← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 137

Sashe 79

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"shi teacher d'in da kike magana akwae wani list na textbooks da ya ta6a baki right?" jinjina mashi kai tayi alamar eh,
"Ok,ina list d'in?"
"Paper d'in na wurin gwaggo tun lokacin da aka bani nakai mata nace ance asiyo wad'annan littattafan to sai ta ba kawu Amadu tace ya tambayo mata kudinsu lokacin da zaije kasuwa to daya dawo ne yace mata duk shagon daya je babu su sai da aka mashi kwatancen wani Babban Bookshop acan ne aka samu wasu acikinsu wasu kuma suka ce sun k'are amman za'a kawo ita kuma gwaggo data ji suna da d'an kudi don akwae ma wani na English dubu biyar yake shi kadae sai tace gaskiya bata da kud'in da zata siye su lokaci guda amman akwae adashe da take yi wanda zata siya ma kawu Amadu freezer saboda azumi daya kusan zuwa ya rinka saida kankara in ta kwashi kudin zata siya mansu duka shi kuma sai ta nemi ciko ta siya mashi,to ita nike ta jira fa kuma shima Uncle Bash d'in in ya tambaya ai inace mashi ance za'a siyo"ta k'arasa tana ta nishi sai kace ya tambayeta duk wannan bayanin,shi dai yayi shiru yana sauraranta har ta gama,

Gently yace" je ki amso man paper d'in",
Bud'a idanu tayi"siyo man zakayi?"
d'an k'ank'ance idanu yayi"ko baki so?"
A shagwa6e tana tura baki tace"to amman ai tsada garesu fa sai a saka ka kashe kudinka hakanan,shima ba ance za'a siyo ba",
"Shine ai yanzu za'a siyo d'in ko saboda kina bukatansu"

"Ni dai gaskiya banso kaita kashe kudinka fa,in kuma suka k'are fa", d'an Murmushi yayi jin abunda tace,d'an gyara zama yayi ya jingina sosae yana kallonta,
" bazasu k'are ba inada su da yawa so don't worry about dat, yanzu kije ki kawo man and daga yanzu duk in kina bukatar wani abu game da karatunki ki sanar man" zaro ido ta k'ara yi a d'an rud'e tace "kai kuma ba gwaggo ba?"

"Yeah"ya bata amsa fuskarshi still da Murmushi,
" to saboda me?"ta sake tambaya,
"Saboda na fita kudi kuma abubuwa sunyi mata yawa kinga sai in rage mata burden ko",
d'age kai tayi gyalen ya idasa sa6ulewa ya tsaya kan kafad'arta a shagwa6e tace "to amman kai ai ba d'an gidanmu bane kuma sai ka d'aura ma kanka nauyi"

"Yanzu ai nazama ko baki so?"

"To ai sai ka dawo gidanmu zaka zama d'an gidan"
"Ok sai in dawo in kin tanadar man inda zan zauna",

" sai ka dawo d'akina ni kuma sai in koma na gwaggo,tunda akwae gado sai ka d'auki wannan kujeran daka fi zama tunda d'akin bazai isa asa dukkansu ba"still da Murmushi akan fuskarshi da alama yana enjoying hiran ne,
"Ok zanyi hakan,sai ki fitar man da ranan da zan dawo but ki fara sanar da Grandma d'inki",
Wani kallo ta bishi dashi baki bud'e alamar mamaki sai kuma tace" wllh nasan karya...au wasa kake ba dawowa za kai ba,tabb yama za'ai kabar wannan Aljannar duniyar ka koma gidanmu d'an kut dashi kaman zuciyar talaka,ai zafi da sauro ma kadae sun isheka ka gudu sai dai mu farka muga Ya Handsome ya tsere"ta k'arasa tanata dariya shima dariyar yake har hakoransa sun bayyana sosae ba kaman da tace wai gidansu kaman zuciyar talaka ko a ina ta iya wannan Maganar ya fad'a aransa,

"Yanzu dae kije ki kawo man abunda nace" ya fad'a bayan ya gama dariyar,amsa mashi tayi da to kafin ta yunk'ura ta mik'e tsaye har zata juya sai kuma ta juya da yar damuwa a fuskarta tace"to kuma Ya Handsome in Gwaggo tace ni na fad'i maka Maganar littattafan fa,tana iya duka na fa don tace kar na rok'e ka abu",
Shiru ya dan yi kaman mai tunanin wani abu sai kuma yace"ki fad'a mata shi teacher dinne yayi man magana"still da yar damuwa akan fuskarta tace"to Allah yasa ta yarda" har ta juya zata fita ya kirata ta juyo,tambayarta yayi Uncle d'inta nada waya tace mashi eh,yace tasan number dinshi tace eh ta sani yace ta karanto mashi dama wayarsa na aje akan kujera tun bayan da ya dawo,bayan ta bashi lambar wayar kawu Amadun yayi dialing kira yana jin ta fara ringing yace mata taje gidan kawai za'a bata ta kawo mashi,

Lokacin da ta isa kopar gidan Amadun bai acikin kiosk dinshi,tana shiga gidan ta ganshi atsaye shi da gwaggo abakin kopar d'akinta, k'arasawa tayi ta tsaya agefe tana ta faman zare ido,

"To shi bai gajiya ne yai ta faman hidima" gwaggo ta fad'a yayin da ta maida idonta kan Fatuu da sauri fatun tace "Uncle Bash ne yayi mashi Maganar d'azun daya kaimu Makarantar shine yanzu yace wai in kawo mashi takardar",jinjina kai kawae gwaggon tayi kafin ta k'ara cewa wani abu Amadu ya rigata da fad'in" to wai duk minene na damuwa da jan Maganar ma tunda dai ba rok'onshi mukai ba shi yace abashi ki bata ta kai mashi kawae",

"Hakane amman dai wai kar abun yayi yawa aita d'aura ma Mutum hidimar da ba tashi ba" gwaggon ta fad'a da yar damuwa,
"Ba wani abunda zaiyi yawa tunda yana da hali,ki d'auka kawai Allah ne ya dubi duminiyarki kinsan in bawa ya dogara ga Allah sai ya bud'a mashi ta hanyar da bai ta6a zata ba,kuma kinga dama ni da ita duk marayu ne haka kike ta kula damu,to ki d'auka sauk'i ne Allah ya kawo maki ta hanyarshi don haka ki d'aukko takardar ki bata ayi mashi godiya kawai",
jin hakan yasa da sauri Fatuu ta kar6e" haka ma yace wai duk in ina buk'atar abu game da karatuna in sanar mashi,da nace saboda mi sai yace wai ke abubuwa sunyi maki yawa zai rage maki nauyi",
Da sauri Amadu yace"Kinji ko,kar ki wani damu",
jinjina kai tayi cike da gamsuwa"shikenan,Allah ya saka masu da mafificin Alkhairi,yasa ya gama da duniya lafiya ya biya masa bukatunshi na Alkhairi" gaba d'aya suka amsa da Amin,daga haka ta shiga ta d'aukko mata takardar dake d'auke da sunayen littattafan ta bata ta kai mashi.

Lokacin data koma bai cikin parlon hakan yasa tayi tunanin ko ya koma cikin Bedroom ne,nufar corridor d'in tayi ta d'an shiga daga ciki ta rafka uwar sallama,
"Assalamu alaikum Ya Handsome ga takardan" jin shiru yasa ta sake maimaitawa still bata ji yayi Magana ba hakan yasata k'ara d'aga murya tace"Ya Handsome na dawo ga takardan ko in shigo in kawo maka ne?"

"Tunda d'akin ki ne ba sai ki shiga ba"
ba zato ba tsammani taji daga bayanta ya fad'i haka,aikuwa a furgice ta juya ashe bai cikin d'akin fita yayi ya d'aukko abu a Mota,hannu tasa ta rufe baki tana gumtse dariya shi kuma ya d'an harareta ya nufi inda ya tashi ya zauna bayan ya aje abunda ya d'aukko kan c-table, nufo shi tayi tana zuwa gefenshi ta mik'a masa takardar kafin ta zauna kan carpet,dubawa ya d'an yi itama ya d'aurata kan c-table din,
"Kasan inda ake saida su?" kai ya d'aga mata alamar eh,

"To yaushe zakaje ka siyo?" shiru ya d'an yi sai kuma yace"After Asr prayer",

"Kai wai yanzu ma ba dadewa kenan,to yau bazaka je d'aga karfen bane?" wani kallo yayi mata ba tare daya ce komai ba hakan yasata gwalo ido don a tunaninta ko tayi laifi ne da sauri tace"haka naji Hajiya tace rannan shiyasa nima nace",
D'an lumshe ido yayi calmly yace"ba sunanshi kenan ba exercise ne,kinsan mi kenan ko?"da sauri ta d'aga kai tace"to bazaka je exercise d'in ba?"
"Zanje amman sai na dawo"
"To kullum kake zuwa exercise din?"
Girgiza mata kai yayi"bani zuwa weekends but nakan yi saturdays wani lokacin, sundays dai bani yi"

"Yauwa to tunda baka zuwa ranar lahadin ka bari sai ranar sai kaje ka siyo man kaga ranar Monday ba sai inje dasu ba kawai"
Kai ya k'ara d'an girgizawa"No,tunda yayi Magana gobe yakamata ki shiga dasu,lafiya lou har naje na dawo ai",
kai ta d'aga alamar gamsuwa sai kuma tace"to don Allah zan raka ka Ya Handsome "
Shiru ya danyi sai kuma yace"Ai ba wani dad'ewa zanyi ba zan dawo",
" to ba sai mu wuce wurin exercise d'in ba in ka gama sai mu dawo ko",wani kallo ya bita dashi,
"Pls don Allah kaje dani,wllh ni da kake gani na kifin rijiya ne duk bansan wurare ba in baya ga kasuwa sai asibitin da gwaggo ke aiki sai wasu yan wurare kad'an fa" still kallonta yake,yana ganin k'okarinta intayi wata Maganar just cikin 3 years ta iya hausa sosae bacin ko agida tace wani lokacin Grandma d'inta fulatanci take mata,

"Pls don Allah Sweetheart ka tafi dani" Fatuu ta katse mashi zancen zucinshi,tunani ya shiga yi ina zaije da ita in ya tafi da ita,yana da register da gym ukku so baisan wanne zaije da ita ba duk da mata na zuwa amman ba kamarta ba,
"Don Allah Sweetheart Ya Handsome ka tafi dani inga gari" ta k'ara fad'a a shagwa6e,

sigh yayi idonshi akanta yace"in matana taji ki kina ce man Sweetheart d'innan zata fasa maki baki fa" yayi Maganar fuskarshi a sake kaman zaiyi dariya,
"Nasan wasa kake,Kai da ma baka da ko budurwa balle mata kuma",
jinjina kai kawai yayi sai kuma yace" to mi zaki fad'i ma grandma d'inki?" da sauri tace"yo zance mata zan bika siyo littattafan daga nan zan raka ka wurin exercise in ka gama sai mu dawo",
nodding kai yayi"Ok kije ki fad'a mata,if she agrees sai kizo in an gama salla",
Yar k'arar murna ta saki ta fara mashi godiya daga haka ta mik'e ta nufi kopar fita da sauri,har zata kama kopar ta bud'e ya kirata ta juyo,
Chapter 79 · 0% Book details