← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 137

Sashe 86

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da safe Haisam ya parker akopar gidansu lokacin zai tafi wurin aiki, kiran Amadu yayi a waya yace ya d'an fito waje, bayan ya fito ya gaidashi cike da girmamawa, amsawa yay yace ya bud'e back door akwae sako ya kaima bako, wata katuwar leda ce mai hannu ya fiddo saida yay mashi godiya kana ya shige gida shi kuma ya tafi, gwaggo ya kaima sak'on yace inji Yaya haisam yace aba Baffan Fatuu, jinjina kai kawae tayi tana Murmushi ta jawo ledan ta bud'e, kaya ne ciki sosae, shaddoji dinkakku guda biyu daya mai babbar riga daya kuma dogayen riga da wando ne, sai guda daya da ba'a dinka ba sai kuma manyan yadi kala biyu, takalma da huluna kala bibbiyu sai agogo ma guda biyu sai kwalin turare guda ukku, duk yadda gwaggo taso kin yin mamaki saida tayi shi haka Amadu ma sai faman jinjina kai yake don Haisam ya iya yin kyautar ban Al'ajabi, lokacin da aka kai mashi kayan shima saida ya d'an rude ba kamar dayaga duka fa jiya ya sanshi gwaggo tace mashi haka halinshi yake, koda ya buk'aci zuwa yi mashi godiya Amadu ya sanar dashi ya tafi wurin aiki saidai ya kirashi awaya, koda ya kira bai d'aga ba almost 3 times gwaggo tace ya kyaleshi kawai in ya gama shiryawa ya kaishi wurin hajiya su gaisa sai yay mata godiyar,

Lokacin da suka je gidan cike da mutuntawa hajiya ta kar6e shi tana ta fara'a don bata ta6a ganinshi ba sai yau sai kuma a wani hoto da Fatun ta ta6a kawo mata can da dad'ewa shida mahaifiyarta, har Saude da Tk saida Hajiya ta kirawo tace suzo su gaisa da Baban Fatuu, suma cikin girmamawa suka gaidashi yana ta dae fara'a Fatuu na lik'e dashi har hajiya na tsokanarta tana cewa to ko zata bishi ne, ta mak'e kafad'a tace in taje aure za'ai mata gaba daya suka sa dariya,sosae yayi mata godiya lokacin da zai bar gidan, kud'i hajiya ta ba Amadu abashi acikin envelope ba tare da saninshi ba, har Amadun zai yi mata gaddama yak'i amsa tace yaushe ta fara yin wasa irin wannan dashi dole ya kar6a, bayan sun koma yay sallama da gwaggo alokacin Amadu ya bashi kudin da hajiya ta bashi yace suyi amfani dasu amman gwaggo taki amsa tace shi aka ba adole ya amsa don bai iya yin jayayya da ita, Fatuu da Amadu ne zasu raka shi tasha don anyi hutun Azumi shiyasa basuje makaranta ba, har kopar gida gwaggo ta rako su tana yi mashi Allah ya kiyaye Amadu na ruke da jakar da gwaggo ta zuba mashi kayan da aka bashi don yar jakarshi da yazo da ita bazata dauki ko kwatan kayan ba don yar k'arama ce iya kayan da zai canja ya sako a ciki hakan yasa ta bashi babba mai zip wadda ta d'auke duka kayan harda jakar da yazo da ita, akan hanyarsu ta zuwa bakin hanya don hawa keke napep ne ta tuna da Haulat, rokon Kawu Amadu tayi su bi ta lungun gidansu don Haulat d'in ta gaisa da babanta, bai mata musu ba suka bi ta lungun lokacin da suka karasa, da zata shiga kiran haulat d'in yace mata kar ta 6ata masu lokaci tace yanzu zata fito, bada jimawa ba kuwa sai gata ta fito da haulat d'in tana sanye da hijab har k'asa ta duka ta gaidashi tana ta murmushi ya amsa mata shima yana murmushin, ce masu tayi bari taje ta tambayo innarta sai su rakashi tare, lokacin da ta dawo wajen harda innar tasu itama ta lek'o don su gaisa, atare suka durkusa suna gaida juna kafin tayi mashi Allah ya kiyaye hanya, k'arasawa sukai bakin hanya suka hau Napep don zuwa tasha, lokacin da suka sauka Haulat taba kawu Amadu dubu dayar da innarsu tace abashi har yana cewa ai da bata bada ba, Motar Kano ya hau lokacin bai fi saura mutum biyu ba ta cika, Fatuu tace bazata tafi ba sai sun tafi yanata cewa su tafi tana mak'e mashi kafada saidae yay Murmushi kawai don ya fahimci har yanzu da sauran rigimarta amman acan k'asan zuciyarshi ba k'aramin farinciki yake ji ba da ganin yadda ta koma gaba d'aya ta canja daka kalleta zaka san tana cikin jin dad'i, ba'a dau wani dogon lokaci ba mutum biyun suka samu motarsu ta tashi suna ta d'aga mashi hannu suna cewa Allah ya tsare Fatuu na fad'in wayyo babana ya tafi harda yin baya kaman zata fadi haulat ta tareta tana mata dariya,

(To Baban Fatuu, muma muna yi maka Addu'ar Allah ya kiyaye hanya,Allah yasa a sauka lpy,Amin)

Ana gobe za'a fara Azumi Tk ya kai uban kayan abinci gidansu Fatuu, dama duk azumi Senator Ali na aiko da kayan abinci masu yawan gaske a rarraba gida gida sai dae wannan karon kayan da aka kai gidansu Fatun sunfi na baya yawa sosae sakamakon Haisam da ya kara masu, bama su kadae ba harda sauran mutane saidae nasu yafi yawa don babu abunda babu wanda mutum zaiyi lafiyayyan buda baki da sahur, bayan d'anye da ake rarrabawa anayin lafiyayyan dafaffen abinci na sadaka agidan hajiyar, musamman ma'aikata masu yin girkin duk azumi ke akwae, a can bayan part d'in hajiyar ake kafa rumfuna ana yin aikin, bayan abinci ana yin kunu da kosai da kuma abunsha kamansu zo6o kunun aya wani lokacin harda fruit acikin wanda ake kaiwa masallacin gidan alokacin bud'a baki,

**** **** ****

An fara azumi lafiya gashi yau in an kai na bakwae kenan wato sati guda da farawa,Misalin karfe sha daya na safiyar ranar wadda take Asabar Fatuu ta shigo gidan hajiya ta Gate don tunda aka fara azumi ta rage zuwa part d'in Haisam don da safe yana wurin aiki ko tazo bai nan dayake ita an basu hutu in ya dawo da rana kuma mafi yawancin lokutta ko taje bacci yake da yamma kuma in aka gama sallar la'asar tsayawa yake wurin tafsir hakan yasa basu cika haduwa ba sai a part din Hajiya, tana shigowa ta hango shi acikin parking space ya bude boot d'in mota ya d'an dukar da kanshi da alama wani abu yake yi, wurinshi ta nufa ta tsaya daga gefenshi ganin alamar mutum yasashi d'agowa ya kalleta, gaidashi tayi tana d'an d'age baki tana yamutsa fuska,

"Miya faru?" ya tambayeta,kaman zatayi kuka tace "ba azumin ne ke bani wahala ba" jinjina kai yayi yace "tunda wuri haka" tana ta faman yamutsa fuska ta d'aga mashi kai, dama kullum in sun hadu haka take complain d'in Azumin wuya,
"Ki shiga ciki sai ki kwanta ki huta",
amsa mashi tayi da to ta nufi part d'in Hajiya, lokacin da ta shiga cikin parlon ba kowa amman an gyara shi tsaf sai dan sanyayyan kamshi ba mai karfi ba ke tashi don tunda aka fara azumi aka rage sa turare da yawa, kitchen ta nufa wurin Saude don tasan war haka Hajiya bacci take, tana shiga ta isketa tana yin wanke wanke,

"Aunty Saude ina kwana",
da fara'a ta juyo ta kalleta "lafiya lou Fateema har an dawo daga islamiyyar" kai ta d'aga mata alamar eh,
"Ina fata dai yau kina yin azumin?"
tana tura baki tace "banyi,ni wllh wuya yake bani shiyasa nike karyawa" jinjina kai Saude tayi tace "ki rink'a daurewa kina yi ta hakane zaki saba" d'aga mata kai tayi alamar toh tana dai atsaye can ta matsa tace bari ta tayata, d'auraya ta fara yi mata suna cikin yi sauden tace "Don Allah jeki part d'in Yayanki ki d'aukko man basket d'in kayan sahur da aka kai mashi da asuba na manta ba'a d'aukko su ba",
amsa mata tayi da to ta juya ta fita, lokacin data fita harabar gidan bata hango shi a cikin parking space d'in ba hakan yasa tayi tunanin ya koma part din nashi, da sallama ta shiga lokacin data isa saidai bai amsa mata ba don bai cikin parlon, k'ara yin sallamar tayi wai ko zai jiyo ta don kilan yana cikin Bedroom ne amman bata ji ya amsa ba hakan yasa ta nufi center table don d'aukar basket d'in da ta gani a samanshi cikinshi dauke da kayan tea da warmer, maimakon ta d'auka din sai takai hannu ta bud'e warmer dake ciki nan take ta zare ido ganin soyayyan dankalin turawa mai d'an yawa aciki, shiru tayi tana kallonshi ta fara hadiye miyau,d'an d'agowa tayi ta kalli kopar Bedroom d'in nashi jin bata ji wani motsi ba yasa ta kai hannu ta d'ebo dankalin mai yawa ta tura abaki tana taunawa idonta na a corridor d'in Bedroom din, tun tana ci atsaye har ta duk'a tayi ruku'u tana yi tana kallon corridorn don kar ya fito ya ganta,

"Can't u sit properly, haka zai iya shake ki ai" taji daga bayanta ya fad'a aikuwa a firgice ta juya ta kalleshi baki cike da dankali, ashe bai cikin d'akin kuma da ta shigo bata kulle kopar falon ba hakan yasa bata ji shigowarshi ba, can 6arin L-shape ya nufa ya zauna ya d'aura abunda ya ruko ahannunshi saman c-table wanda da gani wani abun computer ne, ci gaba da duba abun yayi alamar gyara yake yi ajikinshi,

shin wai ina Fatuu????

ALBISHIRUNKU MATAN AFRICA DA KEWAYE SHAHARARRAR MAISAIDA KAYAN MATAN WADDA KUKAFI SANI DA MAMAN HAIDAR TANA YIMAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE AFADIN NIGERIA DA NIGAR KARKU MANTA MACE MAI GYARA BATA BORANCE💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃08040448621
Akwai zafafan kayan mata masu kyau da arha cikin sauki zamu aika miki da kayanki cikin aminci da yardar Allah ba cuta ba cutarwa karku bari abaku labari
Muna kawo kalolin kaya kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-Maganin sanyi
2-Maganin gyaran nono
3-Maganin hips
4-Akwai gumba kala kala
5-Maganin matsi masu ciko da gaba ki koma kamar budurwa
6-Kalolin garirrika masu bawa mace ni ima da jimawa yana aiki
7-Akwai tsumi sha yanxu magani yanzu
8-Akwai jigidar sirri kala kala
Sannan kuma muna dahuwa kamar haka 💥💫💥💫👇👇👇👇
1-dahuwar kaza
2-yan shila
3-ciccibi
Dadai sauran su.Abubuwa dayawa gaskiya bazasu lissafu bah saboda lokaci maiso tabini PC don ganin Kalolin kayan da muke dasu 08040448621

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching story of Love and Destiny_ 💔
Chapter 86 · 0% Book details