararen kaya rawaninsa ma fari qal hatta takalmin kafarsa mai kafar half cover fari ne, qure bimbii yyi da idanu sbd wani kyau da haiba data qara masa ita yake gani ta haske dukkanin wurin don shikam idanunsa basu gane masa macen data darata kyau ba, ita kanta sarauniya bimbii ta birgeta tuni taji tana alfahari da ita cikin taron, ita kuwa gimbiya mariyatul qifdiya ta kasa dauke idanunta kan bimbii kawai kallonta take har bayinta suka gyara mata wurin zama ta zauna, gimbiya hindu kuwa mamaki bimbii take yadda taga tayi tamkar daman can tayi gadon sarauta ne komai nata cike da izzah tamkar ba jinin bayi ba, ramlatul aswat kuwa dake tare da gimbiya mariyatu? qamewa tayi a tsaye sbd tsantsar mamakin bimbii a wannan masarauta kuma a matsayi mai girma na matar babban prince, ita dai tasan bimbii a matsayin baiwar data tura turakar jira daga baya kuma hadiman gdn yaseer bin walid suka tafi da ita kan gudajjiyar baiwa ce, toh meke faruwa ne? tmbyr data yiwa kanta kenan ta qara kallon 6angaren da bimbii ke hakimce cike da mamaki da daurewar kai, bimbii ita kanta tasan akwai tarin yan adawanta a wannan wuri hknne yasa ita take nuna cikar izza yadda ya kamata sbd ta basu abun fada, aikuwa kam ta raba musu abun fada, a hk taro ya soma amitattun hadiman dake wurin suka soma raba abubuwan sha cikin hadiman dake dawainiyya a wannan wuri har da lenah tsohuwar baiwa ga babban prince, daukan abun sha tayi a wani faranti na alfarma ta haura tudun da prince ke zaune a wata qasaitacciya kujera ta ajiye farantin a saman hadadden table din dake gabansa tana shirin tsiyaya masa ruwan inibin a qaramin cup yyi saurin daga mata hannu alamar ta ajiye taje, daidai lkcin suka hada idanu da gimbiyarsa ya kashe mata ido tare da mata inkiya ta qaraso tayi aikinta don itace komai nasa, tuni ta ankara da abunda yake nufi, qoqarin miqewa tayi sumayya tayi saurin gyara mata mayafinta, tashin nata sai ya kuma janyo idanu kanta, bata damu da idanun dake kanta ba ta soma takawa taku irin na qasaita da cikar izza koda ta fitar da prince dinta kunya har ta soma hawa steps ta wuce inda prince ke hakimce, tunkan ta qaraso yake murmushi har ta qarasa, rissinar dakai tayi a gabansa sannan ta sunkuyawa ta soma tsiyaya masa ruwan inibi a cup din ta sanya hannu biyu tare da rissinar dakanta qasa ta miqa masa cup din hannu ya miqa ya hada cup din da hannunta ya riqe tayi saurin janye hannunta sbd kar su wuce gona da iri a gaban suruka, ita tasan wani abu wai kunyar idon suruka sukam basu san shi ba, sake riqo hannunta yyi yana gyara mata mayafi, bimbii ji tayi tamkar ta nutse a wurin don kunya sbd prince ya gama bata kunya, jikinta ya bata kowa kallonsu yake, bata ankara ba taji ya miqe ya matso kusa da inda take ya manna mata light kiss a goshinta sannan ya koma ya zauna, yadda yaga ta rissinar dakanta yasan kunya taji shikam ko a jikinsa, toh meye don ya nunawa duniya abunda mutuqar so da qauna, dakyar bimbii ta iya sauka daga step din, sumayya dake tsaye ta take mata baya ta koma mazauninta, wasu dake wurin tuni sukaji soyayyar nasu ta birgesu suka soma tafawa a hnkli kuma sai dukka wurin ya dauki tafi, murmushi sosai sarauniya mar'atussaliha tayi sbd ba prince kadai bimbii ta fidda kunya ba har da ita kanta bimbii ta fiddata kunya ta nuna izza yadda ya kamata irinta ta jinin sarautar burham,fuskarta ta cika da annuri, idanunta ne yakai kan ummu nana ta saci jiki ta fita, da ido ta yiwa wata baiwa alama tayi hanzari bin bayan ummu nana,hk taron nan ya gudana wasu zucciyoyi fal da farin ciki wasu kuma suna cike da baqin ciki, gimbiya mariyatul qifdiya tayi dana sanin halartar wannan taro, jin zuciyarta take tamkar zata fashe ga wani azababben kishi dake taso mata tamkar zeyi ajalinta, bayan kammala taron ne ta wuce masaukinta kanta har wani juyawa yake, a gabanta mutumin da take yiwa haukar so yyi kissing wata mace cike da farin ciki da annushuwa wanda ita bata ta6a ganin hk tattare dashi ba, ashe prince ze iya yin hk ga mace amma ita magana ma dakyar yake mata dukda kasancewarta jinin sarauta amma sai gashi ita bata samu hk daga gare shi sai wata qasqantacciyar baiwa mara asali da tushe, tana ciki ramlatul aswat ta shigo ta durgusa gabanta tace" ranki ya dade wato nikam akwai abunda ya bani mamaki a wannan masarauta" kallonta gimbiya mariyatul qifdiya tayi fuskarta ba annuri ko kada tace" kiyimin mgn kai tsaye" sake rissinar dakai ramlatul aswat tayi tace"game da wannan uwar izzar dana gani yau a matsayin mata ga wannar dan sarki ba wata bace wannan face qasqantacciyar baiwa wacce na tura turakar jira" saurin tashi zaune gimbiya mariyatu tayi tana kallon ramlatul aswat tace" kina nufin kice baiwar masarautar abu ansar ce ita" tace" tabbas babu qarya cikin zance na itace wacce suwaiba ta za6a ta tura ga wannan dan sarki lkcin daya kai ziyara masarautar abu ansar" cike da tsagwaron mamaki gimbiya mariyatu ke kallon ramlatul aswat, kai tsaye ramlatul aswat ta labarta mata yadda akayi bimbii tabar masarautar abu ansar, shiru mariyatul qifdiya tayi tana auna lamarin don gano bakin zaren, kallon ramlatul aswat tayi da sauri tace" ina son kiyimin cikakken bincike kan al'amarin wannan mace" kada kai tayi alamar amsar umarni, daga mata hannu tayi ta miqe cikin sauri ta fita ita kuma ta dulmiya cikin kogin tunanin......

Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqatar krtw ki tura #300 ta wannan acct..0100790419, alhaji shahida nasir,union bank, saiki turon da screenshrt na payment naki ta wannan layi...07041195806.....Idan da buqatar kira ga layin kira

08036598141
Chapter 54 · 0% Book details