Sashe 31
Daren Goma Sha Hudu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sati biyu kenan da 6acewar bimbii daga masarautar burham dayawa sun mance da batunta idan aka dauke prince akbar da duk wayewar garin duniya sai ya fita neman bimbii ya gama zaga gari ya dawo babu labari, daga qarshe kawai ya soma bin duk wata kasuwa ta saida bayi, duk kasuwar daya shiga hk zaka ga masu cinikin bayi na binsa da gudu suna masa tallan bayi ko za'a samu irin wadanda yakeso, idan ya qarewa bayin kallo be ga wacce yake nema ba sai yyi gaba abinshi, babban hadiminsa ubaid na take masa baya domin idan zeyi irin wannan fitar ta sirri baya fitowa da sauran masu tsaron lfyrshi, ubaid shine na hannun damansa ya bashi daman sanin dukkanin sirrinshi sbd ya yarda dashi dari bisa dari dashi kadai yake fitowa, ubaid yana mutuqar tausayin prince yadda yaga ya zurfafa kan soyayyar wannan baiwa wanda tabbas yasan hkn na iya kawo fitina ba qarama ba cikin gdn sarautar burham, ranar ma hk suka koma gd babu wani kyakykyawan labari, bayan yyi wanka ya zauna ya zurfafa tunani kan wannan abu daya faru, nasarar gudu ga bawan dake masarautar burham ba abu ne mai sauqi ba sbd tsatstsauran matakan tsaro ta kowacce kofa,idan kuwa hkne taya bimbii har ta samu nasarar tserewa batare da kowa daga cikin dakarin dake tsaron kofa sun ankara ba,sunkuyar dakansa yyi yana tunani sosai don gani yake kamar da akwai lauje ciki nad'I cikin wannan abu, kiran ubaid yyi dake bakin kofa a dogare, shigowa yyi da sauri ya iso gabansa tare da rissinar dakansa qasa, dago idanunsa yyi da suke jaji dasu tamkar yyi kuka ya kalli ubaid yace" kaje kayimin bincike na musamman kan yadda abun ya faru" ko be nemi qarin haske ba yasan me prince ke nufi, rissinar dakansa yyi alamar amsar umarni, daga masa hannu prince yyi sannan ya fice don aiwatar da abunda aka umarce shi, yana ganin ya fita ya maida kansa ya kwantar jikin kujera dayake zaune,lenah ce ta shigo hannunta riqe da qaramin basket na kayan marmari taje kan table dake gabansa ta ajiye, ta fito da yar qaramar wuqa ta dauki tuffa daya tayi slicing dinta gida hudu tana daukan slice daya daga cikin yankan tana miqa masa idan yaci saita qara masa wani,slices biyu kawai yaci ya daga mata hannu alamar ya isa hk, daukan basket din tayi ta fita dashi sannan ta dawo taci uwar kwalliya tamkar wacce zata gasar sarauniyar kyau, sanye take cikin wata abaya fara sol ta rufe ko'ina na cikinta amma bakinta yadau jan janbaki sai daukar idanu yake abunku da farar fata, gashi ta tsayar da eye lashes na idanunta hkn yasa gashin idanun nata yyi duhu, kafarta bbu takalmi don daman ba'a shiga 6angaren nasa da takalmi, tunda ta shiga yake kallonta amma a zahiri gixo take masa sai yake mata kallo da bimbii, ita kuma ganin yana kallonta sai tayi zaton ta yaudaro hnklinsa kanta ne, murmushi tayi ta wuce kan royal bed nasa ta hau ta zauna tana jiran ya gama abunda yake ya hawo ita kuma ta soma mishi tausa daga nan ta qure basira da hikimarta ko Allah ze bata sa'a prince ya amshi budurcinta daren yau, prince kuwa ya jima yana 2karancensa sannan ya taso ya nufo gadon yahau, yanayin kwanciyar da yyi kawai ya nuna mata baya buqatar komai daga gareta, duk bayin dake masa hidima sun san alamomin mgnrsa koda be furta komai ba idan yyi wata alamar suna gane abunda yake nufi, idan yana son tausa ze kwanta ya juyo bayansa idan kuma ba hk ba toh tsakanin biyu za'ayi daya ko ki tafi ko kuma dai yana buqatar wani abun daban, itama yanzu tana ganin ya kwanta fuskarsa na kallon sama taja gefe sai kuma taga ya daga mata hannu, jikinta a mugun sanyaye ta sakko daga gadon ta sake masa curtains din dake kame gefe gefen kusurwar sannan ta juya a hnkli ta soma tfy har ta fice, 6angaren bimbii kuwa Izuwa yanzu ta gama jigatuwa, abinci sau guda kawai ake basu ga ciwo dake cinta a hnkli amma cikin masu tsaron wannan kurku babu wanda ya kalleta bare tasa ran zasu bata magani, qishirwa kawai ze iya kar mutum cikin wannan wuri don kusan kullum ma sai an fitar da fursunonin da suka mace a dakunansu, su kuwa masu tsaron wannan kurku zuciyarsu a bushe da rashin imani, hk zasu fito da gawarwakin mutanen da wahala ta kashesu su zubasu cikin keken doki aje a watsasu a babban kogi ruwa ya tafi dasu, dayake zuciyar tasu babu ko digon imani basu dauki ran mutum bakin komai ba, bimbii zazza6ine sosai yake wujijjigata kwana biyu amma babu yasan tanayi iyakarsu da furnoni shine duk safiyya su miqa musu abinci a wani qaramin akushi sai ruwa a wani cup na katako, hk zasu dauka suna ci tamkar mayu, bimbii tayi duhu ta lalace sai dogon hanci da manyan idanu da kuma dogon suman kanta daya hargitse ya sake fallasa tsantsar wahalar da take fuskanta, ruwan hawaye ya qare mata kawai kukan zucci take fama dashi da tafasar ruhi, burinta a yanzu shine mutuwa ta kawo mata ziyarar gaggawa, Allah kuma yasa qarshen wahalarta kenan, cikin dare ciwo ya tsananta mata sai murqususu take tana kakari sbd azaba ga gumi dake fama keto mata ta ko'ina, jan jikinta ta somayi har ta qarasa bakin kofa ta miqe zaune a hnkli tana buga kofar da hannunta ko zasu jiyota amma babu wanda ya jiyota har dan qarfin da yyi saura jikinta yyi qasa ta koma ta kwanta kawai, sai safiyya suka bude don ajiye mata abinci suka tarar da ita cikin wani irin yanayi na tsananin ciwo, fito da ita sukayi suka kaita wani babban daki da suka jibge masara lfy, daya daga cikin masu kula da marasa lfyn ana shigo da bimbii ta kalleta sannan ta koma tsaya bisa kanta, wasu yan 2kalle tayi kawai a jikin bimbii ta dago dakanta ta kalli wadanda suka shigo da ita tace" wannan sabuwa ce koh?" daga mata kai sukayi alamar ehh, tace"tana da aure ne?" duk suka kalli bimbii dake kwance a qasa gefe guda tana fama da ciwon dake dawainiyya da ita,dayan yace" gsky bamu sani ba ko tana da aure ko bata dashi" wani yace" ni ban san lkcin ma da aka kawota bare laifin data aikata" kallonta matar tayi tace" kina da shigar ciki shine ke wahal dake" bimbii na daga kwance a qasa ba lfy amma tana ji matar ta ambaci kalmar ciki tayi wani irin zabura ta miqe zaune ta kalleta tace" ciki?ciki kkce ina dashi?toh cikin uban wa?" tsabar rudewa yasata jero wadannan tmbyoyi tamkar wata zautacciya, matar bata kuma kallon inda take ba ta kalli wadanda suka shigo da ita cikin wurin tace" gsky bana jin tana da aure" cikin sauri suka juya suka fita, bimbii kuwa tana daga zaune ta dawo kamar wata mutum mutumi tunaninta ya tsaya chak, gbdy kwakwalwarta ta dakata da duty sbd tsabar dimaucewa da tayi, su kuwa wadanda da suka fita kai tsaye 6angaren azeez sukayi suka sanar dashi cewa an samu wata mai dauke da ciki cikin fursunoni mata amma basu tabbatar ko tana da aure ko bata da aure ba tinda su basu san lkcin da aka kawota ba ma,miqewa azeez yyi da hanzarinsa suka nufi wannan dakin da ake ajiye fursunoni marasa lfy, nuna masa inda bimbii ke zaune sukayi, qare bimbii kallo yyi tuni ya ganeta, mamaki ne sosai ya kamashi dalili kuwa yasan dai bimbii babbar baiwa ce ga prince akbar kuma kowa shaida ne prince akbar be ta6a kusantar kowacce daga cikin bayinsa sbd babu wacce har aka samu ta fito wankin budurci, idan kuwa hkne toh daga ina babbar baiwa guda ga dan sarki kuma jinin masarautar burham ta samo ciki,wannan lalle al'amari ne mai girman gaske don kowa tabbas kowanne cikakkiyar budurwa yake za6e kuma bayanshi babu mahalukin daya isa ya ratsa gonarshi ko ya kusanci baiwa ko karya kusanceta ita dai ta haramta ga kowa mutuqar ta taka wannan matsayi,yana gama wannan tunani ya juya ya fice batare daya furta uffan ba sbd duk wurin babu wanda yasan wacce bimbii ko kuma daga inda ta fito sbd abun sirri ne, shiyasa yana fita be tsaya ko'ina ba sai fadar sarauniya mar'atussaliha don sanar mata da wannan al'amari mai girman gaske, ummu nana ce tayi masa iso ya shiga yana shiga ya rissinar dakai gabanta yyi shiru yana shirin ta bashi umarnin yin mgn,ita kanta tayi mamakin ganin batare data nemi ganinshi ba hkn yasa ta soma tunanin ko wani ya fidda sirrinta ne, ummu nana ce ta sanar dashi sarauniyya ta bashi damar mgn, sai lkcin ya dago dakansa ya kalleta yace" ran wannan sarauniya ya dade nazo miki da wani babbar al'amari" kada masa kai tayi alamar tana sauraronsa, sake rissinar dakansa yyi yace" wannan baiwa da hukuncin daurinta yake kai tsaye daga fadarki an sameta da zaunannen ciki tare da ita" zumbur sarauniyya ta miqe tsaye tana nuna shi da yatsa a mutuqar fusace tace" wannan kuma qarya kk mutumin banza kawai, babbar baiwa ga babban prince a ina zata samu ciki, kowa ya shaida tun aka za6eta bata fito wankin budurci bare ace ya kusanceta koda ya kusanceta tayi ciki tabbas tana hukunci mai girma bare bai ma kusanceta toh idan kuwa a wani wurin ta samo ciki nayi rantsuwar da girman Allah saita gwammace mutuwarta da azabar da zata dandana don wannan tozarci ne ga jinin sarautar burham"...........
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqata zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,saiki turon da screenshrt ta wannan layi ...07041195806......
Alkalamin Bintuu ne...
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
25
*My days of deepest sorrow and pain*........heart full of fear💕💕
Littafin nan na kudi ne, idan kina da buqata zaki tura #300 ta wannan acct...0100790419,alhaji shahida nasir,union bank,saiki turon da screenshrt ta wannan layi ...07041195806......
Alkalamin Bintuu ne...
10/10/20, 1:12 AM - Anti qamshi🌷: *DAREN GOMA SHA HUD'U*🪔🪔
Written By Bintuu Seer
25
*My days of deepest sorrow and pain*........heart full of fear💕💕