← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 137

Sashe 129

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lokacin data shiga ciki d'akin gwaggo ta nufa har lokacin Amadu na ciki ya kishingida kan kujera gwaggon na zaune a gefen gado da alama fira suke Fatun ta shigo da sallama ta nufi gwaggo tana washe baki Amadu yace "ai munyi zaton acan zaki kwana keda hankalinki ragaggene" bata tanka mashi ba ta aje ledar gaban gwaggo tana Fad'in tsaraba ce itama Ya Handsome ya bata ta Lagos daya je, fiddo abubuwan dake aciki ta fara yi, Wata hadaddar School Bag ce da takalma cambus guda biyu a cikin jakar akwae littattafai na karatu dana rubutu wato exercise books da textbooks masu yawa don duk manyan Subject d'in da ake a Senior secondary akwae textbook nashi ga uban biroka fensir shafana kilina da sauransu dae abubuwan gwanin burgewa irin na yan gayu don wannan da gani duk Makarantar tasu ba lallae asamu mai irinsu ba ba kaman jakar goyon irin mai trolley din nan ce, saboda tsabar farinciki har ta kasa Magana sai faman d'aga kayan take gwaggo ma dariya ce akan fuskarta, juyawa tayi tana nunnunama Amadu kayan yace "inyee yar gidan Ya Handsome sai nima ki dibar man rabona to" mak'e mashi kafad'a tayi yace wllh bata isa ba wannan uban kayan ya zata yi dasu tace ai tasan harda Haulat shiyasa ya siyo su da yawan yace to shima harda shi ai aka siyon gwaggo dae nata dariya tana girgiza kai, koda ta gwada takalman ba k'aramin kyau suka yi mata ba gashi sunyi mata daidai sai faman washe baki take tana nuna ma gwaggo kafar tata ita kuma tana yin Addu'a, mik'ewa Amadu yay yayi masu sallama dama tun d'azun yake jin bacci daurewa kawai yake yana ma gwaggo firan ruga, bayan ya tafi gwaggo tace "to ki maida su ciki kije kiyi wanka ko kya ji dad'in jikin kinje kin zauna gashi dare ma yayi sosae kije dae kiyi ki rufe kanki kuma ki tabbatar kinyi Addu'a" kai ta d'aga mata bayan ta mayar dasu suka fita tare don ta had'a mata ruwan wankan. Washegari suna gama yin karin kumallo taje tayi wanka ta shirya cikin riga da skirt na atampa ta yafa mayafi ta nufi gidan Hajiya don kai mata sauran tsarabar lokacin k'arfe goma da wasu mintuna, lokacin data shiga Falon Hajiyar na zaune kan kujera tana kallon labaru su Jidderh kuma na kan Dining table suna yin breakfast don basu dad'e da tashi ba, da sallama ta shiga Hajiya ta amsa mata tana ganinta ta saki Murmushin jin dad'in ganinta don hakan ya tabbatar mata da bata yi fushi ba kan abunda ya faru jiya su twins ma na ganinta suka taso da gudu suna fad'in "Welcome sis Fatuu" suna k'arasowa suka fad'a jikinta tasa hannu ta dafa bayansu su duka, a kusa da kujerar da Hajiya take suka zauna ta gaidata tana dariya itama dariyar take tace "Yan tafiya ya gajiya?" tace " ba gajiya" aje mata ledar da ta shigo da ita tayi gabanta tace ga sauran tsarabar nan hajiyar tace "kuma dae muna ta shan tsaraba haka da dijen ma ta dawo ta kawo mana fa, to an gode Allah yasaka da Alkhairi" tana rufe baki Jidderh ta k'araso wurin jikinta sanye da doguwar rigar bacci brown mai santsi kanta ta yafa bak'in gyale tana kallon Fatun da Murmushi ta zauna kan Sofa Fatuu ta gaisheta ta amsa cikin muryarta ta yan gayu tace "ya gajiyan tafiya" amsa mata tayi da babu gajiya ta jinjina mata kai, kama hannun Mubeena mubeen yayi yace "zo muje mu gaya ma Ya Nameer Sis Fatuu tazo" suka nufi hanyar Bedroom da gudu, bada jimawa sai gasu sun dawo tare da Nameer d'in ya kamo hannuwansu da gani daga bacci yake don idanunsa sun nuna yana sanye da wando 3 quarter da riga armless da gani shima yana gyming don damtsen hannunsa ya gwada, da Murmushi ya k'arasa kujerar da Fatun take ya haye kan hannun kujerar idonshi akanta itama kallonshi take tana Murmushi cikin muryarshi da bata idasa washewa ba yace " yar fillo kin tashi lpy ya gajiyan tafiya" d'an tura mashi baki tayi tace "nifa ka daina ce man yar fillo ba kasan sunana ba" kawae sai ya dungure mata kai yace "to ke ba yar fillon bace" dariya ya basu gaba d'aya ganin abunda yayi mata, k'ura mata ido yay yana kallonta kafin yace "baki fushi ba kenan?" shiru ta d'anyi kafin ta d'aga mashi kai alamar eh yace "Gud haka ake so mutum ya kasance mai hakuri" Hajiya tace "aikuwa dai Fateema ba dai hakuri ba dama" wani kallo Fatun tayi mata alamar bata yarda da Maganar Hajiyan ba ba kamar da ta ga tana dariya alamar itama da biyu tayi Maganar duk suka yi Murmushi suma don sun san labarin Fatun na bata barin ta kwana duk wannan abun Farha na dining tunda ta juyo lokacin da Fatun ta shigo ta kalleta bata k'ara waigowa ba karshe ma sai ta mik'e ta nufi Bedroom, sai wurin Azahar ta bar gidan su twins na tambayarta zata dawo ko tace masu eh sai da daddare zata zo suyi fira lokacin Nameer har yayi wanka ya canja kaya suka fito atare yace bari ya rakata daga can ya wuce Masallaci, bayan sun fito ta tambayeshi Haisam yace mata yana wurin aiki dama tasani kawae hakanan ta tambayeshi, suna tafe suna fira sai kace sun dad'e da sanin juna har kopar gida ya rakota ya tsaya suka gaisa da Amadu Fatuu na gaya mashi k'anin Ya Handsome ne yace ai ya gane tunda ga kama nan ya gani, yayi mashi anzo lafiya fuska sake Nameer d'in ya ce mashi lafiya lou suma sun dawo lpy, cikin mutuntawa suka gama gaisawar ya kalli Fatuu yace "to yar fillo sai anjima ko" yar harara ta wurga mashi shima ya rama suka sa dariya harda Amadu daga haka ya juya ya tafi, bayan ta shiga gidan tsarabar Haulat ta d'auka ta nufi gidansu don bata san sun dawo ba tun ranar asabar data zo don da sukayi waya da Fatun lokacin suna can ta sanar mata ranar zasu dawo ta iske basu dawo ba Gwaggo tace mata sai washegari hakan yasa jiyan bayan la'asar ta sake zuwa still ta iske basu dawon ba, ba k'aramin farinciki Haulat tayi ba da ganin Fatun sai faman washe baki take kamar zata goyata innarsu ma da kannenta suka yi mata an dawo lafiya, lokacin data bata tsarabar harda ta haisam bayan sun shiga d'aki kasa rufe baki tayi don murna sai faman tatta6a abubuwan da haisam ya siyo masu take cike da zumud'i ta kwashesu taje ta nuno ma innarsu,bayan ta dawo ne innar tasu itama tazo d'akin tayi ma Fatun godiya kafin ta tafi, firan ruga ta shiga bata har akayi la'asar sannan ta baro gidan don tana son zuwa wurin Haisam in ya dawo tayi mashi godiyar tsaraba sosae don ba k'aramin dad'in kayan taji ba, tare da haulat d'in suka taho zata islamiyya tace ma Fatun ita bazata je ba tace eh sai gobe, a daidai kiosk d'in kawu Amadu suka rabu ta wuce, matsawa tayi gaban kiosk d'in ta tambayeshi yaga Ya Handsome ya wuce yace shi bai ganshi ba hakan yasa ta nufi cikin gidan tayi salla bayan ta gama ta fiddo da tsarabar kayan makarantar tana sake dubawa cike da jin dad'i ba komae yafi mata dad'i ba sai sanin cewa duk Makarantar baza'a samu mai irinsu ba, ganin hud'u da rabi ta wuce karfe biyar ta kusa yasa ta maida komae ta mik'e da sauri ta fita waje, wurin kawu Amadu ta sake komawa ta k'ara tambayarshi ko Haisam ya wuce da farko cewa yayi bai sani ba ta aje shi ne yay mata gadi, magiya ta hau yi mashi sannan yace eh ya wuce bada jimawa sosae ba, ko gidan bata koma ba ta nufi gidan Hajiyar ta k'aramar kopa tabi ta shiga part d'inshi tana niyyar hayewa balcony taji daga bayanta da d'an k'arfi ance "Hey!!!" da sauri ta juya don bata tsammaci ganin wani ba, Farha ta gani tsaye bakin fence door tana sanye da skinny fit bak'i wanda iyakarshi gwiwarta sai riga mai dogon hannu bak'a ta kamata sosae gashi daga k'asa bata rufe saman wandon sosae ba ana d'an hango k'asan cikinta da yake fari fat, kanta tasa bakar hula irin mai kama kai yayin da gashinta ash ke zube a gefe da gefen fuskarta hannunta ruke da wayarta wadda keda cover ash haka kafafunta ma na sanye da flat shoe ash ba k'arya tayi kyau sosae ta fito a baturiyarta dama gashi ba ramamma bace tana da yar k'iba sannan a shekaru ta girmewa Fatun sosae don zata kai shekara 18 zuwa 19, da wani irin taku ta nufo Fatun ta tsaya agabanta tana yi mata wani kallon rashin arziki itama Fatun kallonta take ta d'an d'aure fuska saidae jurewa kawae take saboda k'wayar idonta mutum bazai iya jure ma kallonta ba na tsawon lokaci,
Chapter 129 · 0% Book details