← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 137

Sashe 95

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan wasu tsawon Mintuna sai gata ta fito gyalenta a hannu da gudu ta isa gaban Motar tasa hannu ta bud'e kopar gefen driver ta shige lokacin idanun Haisam na a lumshe,
"Ya Handsome!" ta kirashi da karfin gaske dama yaji shigowarta kawae dae bai kalleta bane, a hankali ya ware eyes dinshi akanta, cike da farinciki ta juya masha bayan kanta tana nuna mashi gashinta daya sha gyara ya sauka sosae don har ya kai tsakiyar bayanta da gani harda stretching akai mata sai faman salki gashin yake, gyara zaman shi yay sosae fuskarshi d'auke da murmushi ya furta "yayi kyau" washe baki tayi sam ta kasa Magana saboda tsabar murna sai faman janyo gashin take ta gaba, suna cikin hakan Maman Abdul d'in ta k'araso bakin Motar, Haisam na ganinta ya bud'e kopar tun kafin yace wani abu tana ta fara'a ta tambayeshi gashin yayi yadda yake so ya amsa mata da yayi kafin ya tambayi kudin service d'in da sauri tace komi ya bada yayi, ba tare da ya k'ara cewa komai ba ya koma cikin Motar, glove box ya bud'e ya k'irgo kudi dubu goma Fatuu nata binshi da ido ya juya ya fita, a rude ta karbi kud'in lokacin da ya mik'a mata har da d'an duk'awa, sosae ta shiga yi mashi godiya tana fad'in "Thank u sir, May Almighty Allah increases ur wealth, May God bless u....." sai faman duk'awa take don ita kanta tasan bawae kudin aikinta bane ya bata kawai kyauta ce yay mata, shi dae jinjina mata kai kawae yay ya koma cikin Motar, kafin ya rufe ta lek'a da fara'a tace ma Fatuu tana jiranta ta k'ara zuwa tunda yanzu tasan Dryer d'in bai cire kai, kai fatun ta d'aga mata kawae ta juya ta nufi shago tana yi masu bye bye, yana Niyyar tashin Motar yaga Fatun na k'okarin bud'e mota ta fita ya tambayi lafiya,
" zanje in daukko abunne",
"Wani abu?" ya tambaya cikin rashin fahimta,
"Shi abun yin, dryer sunanshi ko?"
Bin ta da ido yay kafin yace "is it ur own?"
" ai naga ka bata uban kudi ba siya kayi ba?" yar harara ya wurga mata ba tare da yace komai ba ya tashi Motar suka sauka kan titi yaja Motar suka tafi,

Tunda suka bar wurin ta kasa natsuwa acikin motar, gaba daya ta aje gyalen rigar ma sai faman d'oki take tana ta6a gashinta har hannu take kaiwa ta juyo da rearview mirror bayan wani lokaci sai yasa hannu ya juya shi yadda zai ga bayanshi, da taga yana juyashi sai ta sauke glass d'in kopar da take ta rink'a lek'a madubin wajen tana ta washe baki,

"Ki rufe shi ko wanda Grandpa d'inki yace sunyi maki fitsari su k'ara" taji ya fad'a ba tare daya kalleta ba, juyawa tayi ta kalleshi tana zare ido tace "Aljanu?" kai ya d'aga mata,
" To ai banda su fa, in ma inadasu yanzu sun tafi",
"In kinbar kan a bud'e ai zasu ga yayi kyau su dawo ko",

hannu tasa ta rufe baki sai kuma ta kai hannu da sauri ta d'auki gyalen rigarta tasa ta rufe glass d'in don dama Gwaggo na yawan ce mata in bata son rufe gashinta shed'anun Aljanu zasu hau mata su shige jikinta,

A daidai wata k'atuwar Plaza ya juya kan Motar ya shiga, can gefe guda ya parker Motar bayan ya kashe yace mata ta fito, wani katon shago mai d'auke da sunan Zee's Collection ya nufa tana biye dashi sai faman kalle kalle take, suna shiga wata wayayyar mata fara mai d'an jiki ba sosae ba kuma tana da dan tsawo jikinta sanye da bakar Jallabiya tayi rolling veil dinta ta nufo su da fara'a hakanne ya bayyana hakorin makkan dake bakinta,
" The Big CoE, U'r welcome" fuskarshi da d'an Murmushi ya furta "thanks Zee" hannu ta mik'a ta nuna masu 2 seater leather sofa dake a shagon wanda yake dankam da kaya su laces, Atampopi, Materials harda dinkakku wato ready-made da kayatattun dogayen riguna, nufar kujerar yay ya zauna ta maida kallonta kan Fatuu dake ta bin shagon da kallo tace "Beauty ave a seat" kallonta tayi sai lokacin ta gaidata da fara' a ta amsa mata tace ta zaune, acan gefen Haisam ta zauna,
"H,Zakee ya ibada" ta tambaya tana ta faman fara'a, "Alhamdulillah, Ya bussiness"
" Alhamdulillah gamu munata kokartawa" jinjina mata kai kawae yay,
Kallon Fatuu tayi tace "What's ur name?"
"Zaraah" ta bata amsa
"Sannu Fateema Zahra anata Azumi balle kisha ko ruwa" da sauri tace "ai banayi" d'an bud'a ido Zee tayi tace " bakya yi why?"
"Ai bai zamar man dole ba saboda ban...." cakk ta kasa k'arasawa ta juya tana kallon Haisam da ya dan kishingida ajikin kujeran, lokaci guda Zee ta fahimci abunda zata ce hakan yasa tayi d'an Murmushi tace "to amman dae kinayi ko?" d'aga mata kai tayi "Eh, inna yi biyu sai in huta kwana d'aya" jinjina kai tayi tace gud, juyawa tayi ta kwala ma wata Esther kira sai gata ta fito yar matashiya ce da bazata wuce shekara sha biyar ba kuma tun daga kan shigarta da sunanta zaka gane ba musulma bace, tana zuwa ta d'an rankwafa ta gaida haisam da turanci ita kau fatuu sakin baki tayi cike da al'ajabi tana kallonta, abunda ya d'aure mata kai shine ganin kanta a aske kwal ga ba d'an kunne hakan yasa da farko tayi tunanin namiji ne sai kuma idonta ya sauka kan kirjinta dake dauke da breasts, Umarnin amso cake da lemu ta bata awani shago ta nufi hanyar fita Fatuu ta bita da kallo baki sake tace "kai! Wannan Namijine ko mace, kodae irin tane mata maza!" duk atunaninta acikin zuciyarta ta fad'i hakan bata san a fili tayi ta ba,
Murmushi Zee tayi "ba Namiji bane Mace ne haka al'adansu yake" bin ta da ido kawae tayi lokacin esther d'in ta dawo ruke da leda mai dauke da abubuwan da kace ta amso, d'an durkusawa tayi taba zee tace mata ta kawo plate cikin inda ta fito ta koma sai gata ta dawo rike da plate d'in ta bata, fiddo cake d'in Zee tayi ta d'aura asaman plate d'in da lemun, da d'an Murmushi ta mik'a ma Fatuu ta amsa tace ta gode, a hannun kujera ta d'aura plate d'in ta fara ci bayan ta bud'e lemun, yar hira Zee suka ci gaba da yi da Haisam don kawarshi ce tare sukae Secondary school da ita sai dae ta d'an girmeshi, jefi jefi yake tanka mata Fatuu dai nata cin cake d'inta tana kurbar lemu, bayan wani lokaci ya duba wrist watch ganin lokaci ya tafi yace ma Zee ta duba mata kayan da sukae Magana ta amsa mashi da to kafin ta kalli Fatuu tace mata tayi sauri tazo ta za6i kaya, jin hakan yasa tai saurin tura sauran cake din gaba daya ta kwankwad'e lemun da sauri ta mik'e tace ta gama, Zee na murmushi ta mik'e suka nufi bangaren laces tace mata ta zabi wanda yay mata nan fa Fatuu ta zaro idanu tana tsuke baki ta fara bin kayan da kallo zee dae na tsaye agefe tana Murmushi,
"Should i help u?" girgiza mata kai tayi tace "zan iya za6a" can ta nuna wani hadaddan swiss lace,

"Wow, gaskia kin iya za6e" Zee ta fad'a yayin da takai hannu ta ciro mata lace din, sosae Fatuu ta shiga washe baki tana juya lace din a hannunta can idonta ya kai kan price d'inshi dake manne ajikin ledan lace din, kura ma kudin ido tayi cikin rashin fahimta tace ma Zee "Wannan kudinshi ne?" kai ta d'aga mata alamar eh,
" To..Naira nawa ne naga ansa 64..,dubu shidda da dari hudu yake kenan?" tana ta Murmushi tace mata "No, ki duba sosae dai how many zeros are there?"
K'ara k'ura ido Fatuu tayi tana kallon kudin can ta dago a d'an firgice tace "zero ukku ne, kenan dubu sittin da hudu yake?"
"Yea, haka ne kin fad'a daidai" tana rufe baki ta tura mata lace d'in sai kace wani mugun abu, cikin rashin fahimta Zee ta tambayi miya faru ne tana tura baki tace " banson shi yay tsada da yawa, ace kudinshi har yayi kudin dan shanu wannan ma ai Almubazzaranci ne" sai yanzu Zee ta gano dalili kuma Maganar shanun da tayi tasa ta fahimci bafullatana ce nan take ta yanke aranta k'ilan cikin yan'uwan H,zakee ne na Daura, cikin d'an lallami tace "ai isn't an extravagance, in kana da hali ba laifi bane don ka siya abu mai kudi sosae, kuma ai kinga lace d'in is very fine and unique" turo baki tayi tace ita dae bata sonshi,
Chapter 95 · 0% Book details