← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 137

Sashe 24

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani mutum ne ya shigo kwanar ta bayan Fatun yana zuwa saitin ta yace "Ke bake ki ka yada jaka bane? sam Fatuu bata lura da ba jakarta a hannunta ba,don bata cikin hayyacinta,d'agowa tayi ta kafe Mutumin da idanu tama kasa bashi amsa,ganin yanayinta,ga fararen idanunta sun rikid'e sunyi ja yasa Mutumin cewa"baki lafia ne? d'aga masa kai kawae Fatuu tayi alamar "eh,juyawa yayi ya d'aukko mata jakar ya dawo inda take tsaye yace "Muje" bata ce komae ba tabi bayanshi a hankali take tafiyar har suka fito suka hau hanya Mutumin yace"ina ne gidanku?" da yatsa Fatuu ta nuna mashi,
"to zaki iya k'arasawa?ya tambayeta,Kai ta k'ara dagawa,ya mik'a mata jakar yace "Allah ya sawak'e,ni ta can zan bi ne, ki bi a hankali ki k'arasa kinji" nan ma kan ta d'aga,Mutumin ya juya ya tafi, Ikon Allah wai yau Fatuu ce ta kasa magana,lalle ba karamin tashin hankali kalaman gaye suka jefa ta ba,
Lokacin da ta iso gida shagon Amadu a rufe yake,tana shiga zaure taga k'ofar dakinshi a bud'e,shigewa ciki kawai tayi, tana shiga ta wuce band'aki tayi fitsarin da tuni ya d'aure mata mara don har ya d'an zubo ma,tana fitowa ta shige ciki,a bakin k'ofar dakinta ta aje jakarta ta shige,bata bi takan gwaggo ba don tasan bata nan tunda safe ta sanar da ita cewa aikin rana take,amman zata fita da wuri don zasu je Walimar d'iyar abokiyar aikinsu da aka d'aura ma Aure jiya Asabar,daga can zasu wuce Aiki,
Can k'arshen d'an gadonta ta haye ta had'e kafafuwanta ta tura kanta ciki,tayi zuru tana ta tuna maganganun Gaye,
kwata kwata ta kasa yin tunanin Mafita,don tana ganin ba wata mafita tabbas abunda gaye yace sai ya faru,don kud'in gilashin da yawa ba zai yuwu Mutumin ya yafe ba, tunda gashi harma ya tambayi kwatancen gidansu,sai lokacin wasu kwalla masu zafi suka zubo mata don tun d'azun ta kasa ma yin kukan,wani irin d'aci take ji a bakinta,

Ta dau tsawon lokaci a haka, ta kasa ko kwanciya don komae bai yi mata dad'i,tana a haka har aka kira sallar Azahar,tana ji ana yin sallar amman ta kasa saukkowa daga gadon ga yunwa tana ji amman bata jin ma zata iya cin abinci,
Amadu ne ya shigo cikin gidan don d'ibar Abinci bayan ya dawo daga salla,ya hango jakar Fatu da takalmanta a bakin k'ofar daki a ranshi yace "Yanzun haka tana can tana baccin tsiya bata tashi tayi Sallah ba" ya nufi dakin Fatun ya d'age labulen,kafin yace wani abu Fatuu tayi zumbur ta d'ago,hawaye duk ya wanke mata fuska,ganin haka yasa Amadu shigowa cikin d'akin yana kallonta yace"Miya faru?" dakyar murya can ciki tace "ban lafia.." Amadu dake ta kallonta har ranshi ya yarda bata lapiyan don da ganin fuskarta ma,yace"mike damunki",
Tace"zazzabi da ciwon kai" yace"kinsha magani" girgixa masa kai tayi alamar "a'a"
"To ai ba kwanciya zaki yi kita wani kuka ba,ba kinsan inda Gwaggo ke aje magunguna ba sai ki d'auka kisha ko" har ya nufi k'ofa zai fita ya juyo yace "Kinci Abinci" tace "a'a" juyawa yayi ya fice,ba'a jima ba ya dawo,hannunshi rik'e da plate d'in abinci yace"saukko ki ci" aje mata yayi a k'asa ya sake fita,sai gashi ya sake dawowa da Cup d'in ruwa da magani Panadol,tsayawa yayi yana mata wani irin kallo ganin bata saukko ba yace "ba saukkowa nace kiyi bane,in ki ka ban haushi sai in kyale ki kiyi ta zama da ciwon..."
A hankali ta saukko cikin zuciyarta tana fad'in"in kayi hakuri ma daga yau ba sake ganina za kai ba" aje mata ruwa da maganin yayi ya nufi k'ofa yana fad'in "kafin in sake dawowa ki tabbatar kin cinye shi kinsha maganin"daga haka ya fice,
Tunda ya fita ta kafe abincin da idanu,ta zabga uban tagumi tana ta faman tunanin a ina za'a samu kudin shanu gomaaa a biya mutumin nan,ita dai bata so akaita gidan yarin nan,gashi Gaye yace wasu wahala ke kashesu acan....,Zuciyarta ce ta raya mata "ARD'O" dammm gaban Fatuu ya fad'i,lokaci guda kuma ta fashe da matsanancin kuka,a fili take fad'in "Shi kadai ne zai iya biyan wadannan kudin,amman nasan ko kashe ni za'ai a gabansa da kwarankwatsa ba zai biya ba...." a zuciyarta tace "to ko in fad'ama Kawu Amadu ne..."da sauri ta girgiza kai a fili ta sake cewa"kafin gwaggo ta dawo nasan ya karairaya ni, don dama shi ake sawa yana zaneni"haka dae Fatuu tayi ta tufka da warwara,k'arshe ta maida hankalinta kan Abincin wanda jallof din shinkafa da taliya ne,a hankali tasa hannu ta d'iba ta kai baki ta fara taunawa da kyar take hadiye abincin,tana yin loma ukku ta tsame hannunta,sam bata jin dad'in abincin,shima d'aci yake mata a baki,tayi zuru tana kallon shi don tana jin yunwa sosae,a ranta tace "dama tuwo Gwaggo tayi kilan in fi jin dad'in shi...."Wata zuciyar tace"A ina zaki k'ara ganin tuwon ma,dama kinci Abincin don daga yau shima ba sake ganinshi zaki ba sai dai ki rink'a ganin gabza" da sauri ta jawo Abincin ta shiga turawa a baki ba don dad'i ba.

Bayan ta cinye Abincin tana cikin shan Maganin Amadu ya d'aga labulen ganin ta cinye yace" Yauwa,yanxu sai kitashi ki yi sallah inkin gama sai ki kwanta,insha Allahu zaki ji kin wartsake",a hankali tace "toh" ta mik'e don yin sallar,
Bayan ta gama sallar ta d'aga hannuwa sai Addu'a take tana fadin,"Allah don Allah na rok'e ka kada kasa a kaini gidan yari,don Allah,don masoyinka Annabi Muhammadu kasa Mutumin ya manta da abunda ya faru kwata kwata,nayi maka Alkawari na daina rashin ji,zan zama kamar Haulatu....." haka tai ta rok'on Allah tana kuka har tagama ta tofe a hannuwanta ta shafa,A saman abun sallan ta kwanta ta takure jikinta tana ta ajiyar zuciya a haka bacci ya kwashe ta.
Bayan an kira Sallar la'asar Amadu yazo ya tada ta yace"ki tashi ki watsa ruwa kiyi Sallah,naji ruwan bokitin wurin wanke wanke nada d'umi sai ki d'ibe shi" kai ta daga masa kawae,ya juya ya fice.
Bayan ta gama sallar tayi zaune a wurin ta buga uban tagumi,ba laifi ta dan ji dad'in jikinta,tunani ta fara yi ko ta tafi islamiyya taje tagani in Haulat tazo ta fadi mata halin da take ciki...,d'an tsoki tayi a fili tace"koma na fad'a mata,ba abunda zata iya yi,karshe ma ta kama man nasihar banza,baccin lokaci ya rigada ya k'ure" can kuma wata zuciyar ta raya mata"ba gara kije ba,watakil dalilin zuwan Allah ya tausaya maki yasa a k'i zuwa kama ki,amman in kika zauna kina iya ganin anzo yanzu an tafi dake.." zumbur ta mik'e ta nufi yar wardrobe dinta ta ciro wasu kayan Islamiyyar tasa,
tunda ta nufo zaure take jin tashin kida a waje,Amadu ne ya kunna wakar india a shagonshi,a hankali take tafiyar don yadda take jin jikinta kaman ta tashi daga ciwo sam ba karfi,lokacin da ta fito waje ta girgiza kanta tace "Shi sam baida matsala,waka ma yake ji" hannu tasa ta share dan siririn hawayen da ya zubo mata a ido daya,tace"in sha Allahu nima indai Allah ya ku6utar dani ba ruwana da kowa" Allah sarki Fatuu har kin bani tausayi,sai dae Allah yasa ba tuban mazuru kike ba.
Amadu ya hangota zata wuce ya leko da kansa yace "zaki iya zuwa islamiyyar ne? tace "ehh naji nasamu sauki" yace "dan jira" miko mata biscuit pure bliss yayi da sweet guda biyu yace"Sai kin dawo,kibi a hankali" daga haka ya maida kanshi ciki yana ci gaba da bin wak'ar da yake saurare hadi da dan jujjuya kai,tafiya take tana ta kallon abunda Amadu ya bata tana mamaki wai yau ba tare da ta rok'e shi ba ya bata,ko ya zage ta kaman yadda yake mata inta tambaye shi,wani lokacin har rankwashinta yake kafin ya bata yace ita zata cinye masa jari,dan murmushin takaici tayi a fili tace "tabbas shima yaji a jikinshi ya kusa rabuwa dani" taci gaba da tafiya tana yi tana goge kwallan dake zubo mata da gefen hijab dinta.

Tunda ta zauna a aji kanta na k'asa,Haulat sai kallonta take tana nazarin yanayinta gashi akwae malami balle ta tambayeta abunda ke damunta,sam ta kasa natsuwa ganin kwalla na zubo ma Fatun tana sa hijab tana gogewa,tana sauraron bayanin malam dake masu Ahalari tana kuma satar kallon Fatuu,
"FATIMA MUHAMMAD ARDO" Malam ya kira sunan fatuu,sai dai sam bata ji shi ba, Haulat ta ta6o ta,lokacin yana k'ara kiran sunan,da sauri ta d'ago Manyan idanunta da su kayi ja ta kalle shi hadi da fad'in "labbaika...." tashi ki k'ara yi mana bayanin da nayi" Malam yace,tsuru tayi ta kafe sa da idanu,don bata san akan mi yayi bayanin ba,gaba daya ajin anyi tsit ana ta kallonta, Haulat ta d'an dukar da kanta murya can k'asa tana fadi mata bayanin da yayi,Fatuu ta saci kallonta sai dai sam bata san mi take cewa ba,
A fusace malam yace"ke muke saurare!" Fatuu ta dukar da kanta jin kwalla zata zubo mata,hakan ya kara fusata Malam din yace "fita kiba mutane wuri,tunda ba karatun kika zo dauka ba" ba musu ta nufi hanyar waje har lokacin kanta na k'asa,Malam yaci gaba da magana"don iskanci yara k'anana daku sai kuje kuyi samari,in kuka yi fad'a kuzo kuyi ta tunane-tunanen banza,in baku son karatun kuje kuce Aure kuke so mana" Sauran yan ajin suka sa dariya suna sussunna kai kasa alamun kunya banda Haulat da sam bata ji dad'in maganar da yayi ba,don tasan ba abunda ke damun Fatuu ba kenan,tabb ita da koda wasa akace ana sonta yanzu ta fara masifa da zage zage tana fadin ita bazata yi saurayi ba sai ta zama likita",haulat ta fada a ranta,ita kam Fatuu kallon Malam din tayi da runannun idanuwanta suka hada ido yace"ko zaki zo ki buge ni ne?" batace komae ba ta juya ta fice....

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

*BY ZAINAB LALUH📲*
~(Oummu Imam)~

*Paid Book*

*Free Page22⃣*
Chapter 24 · 0% Book details