Sashe 113
Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
.......A nutse yake driving d'in yayin da Fatuu keta kallon gefen hanya ta 6angaren da take can ta juya ta kalli Haisam ta kira sunanshi, d'age mata gira yay idonshi akan hanya tace "ka kunna mana waka" shiru ya d'an yi kafin yace mata babu wakar,
"To a wayanka fa baka da wak'oki?"
"Ba wanda kike so" ya bata amsa a takaice,
"To ka kunna mana radio k'ilan suna yin wakokin" ba tare daya kalleta ba yace "baki iya kunnawa bane?" jin hakan yasa ta kai hannu ta kunna radio d'in don ta iya, jin ba'ayin wak'okin yasa ta canja wani gidan radion nan ma wani shiri sukeyi d'an tsoki ta ja a fili tace "duk ma basu yin wakokin" har ta koma ta zauna ta tuno da sabon gidan radion da aka bud'e wanda kullum cikin sa wak'oki suke, da sauri ta kai hannu ta kamo shi aikuwa sai gashi suna cikin yin wak'okin Umar m sharif ana gama wadda ake yi aka sako wakar zan rayu dake, Murmushi Fatun tayi ta fara bin wakar kai kace ita ta rairata, tana cikin bi ta juya ta kalli haisam dake driving tace "Ya Handsome muma atare zamu cigaba da rayuwa har mu Mutu ko?" d'an Murmushi yay ba tare daya kalleta ba bai kuma ce komai ba hakan yasa ta cigaba da cewa "kaga tunda kana da bangarenka agidan Hajiya in kayi aure sai akawo maka Matarka nan in ka tafi aiki sai in rink'a zuwa ina tayata fira in kuma ta haihu sai in rink'a goya babyn ina yi mashi wasa" sai lokacin ya juyo ya kalleta da Murmushi suka had'a ido yace "ke bazaki yi auren ba kenan?" tace "zanyi mana, amman fa sai nazama likita" jinjina kai yay "zamu rabu kenan tunda zaki aure kema" yay Maganar yayin da yake maida idonshi kan hanya, tace "ai lokacin na fara aiki sai in sayi gida anan unguwar ko kuma tunda gidan Hajiya akwae k'aton fili sai nima abani in gina kaman naka ba shikenan ba sai muci gaba da yin rayuwa atare" d'an ta6e baki yay hadi da jinjina kai sai kuma yace "kyauta za'a baki ki gina kenan",
"Sai na biya? Ta tambaya ta d'an waro ido, d'aga mata kai yay alamar eh tace "to sai in biya tunda lokacin na fara aiki shikenan kaga sai mu cigaba da rayuwa atare tunda muna gida d'aya ko?" kai ya d'aga mata ta koma ta jingina bayanta a jikin seat tana ci gaba da bin wakar da ake, basu dad'e ba suka k'arasa estate d'in da Abbas yake, a gaban gate d'in gidan ya dakata ya latsa horn sau biyo sai ga Abbas d'in ya lek'o yana ganinsu ya shiga idasa bud'e gate din, yana gama wage masu shi ya kutsa kan Motar ciki, can gefe inda Motar Abbas take fake ya nufa, yana parker Motar Fatuu ta bud'e ta fito tana ma Abbas Dariya, shima dariyarce akan Fuskarshi ya nufeta yana fad'in "u'r highly welcome Mom Zarah" still dariyar ce a fuskarta bata ce mashi komae ba adaidai lokacin Haisam ya bud'e Motar ya fito,nufarshi Abbas yayi ya mik'a mashi hannu suka gaisa yana k'ara yi mashi an dawo lafiya, hanyar shiga cikin gidan suka nufa yayi ma Fatuu alamar ta taho, suna zuwa bakin entrance d'in yaron Abbas wato Abdul ya fito da gudu yana sanye da jeans da t'shirt ya nufi haisam yana fad'in "Oyoyo Baba zakee" haisam na ganinshi ya ca6eshi had'i da d'aga shi sama suna ma juna dariya ya saka hannunshi cikin sumar haisam d'in yana cakud'ata, sauke shi yay yana fad'in in ya lalata mashi gashi sai ya gyarashi Abdul d'in yace Mommyn shi nada Comb da yawa sai ya gyara mashi gaba d'aya sukai dariya harda Fatuu dake ta binsu da ido tana mamakin yadda haisam kema yaron don batai tunanin yana ma yara wasa har haka ba, juyawa yay ya kalli Fatun irin kallon rashin sani kafin yace "Baba zakee wacece wannan?" d'an kallon Fatun yayi yace mashi "wata rigimamma ce" waro ido yay ya kalli haisam yace "rigimamma irina?" gaba d'aya suka sa dariya haisam d'in ya kai hannu yaja hancinshi yace "ashe kasan kai rigimamme ne" kafin ya bashi amsa sai ga Feenah ta fito tana sanye da doguwar riga A shape ta atamfa tayi daurin dankwali mai kyau, fara ce saidae ba irin tas d'innan ba tana da kyau ba laifi kuma doguwa ce sam bata da jiki kana kallonta zaka fahimci wayyayar yar boko ce kuma haskenta Abdul din ya d'aukko harma ya fita fari amman sak da babanshi yake kama,
"Ni dae na gaji da jiran bak'uwar tawa ta shigo na biyo sahu" ta fad'a idonta akan fatuu tana mata Murmushi itama Murmushin take mata kafin ta gaidata, bayan ta amsa tace su shigo mana duk suka nufi ciki wanda madaidaicin falo ne daka shiga yana d'auke da duk wani abu da akan samu a falon yan gayu masu matsakaicin k'arfi, kujera ta nuna ma fatun tace ta zauna shi kam haisam tuni ya zauna saman 3 seater sofa Abdul na akan cinyarshi Abbas ma ya zauna agefenshi, gaida Haisam din ta shiga yi tayi mashi anyi salla lafiya duk da da sallan tayi mashi ta waya, bayan sun gama gaisawa Abbas ya nuna mata fatuu yace "yau dae ga Mom Zarah" Murmushi Feenah tayi tace "aikam H,zakee ya kyauta man ai da ya kawo man ita inata jin labarin Mom d'inmu ba tare dana ganta ba" ita dae fatuu Murmushi kawae take, kallonta Abdul yayi kafin ya juya yace ma haisam "wai wacece wannan Baba zakee" kafin ya bashi amsa Abbas yace "Mom din shi ce" zaro ido yay yana bin fatuu da kallo itama kallonshi take tana Murmushi, d'aga kai yay ya kalli haisam yace "Wannan yar k'aramar ce mamanka?" kai ya d'aga mashi alamar eh da mamaki ya k'ara kallon fatun sai kuma yace "kodae matarka ce baba zakee" gaba d'aya suka sa dariya Abbas yace "wato tayi k'arama ta zama mamanshi kenan saidai matarshi ko, to sister d'inshi ce" dariya Abdul d'in yayi yace "kenan yayata ce ita?"
"Mamanka dae" Abbas ya bashi amsa, cike da rashin yarda yace "kam ni ba mamata bace wannan yar karamar ga mamata nan babba" Feenah dake dariya tace "zata iya zama mamanka mana,ba Hafsa mamanka bace itama kuma ai yar k'aramace ko" turo baki yay yace "ai ita mamata ce ta k'arya ko wannan ma ta k'arya ce?" ya tambaya yana nuna Fatuu, girgiza kai Abbas yayi yana dariya yace "No ka barta a yayar taka dai" mik'ewa Feenah tayi ta kawo masu abun sha ta zuba ma kowa kafin ta koma ta zauna suka shiga yar hira harda Haisam d'in, tambayar Abbas tayi ko a shirya table yace no ta bari sai sun dawo salla tunda lokaci ya kusa tace to, juyawa tayi ta kalli Fatuu dake ta faman binsu da ido bata cewa komae tace "wai dama Mom Zarah bata magana ne?" d'aga ido haisam yay ya kalli Fatun suka hada ido tayi Murmushi Abbas yace "Magana kai,kawae dai k'ilan bakunta take maki ne"
tace "Ah Mom Zarah kada muyi haka dake gaskiya,inata murna za'a kawo man ke musha fira kuma sai kizo ki man shiru alhalin kina magana" hannu tasa ta rufe bakinta tana dariya jin abunda Feenah din tace,
"Ba dariya zaki man ba bud'a baki zaki muyi fira" cire hannun tayi ta amsa mata da to, saukkowa Abdul yay daga kan cinyar Haisam yaje gaban fatuu yace "zo muje dakina kiga Computer d'ina da Baba zakee ya siyo man a k'asan waje" amsa mashi tayi da to ta mik'e zata bishi Feenah tace ta cire Abayar mana ta sha iska, sa6ule rigan tayi ta daurata kan kujera harda gyalen rigar ta bi bayanshi suka nufi wani Corridor, bin ta da ido sukae gaba d'aya har ta shige kafin Feenah ta juyo suka had'a ido da Abbas tayi dan Murmushi kawae don shima Murmushin yake yi, basu jima ba suka fito Fatuu na ruk'e da computer d'in Abdul na biye da ita, akan carpet ta ajeta duk suka zauna suka cigaba da yin game d'in da suka fara yi anan Feenah ta fara jin muryarta wurin yin gardama da Abdul sai kace wani tsaranta sudae dariya kawae suke yi masu, bayan wani lokaci ta fita daga game din ta shiga wani app na koyon karatu nan ta fara koya mashi da turanci sosae ta burge su Abbas don daga yadda take koya mashin zaka fahimci tana da k'ok'ari da abun ya nisa ma duk sai suka kwanta akan carpet, kiran sallan da aka fara ne yasa Abbas da Haisam mik'ewa don zuwa masallaci Haisam yace ma Abdul ya taso suje suyi salla,mik'ewa yay yana cema Fatun sai sun dawo ta d'aga hannu tana yi masu bye bye, bayan sun fita itama Feenah mik'ewa tayi tace ma Fatuu ta taso suje suma suyi sallar ta amsa mata da to, atare suka nufi Bedroom dinta taba Fatun hula tace ta rufe kanta kafin ta nuna mata toilet tace ta shiga tayo Alwala ita kuma ta nufi d'akin Abbas ta d'auro Alwalar, atare sukayi sallar suna gamawa Fatuu ta koma Falo ta cigaba da abunda take ita kuma Feenah tana fitowa Kitchen ta nufa don shirya abinci kan Table, Fatuu na hangota tana fitowa da kayan abinci ta mik'e taje tace bari ta taya ta suka cigaba da shirya table d'in suna cikin yi su Haisam suka dawo Abbas na hangota ya d'an d'aga murya yace "Mom Zarah an saki jiki kenan har ana taya Feenah aiki" ya yi Maganar yana dariya Feenah tace "aikuwa dae ta zama yar gida dama haka yakamata ai" Abbas d'in yace gaskiya yayin da yake zama kan kujera, bayan sun gama Feenah tace su taso table yazama ready Abdul ya fara rugowa ya zauna kusa da Fatuu don ita tuni ta zauna, atare suka nufo Dining area d'in da Haisam kowa yaja kujera ya zauna Feenah ta hau serving nasu bayan ta gama Abdul yace "kowa yayi Addu'a kada yaci da shedan" gaba d'aya suka jinjina kai suna dariya, a nutse suka fara cin abincin baka jin komae sai k'arar cokulla hankali kwance Fatuu ke tura abinci har ta k'ara abunda bai yi mata ba, Haisam ne ya fara mik'ewa alamar ya koshi Feenah ta d'aga kai ta kalleshi tace"badai wai har ka koshi ba?" kai ya d'aga mata alamar eh,
tace"amman fa baka ci wani na kirki ba, har yanzu dae kana nan da rashin cin Abincin ka kenan" d'an Murmushi yay ba tare daya ce komae ba ya fara kokarin barin wurin Abbas dake kallonshi yace "ki rabu dashi lokaci na zuwa da zai rink'a ci hannu baka hannu kwarya in har yana son samun kuzarin yin noma yadda ya kamata" shiru bai tanka mashi ba bai kuma kalleshi ba yabar wurin amman sarae yaji abunda yace ita kuwa Feenah d'an runtse ido tayi ta sadda kanta k'asa alamar kunya, kusan atare suka gama Abbas ya nufi parlor Feenah kuma ta fara clearing wurin tana cikin kwashe kayan abincin da su Abbas sukae amfani Fatuu ta mik'e alamar itama ta gama ta tambayeta ta tabbatar ta koshi tace mata eh, tayata gyara wurin tayi kafin ta nufi parlor wurin Abdul suka ci gaba da abunda suke a Computer dinshi su kuma su Haisam suna kallo a tv, duba agogo yayi ganin ukku tayi yace ma Abbas suje gidan Najeeb ya amsa masa da ok duk suka mik'e a tare har zasu nufi hanyar fita yace ma haisam "bazamu je da Mom zarah ba su gaisa" shiru yay mashi kaman bai jishi ba har saida ya k'ara Magana sannan ya amsa masa da No kawae daga haka ya fuce,dariya Abbas yayi dama tsokana ce yasa yayi mashi Maganar Fatun, saida ya lek'a Bedroom ya sanar ma feenah zasu je su dawo tayi mashi Allah ya tsare sannan ya dawo falon su Fatuu dai gaba d'aya hankalinsu na akan abunda suke hakan yasa ya fuce kawae. Bayan tafiyarsu ne Feenah ta fito tayi wanka ta canja kaya zuwa doguwar rigar Material ta zauna tana kallon abunda su Fatuu keyi in sukae abun dariya tayi in kuma wani yai gwaninta ta tafa mashi haka in suna gardama sai ta rabasu sosae ta saki jikinta daga baya ta koma kan kujera suka shiga yin fira da Feenah har sata tayi ta rink'a yi mata fullanci ta kuma bata labarin garinsu,