← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 137

Sashe 25

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Fatuu na tsaye ta jingina da karfen barandar gaban ajinsu ta tafi duniyar tunani,Malam ya fito,tsaye ya yi a bayanta yana kallonta kafin yace "ke cewa nayi ki fito ki tsaya? Wato kinfi karfin ki rage tsawon ki ko? Juyowa tayi ta kafe shi da idanu batare da tace komae ba,hakan yasa ya k'ule cikin daka tsawa yace " ba dake nike bane! Sunkuyar da kanta tayi k'asa tace"baka ce in rage tsawo na ba ai,cewa kayi in fito waje kawae....." katseta yayi "da yake ke dak'ikiyace komai sai ance ki yi ko?"
kallon k'asan ido tayi masa suka hada idanu,a fusace yace "kee! ni kike harara...." daga bayansa yaji ance"abunda yafi harara ma yi maka zatai indae wannan ce" a tare suka juya don ganin mai maganar,wani matashin malami ne ya tunkaro su yana sanye cikin farar shadda jamfa hannunsa na dama rungume da Qur'ani dayan kuma rike da zungureriyar dorina,shine displine a Islamiyyar,ya iso inda suke fuska tamke,wanccan malamin yace"Yauwa Malam Nazifi,gatanan kayi mata hukuncin da ya dace,ina bayani hankalinta na wani wuri,nace ta fito kuma tafi karfin ta rage tsawonta", jinjina kai Malam nazifin yayi daga haka d'ayan malamin ya juya ya tafi,

Kallon Fatuu yayi fuska A d'aure yace "bani hannuwanki! ta d'an marairace fuska tace"Malam don Allah ka buge ni a jiki' dama malam nazifi yasan bata son bugu a hannu,hakan yasa ya k'ara tamke fuska yace"ina wasa dake? Girgixa masa kai tayi,ya d'aga bulalan ba tare da yace komae ba,a hankali Fatuu ta mika hannuwan suna dan rawa ta runtse idanunta ya fara bugunta tamkar da gayya,yana yi mata bulala biyar ta janye hannuwan tana dan yamutsa fuska don ba k'aramin zafin bugun take ji ba" yace"nace ki sauke hannuwan ne?" turo baki tayi tamkar zata fashe da kuka tace "don Allah malam kayi hakuri....."ya katse ta "kinsan kina tsoron bugun kike ma mutane iskanci,bulala goma zanyi maki amman wllh kika yi wasa zata koma ishirin",
sanin da gaske yake yasa ta sake mik'a masa hannu daya tana yi tana canjawa har ya gama,ta juya tana yayyerfe hannu don sosae ya bugeta hannuwan duk sunyi jawur,malam nazifi ya dakatar da ita daga tafiya ta hanyar fad'in "ban sallame ki ba" ta juyo tana kallonshi cikin ido ta d'aure fuska,"kije Office dinmu ki cika mana bokitinmu na ruwa,sannan kije ki wanke gaba d'aya bandakin ku na mata,basai nace kiyi ba,inkin so kina iya kin yi" daga haka ya juya ya shige Class dinsu don shine Malaminsu na Al'Qurani da tajweed,da sauri Haulat ta koma gun zamansu don dama tana a la6e bakin kofa tana ganin duk abunda ke faruwa.

Fatuu ta sauke ajiyar zuciya ta juya don zuwa yin purnishments din da Malam ya bata,a hankali ta ke sa hannu ta na goge kwallar dake zubo mata cikin ranta tana fad'in "Mugu kawae,dama yafi kowa tsanata a makarantar nan,daga yau ba sai ka sake gani na ba zaka bugan..."a fili tace"dama ban zo ba,tunda ba za'a kyale mutum da abunda ya isheshi ba,a daidai nan ta iso bakin staffroom din,Haulat nata faman zuba ido don ganin shigowar fatuu,lokaci bayan lokaci ta ke kai dubanta kan k'opar shigowa amman shiru gashi har an kusa tashi kuma har lokacin malam Naxifi na cikin class d'in saboda abu biyu yake masu,sai lokacin da aka tashi Mlm Nazifi ya fita,da sauri Haulat ta d'auki jakarta had'i da ta Fatuu ta fice da sauri baiwar Allah har tana yin tuntu6e wurin fita,hanyar kewayensu ta nufa don taji Aikin da aka sa fatun,bata k'arasa isa ba ta hangota a hanya tana tahowa,Haulat ta ja ta tsaya tana kallonta itama Fatun kallon haulat d'in take har ta iso wurinta,hannu kawae ta mik'a mata alamar ta bata jakarta haulat ta mik'a mata jakar a hankali fatuu tace "nagode" daga haka tayi gaba, haulat itama ta bi bayanta har suka fita daga cikin Islamiyyar suka mik'i hanya,haulat a ranta tana ta tunanin mike damun fatuu haka,don tunda tazo ta lura da yanayinta tana cikin damuwa ga bugu da kuma aikin da aka bata,
A fili tace"ba abun mutum ya tambayeta ba tayi man wulakancin da ta saba,gara ma in kyaleta,da tana son in sani ai da ta sanar dani" can dae haulat ta kasa daurewa ta kira sunanta da yake ba tazara sosae a tsakaninsu don a hankali fatun ke tafiya ba kaman yadda ta saba wuwwurga kafa ba,bata juyo ba haulat ta sake cewa"Fatuu"a hankali ta juyo tace"minene"haulat ta k'arasa gabanta tace "mi yake damunki ne naga kaman kina cikin damuwa tunda kika zo" fatuu tayi yar ajiyar zuciya ta ta6e baki tace"Uhmm,in na gaya maki damuwar zaki man magani ne" d'an murmushi Haulat tayi tace"ai bansan mike damunki ba,balle in san ko zan iya yi maki maganin" girgiza kai Fatuu tayi cikin karewar murya tace "koma kinsani bazaki iya man magani ba,don haka ba sai kin ji ba" ta juya ta ci gaba da tafiya a hankali,
Haulat tayi tsaye sototo tana mamakin abunda Fatuu tace ma ta,don tasan bata 6oye mata abu in yana damunta,koma ta 6oye zata dawo ta bayyana mata,a ranta tace" to mike damunta haka da bazata fadi man ba...?cikin d'an d'aga murya haulat tace "Amman ko da bani iya yi maki maganin ai kilan in baki shawarar da zata iya yi maki maganin ko" shiru bata ce mata komae ba kuma bata juyo ba,hakan yasa Haulat juyawa tabi d'ayan 6arin dake kallon wanda fatuu tabi ta fara tafiya,Fatuu nata juya maganar haulat aranta na shawarar da tace zata bata,tabbas Haulat na bata shawara kuma shawarar nayi mata aiki,ta tuna wani laifi da tayi kwanakin baya wanda ta tsorata sosae hakan yasa Haulat ta bata shawarar yadda zata yi ta ku6uta bayan tayi mata fad'a,aikuwa shawarar tayi mata Amfani don ta tabbatar lokacin ba don aiki da abunda haulat din ta fadi mata ba Kawu Amadu sai ya karyata....,da sauri ta juya "Haulat,haulat.." ta k'wala mata kira har sau biyu,sannan haulat taja ta tsaya ta juyo fuska a d'aure da alama tayi fushi ne,ganin haka yasa Fatuu ta nufeta ta tsaya gabanta tace"bari in fad'a maki to,amman shawarar zaki bani kar kice zaki man fada don aikin gama ya rigada ya gama, kuma ko baki man fada ba ma nayi dana sani bazan kara aikata irin hakan ba..."ta sunkuyar da kanta jin kwalla zasu zubo mata,ajiyar zuciya haulat ta sauke ta kai dubanta gaban wani gida dake agefensu,ta kamo hannun fatun tace"muje can to ki fadi man nan akan hanya muke" daga haka suka nufi jikin bangon gidan suka jingina,

Haulat tace "ina jinki,mike damunki?" Fatuu dake ta matsar kwalla kamar jira take haulat ta tambaye tan ta rushe da kuka tace "Haulat na bani na lalace,gidan yari za'a kai ni,kuma kilan acan zan mutu ma.." zaro idanu haulat tayi gabanta ya fara faduwa,cikin rashin fahimtar zancen fatuu tace"waye zai kai ki gidan yari?" cikin kuka Fatuu ta zayyana mata duk yadda sukai da Gaye harda aikenta da akai gidan Hajia jiya da daddare harta ga Haisam d'in.
Ajiyar zuciya mai karfi Haulat tayi tace "nasan maganar ma" da sauri ta kalleta tace"kinsan za'a kaini gidan yarin dama kuma baki fad'a man ba.." jinjina kae Haulat tayi tace"jiya da yamma nima na hadu da gayen kuma shine ya sanar dani abunda kika yi har da aka tashi nayi maki maganar, kuma naso in sanar dake Mutumin dan gidan Hajiyar Sanata ne amman kika k'i saurarata k'arshe ma sai cewa ki kae wai ko dan sarkin makka ne ke ina ruwanki...."
Chapter 25 · 0% Book details