← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 137

Sashe 98

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A daidai wasu jerin shagona ya parker Motar agefen titi, wayarsa ya fiddo ya kira wani mai suna Kb yace mashi yana waje, ba 6ata lokaci ya fito daga wani shago acikin jerin shagunan wurin wanda na d'inki ne kamar yadda aka rubuta asaman shagon, matashi ne yana sanye da jeans da t-shirt yana zuwa bakin Motar Haisam ya bud'e kopar ya fito, cike da girmamawa ya shiga gaisar dashi yana tambayar ya ibada, bayan ya amsa mashi ne ya bud'e back door na Motar ya fiddo wata leda wadda yasa aka ware kayan da za'a dinka ma Fatuu, da sauri Kb ya kai hannu ya kar6a ya bud'e ledan ya duba kafin ya d'ago ya tambayi wa za'ai ma dinkinne kuma wanne iri, gaya mashi yay suna tare kafin ya lek'a ta gaba yace ma Fatuu ta fito, bayan ta fito yace ma Kb suje ya dau measurement nata sai ta za6i styles da take so, amsa mashi yay da to kafin ya nufi shagon yana zuwa saitin Fatun yace ta biyo shi, maimakon ta bishin sai ta kalli Haisam a rude tace "Ya tafi da abubuwan fa" cikin nuna rashin fahimta yabi Kb d'in daya kusa shigewa shago da kallo kafin ya maido kallon kanta, tana ganin hakan ta fahimci bai gane abunda take nufi ba hakan yasa da sauri ta sake cewa "Abubuwan da aka saka ciki nike nufi" still bin ta yay da ido kafin ya bude baki yace "i don't get u" jin hakan yasa ta d'aga hannu tana kwatanta mashi abunda take nufi harda d'an nuna chest dinta, wani kallo yabita dashi mai kaman harara aikuwa da sauri ta sunkuyar da kanta kasa,
"Ki bishi" taji ya fada, juyawa tai sumi sumi ta nufi shagon haisam daya bita da ido yadan yi wani guntun Murmushi hadi da dan ta6e baki daga haka ya koma cikin Motar,

Tana shiga cikin shagon wanda babbane yana d'auke da manyan kekunan d'inki kala kala masu amfani da wuta Kb ya nuna mata plastic chair yace ta zauna, zaunawa tayi gaba d'aya hankalinta na akan ledar kayan tsoronta kar ace bras din na ciki, saida ya fiddo kayan ya duba taga babu su sannan ta samu natsuwa ta fara tunanin kilan suna acikin sauran kayan, wayarshi ya bata bayan ya bud'o mata inda styles suke yace ta za6i wanda za'ayi mata aikuwa hannu na rawa ta amsa ta fara dubawa, duk Wanda ta gani sai ta wuce bai yi mata ba can ta samu wadanda suka yi mata d'aya fitted gown d'aya kuma riga da skirt, koda ta nuna ma Kb d'in sai cewa yay ta dae sake wani wad'annan na Manyan yan mata ne ko kuma Amare aikuwa a harzuk'e tace ai itama yan matance, nan fa suka fara jayyaya har sauran yan shagon saida suka amshi wayar suka duba style d'in da ta za6an kowa ya duba sai yace da de ta canja, wani ma har shawara ya bata yace kayanta masu kyau ne kar ta lalata su amman ta nace ita dae su take so tunda ai a jikin mutane ta gansu sun sa lafiya lou balle ace wani zata lalata kayanta shidae Kb kafewa yay akan ta canja in ba haka ba zaije ya nuna ma yalla6ai Haisam, ganin taki canzawar yasashi nufar waje aikuwa zumbur ta mik'e tabi bayanshi suka nufi Motar sai faman wawwatsa hannuwa take tana fad'in ita da kayanta ba abunda take so zata za6a ba, suna isowa bakin Motar taja kopar ta bud'e lokacin ya d'age kanshi jikin headrest yana sauraron Radio, sauke kan yay ya kalleta ta Matuk'ar d'aure fuska tanata hura hanci,

"Miya faru" ya tambaya da kasalalliyar murya, hannu ta d'aga ta nuna mashi Kb dake gefe don shi baima ganshi ba, lek'o wajen yay ya zuro da k'afarshi guda ya kalli Kb d'in tambayarshi abunda ya faru yay, cike da girmamawa ya fara mashi bayani "Yalla6ai dama styles d'in data za6a ne naga kaman basu dace da ita ba don an fi yima Amare haka ko Manyan yan mata, ita in akayi mata karshe zasu takurata ne ma shine nace da ta canja wasu simple wanda zata mora sosae"
tun kafin Haisam yace wani abu ta amshe a tsiwace tace "ai dae nima yanzu yar Matance ko, zaka wani ce na Manyan yan Matane to an gaya maka nima yanzu yarinya ce..." tsit ta dakata da Maganar ta juya tana kallon haisam daya d'an k'ank'ance ido had'i da d'an d'age gira yana kallonta lokaci guda tasha jinin jikinta ta fara d'an sussunnar da kai tana mashi kallon kasan ido, wani guntun bazawarin Murmushi yay tana ganin hakan ta turo baki tana kyakkyafta ido,

"Kai mata wanda take so" ya fad'a ba tare daya kalli Kb d'in ba, kallonshi tai tayi mashi gwalo shidae Murmushi kawae yay yace suje ya dauki measurement dinta tabi bayanshi tanata surutai tana fad'in "ai daman nasan cewa zaiyi kayi man don duk abunda nike so yi man yake gashi nan ai kasha wahalar banza" ta k'arasa tana mashi dariya, girgiza kai kawae yay ba tare daya ce mata komai ba don ya fahimci rigimamma ce, bayan ya gwadata atare suka fito har yan shagon na mata sai anjima, suna isa ta bud'e Motar ta shige shi kuma ya zagaya wurin Haisam ya fad'i mashi an gama komae yace zasuyi Magana daga haka ya tashi motar, zuge glass Fatuu tayi tana jaddada mashi ya d'inka mata su suyi kyau kaman yadda na jikin matan data gani suke, cike da zolaya ya d'aga murya yace bazai mata irinsu ba zani jaka tsaye(zani single) da riga zai yi mata, atsiwace tace " Wllh in kayi man su sai ka biya ni kayana in ba haka ba a kaika gidan yariii" daga haka Motarsu tabar wurin shi kuma Kb ya nufi shagonsu yana dariya da alama shima d'an barkwanci ne, lokacin da ya koma shagon hiran rikicin Fatun suka cigaba da yi har Kb din na cewa shi abunda ma ya bashi mamaki da yarinyar irin hips din dake gareta duk da ba wani girma ne da ita ba, gaba daya suka tambayeshi measurement din hips din, da mamaki duk suka maimaita daya fad'i masu awon har wani na cewa kodae bai yi awon daidai ba yace wllh daidai awon yake don da farko ita yaba ta zagayo mashi da tape d'in kamar yadda suke yi in zasu auna chest da hips sai suba mai dinkin suce ya zagayo masu dashi, da ya duba awon sai ya kasa yarda hakan yasashi kama tape d'in ya auna da kanshi amman sai gashi same abu ya bashi, gaba daya suka jinjina kai wasu na fad'in hutu ne da cin kayan dadi kawae,
"Kunsan kuwa dangin Senator Ali zakee ce" Kb din ya fada,
"Haba nifa nayi mamakin ganin an kawo maka dinki a wannan lokacin kuma ka amsa kai da kace ka rufe amsar d'inki ashe babbar harka ce" wani dake yin d'inki cikin yan shagonne ya fad'i hakan, dariya Kb yay "ai kaima kasan har dinkin wasu sai in aje akan wannan, daga fa gidan uwar d'akina ne Hajiya Hauwa Zakee mai Alkhairin ban mamaki yake"

"Waye ya kawo dinkinne ko wannan wanda take aikowa miye ma sunanshi?" wani daban ya tambaya,
"Wai Tk, bashine ya kawo ba in shine ai shigowa zai yi jikinta ne Haisam dan Senator d'in" Kb ya bashi amsa,
"Kace Balaraben nan ne, kai gaskiya mutumin nan wllh yana mugun burgeni yasin, kaga mutum kaman shi yay kansa.....",

" ai in dae da irin wad'annan a gari to fa mu munshiga ukku wllh don mata ko kallon irinmu bazasu rink'a yi ba" wani da ya katse waccan ya fad'a aikuwa gaba daya suka kwashe da dariya suna fad'in shi damuwarshi kenan yace to ai gaskiya ya fada suna jin har maza yana burgewa inaga matan kuma, haka suka ci gaba da hiransu suna yin d'inki shi kam Kb fiddo kayan Fatun ma yay yace bari ma ya yanka su tun yanzu.

A daidai kopar gidansu ya parker Motar lokacin anata yin sallar Azahar a Masallacin gidan Hajiya, batare daya fita ba ya mik'a hannu baya ya janyo babbar ledar sauran kayan yace ta fita sai ta d'auka, bayan ta fitan ta saukko ledan k'asa wasu guda biyu marasa girma ya sake daukkowa a bayan ya mik'a mata mai d'auke da atampopi guda biyu yace taba Friend dinta da Mom nata sai mai guda d'ayan yace taba Grandma dinta, gyad'a mashi kai tayi alamar to tana ta bin shi da ido kaman akwae abunda take son fad'a, kallonta yay ya dan kwantar da kanshi ganin tayi mashi tsaye ya furta "any problem" kaman wadda aka zarewa lakka ta girgiza mashi kai alamar ba komae, tana niyyar rufe kopar Motar taji yace "check inside suna nan" da sauri ta juya ta kalleshi shima ita d'in yake kallo fuskanshi a sake kaman zaiyi Murmushi, turo baki tay tace "nifa ban tambayesu ba ai ko",
" kinji nace wani abu ne?" ya d'age mata gira, a hankali ta girgiza mashi kai alamar a'a,

"Owk kije" ya fad'a bayan ya d'ago yana k'okarin jan Motar,

"Ya Handsome" yaji ta kirashi a sanyaye, dakatawa yay ya kalleta ba tare daya amsa ba,
"Nagode, Allah ya saka da Alkhairi ya saka ka a Aljanna" ,"Ameen yar fillo" ya fad'a da dan Murmushi, har ta juya ta sake juyowa,
"Allah ya baka mata ta gari ta haifa maka yara masu kyau in rinka yi masu wasa ina kuma goya su" bud'a ido yay alamar mamaki hakan yasa ta kyalkyace da dariya ta rufo mashi kopar, baija Motar ba har saida ta kinkimi kayan ta shige sannan ya nufi gida,
Chapter 98 · 0% Book details