← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 137

Sashe 32

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tunda ya ambaci shanu gaba daya ta k'ara rikicewa ta wani zazzaro idanu tana kallonshi lokaci guda tasa tafin hannunta na dama ta rufe bakinta tana girgiza masa kai da sauri,shi dai sai kallon ta yake yana k'ara mamakin yadda ta kara rudewa don yace abashi shanu kuma,dan daure fuska yayi yace"kina nufin shanun ma bazai samu ba duk da akwai? baki na kyerma tace"kwarankwatsi kaji na rantse ard'o bazai ta6a yarda ya bada shanu goma ba akan laifin dana aikata,ai ko baffana ya aikata bazai bayar ba balle ni...."waye shi" ya tambayeta,da sauri tace"kaka na ne wanda ya haifi baba na kuma shine mai garinmu" ta6e baki haisam yayi"ni ai dama bani da case da shi,shi ina ruwanshi Dad d'inki shine zai biya ba grandpa ba" cije le6e fatuu tayi alamar bazaka gane ba,hawaye suka gangaro mata tace"ai shi Baffa na baida shanu goma yan kad'an gare shi ko biyar ma basu kai ba kuma duka ard'o ne ke iko dasu,basu isa suyi wani abu dasu ba batare da ya bada izini ba,nasan wallahi bazai bayar da shanun ba koda harbeni za'ai a gabanshi kuwa..." muryarta ce ta karye ta fashe da kuka,
d'an murmushi yayi ba tare da ta gani ba yace"bai ga za'a harbe kin bane" tsayawa tayi da goge kwallan da take,

"wallahi ni nasan bazai bada ba,ko fa Akuyan Jibo dana jefa ta mutu da kyar ya yarda aka biya shi..."kawai sai gani Haisam yayi ta kwashe da daria tana fad'in"wllh ranar yakin badar akai..." ganin yadda haisam din ke kallonta yasa ta shiga daidaita natsuwarta tana fadin"kayi hakuri wllh abunne dariya yake sani in na tuno ko banyi niyyar yin dariyar ba" tayi maganar tana turo baki,shi dai kallonta kawai yake can cikin ransa kuwa mamaki yake wai wadda ke cikin wani hali ce haka take daria lokaci guda yai assuring kansa cewa yarinyar is Mental,

Hannu ya kai ya d'auki lemun gwangwanin daya daukko ya bud'e hadi da tsiyayawa a cup ya dauka ya kai bakinsa,tunda ya fara tsiyaya lemun ta tsaya cakk cike da mamakin wane irin lemu ne wannan take binsa da kallo har yakai bakinsa ya dan kur6a sau biyu kana ya aje"kice dama kinsaba jifan abun mutane ki kashe masu and the worse of it shine da har abu mai rai kike jifa ki kashe",
"Wllh ita kadae ce babban abu mai rai dana ta6a kashewa,sai su 6era,kyankyaso,da kadangare su kuma ai kaga suna cutarwa ko....yauwa na tuna na ta6a karya ma Altine k'afan kazarta amman wannan ramawa nayi, nima take man kafan d'an kaza na tayi kuma ai ba haramun bane in an maka abu kaji baka iya hakuri ka rama ko,ko ita akuyan jibon ba hakanan na kasheta ba laifi tayi man kuma ma wllh bada niyyar kasheta na jefetan ba" ta karasa sai faman nishi take tana daga hannu ita ala dole bata da laifi.

"Nima kenan laifi nayi maki don na raba ku fada shiyasa kika fasa man glass din?haisam ya tambayeta yana k'ara kur6ar lemun,
"a'a ni badon ka rabamu fada ba,ba gaura mun mari ka yi ba,wllh har saida fa naga wuta" ta turo baki tana sussunar da kai kasa,jinjina kai haisam yayi,da alama dai yana enjoying hiran ko kuma kilan har yanzu akwae sauran abunda yake son sani game da ita ne.
"Shi abun da kika jefan ya mutu mi yayi maki shi kuma?ya jefa mata tambaya,kallonshi tayi har lokacin akwae kwalla a fuskarta tace" wai akuyan jibo? dage mata gira yayi alamar eh,durkushewa tayi don ta gaji da kneeling d'in tace"ba a makarantar bokon mu ne aka koya mana yadda ake shuka abinci ba,shine fa na had'a yar gona a gefen gidanmu na shuka gero da masara inason in sun fito in saida insamu kudi saida suka fara fitowa watarana kawai naje gonar naga an tuge su duka wllh ranar naji bakin ciki,kasan mi? ta d'age ido sama,a hankali haisam ya girgiza mata kai alamar a'a,taci gaba"harfa kuka nayi,naita birgima gashi abun haushin ma bansan waye ya tugen shukan ba,Yadikko nace taita bani hakuri da Baffana ya dawo ya sake bani wasu yace inje in shuka yace insamo k'ayoyi na rufe wurin in ta fara fitowa,shine fa na hakuri amman duk da haka na dau alkawarin inna gano ko waye wllh bazan kyale shi ba,bayan wani lokaci da shuka su suka fara fitowa nayi yadda baffana yace inyi sosai nike kula da gonata kowa yasan gonar fatuu masifa ce ba mai zuwa wurinta,abun bak'in ciki...." tasa hannu tayi tagumi cike da damuwa,haisam dai still yayi yana kallon Mental fatuu,

taci gaba"wai fa sai da shukan nan suka fara yin tsawo sosai watarana yadikko ta aikeni in debo ruwa a bayan tudu na dawo d'auke da tulu na akai tun daga nesa na hango kaman an bude man gona da sauri na nufi wurin tun kan na isa na hango yar iskan akuyar nan duk ta cinye shukan saura kad'an ta gama,Allah kun bansan lokacin dana saki tulun nan ba na rarumi dutsi na jefa mata bai sameta ba ta fara kokarin guduwa cikin sa'a kayoyi suka tokareta ta rasa yadda zata gudu nikam ina ganin hakan na dau icce na ritsata naita dukanta sosai hardai tasamu ta fice da kyar take gudu saboda kafafunta dana doka sosai,hakan bai ishe ni ba na sake rarumar wani k'atoton dutse na jefa mata aikam basai ya sauka akan cikinta ba kuma dama ciki ne fa da ita nan take ta fad'i a kasa tana birgima idanuwanta na haka...." ta langwa6ar da kai ta kakkafe idanunta tana displaying yadda Akuyan tayi,Haisam couldn't help it but laugh,da farko tausayin akuyan yaji don shi mutum ne mai tsananin tausayi amman yadda tayi yasa shi yin dariya har hak'oransa suka bayyana,yana ganin zata bude idanun ya yi saurin d'aure fuska.

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching love story_

_*BY ZAINAB LALUH📲*_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

27⃣

......Bud'e idanun tayi taci gaba"ina ganin haka na watsa da gudu gida,ashe wani yaro gidado ya gan sanda na jefi akuyan ina jinsa yana fadin sai ya gayo ma jibo,aikuwa d'an banzan yaron nan ya falfala aguje yaje ya gayo ma jibo abunda nayi ma Akuyarsa,ina tsaye gaban yadikko tana ta tambayana ina ruwan,miya faru ta ganni a firgice gashi na shigo a guje,ban kaiga bata amsa ba sai ga yaron yayan baffana sun shigo da Jibo rungume da Akuyar......,

kyalkyacewa ta sake yi da daria wannan karon har tafi ta d'azun tace "kai,wllh Jibo baida hankali,kasan wai ko wando fa bai sawo ba don masifa daga shi sai yar riga" d'aure fuska Haisam yayi yana d'an harararta,ganin haka yasa da sauri tace"banfa ganin mashi jiki ba,a'a wllh haram ni ba abunda nagani ai rigan jikinshi ya sauko har gwiwa fa,kama duba a computer ka zaka gan ba k'arya nike ba ni banga komai ba" ta daga hannu,

Haisam da yai zugudum yana sauraranta tamkar ya kunna Redio yace"uhum.."alamar taci gaba,tace"masifa da bala'e yazo yayi tayi yana cewa wllh sai an biyasa akuyansa in ya yarda shege ne shi,nan dai duk yan gida suka fito suna tambayan ko lafiya da yake gidanmu babba ne duk yayyu da kannen Baffana anan suke da iyalansu,ganin haka yasa Yadikko ta kira Babana a waya da yake lokacin yana kasuwa,ai yana jin abunda ya faru ya dawo da sauri don yana masifar sona baison wani abu ya same ni su kuwa sauran yan gidan duk sun tsane ni,kowa ya bud'e baki fatuu bata ji,fatuu bata da kunya,fatuu ka za,fatuu yen-yen....,kana ji ko?" daga mata kai yayi kawai da alama al'amarin nata yafi karfin tunaninsa.

ta cigaba"gaba daya aka kwasa aka tafi wurin Ardo don yayi shari'a,karshe dai ardo yace za'a bashi wasu yan kudi yayi hakuri,yace bai ganin ni yarinya ce,kuma suma wai fama suke da ni,Jibo kam ya rantse da kwarankwatsi gajimare Akuyarsa za'a biyasa kuma daidai girmanta harda cikin ma,kaji fa don bala'i,shi kuma Ardo yaji haushin jibon yak'i jin maganarsa amatsayinsa na shugaba yace har kudin ma ba'a bashi,aikuwa yace to ko daga nan gari ya nufa yan sanda zaije ya fada mawa,baffana yayi ta ba ardo hakuri yace ya bashshi ya biyasa acikin akuyoyinsu,saboda baison aje wurin polisawan ai man wani abu,da kyar fa aka biya jibo akuyansa,ai yana fita Ardo yace akamo ni da gudu naje na 6uya a karkashin gadon yadikko amman mugun yaron nan Jauro da yake ya tsane ni shima saida ya jawo ni aka zane ni don dama ardo baison abunda zaisa a ta6a masa dabbobi,bayan an doke ni kuma yace a d'aure ni daga ranar ban sake fita ko makaranta ma ban k'ara zuwa,kuma ko aike na ma kada a sake yi wai aure za'a man ya gaji da hali na,na dinga kuka, ni d'aure nin da akayi ma bai dame ni ba don nasaba,jin za'a man aure shi yafi damu na,don ni bana son auren karatu nike son inyi in zama likita,kwana na biyu a d'aure sai dare ake saki na inje in kwanta da rana kuwa ina a daure don karna fita,kaga ni aka maida Akuyan ko,Baffana ba yadda ya iya saidai yayi ta bani hakuri yana man fad'an in daina rashin ji in natsu don Allah,sam baijin dadin yadda ake maganganu akaina,ana cikin hakan rana ta ukku kawai ba sai ga gwaggo ba....."
Chapter 32 · 0% Book details