Sashe 65
Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haisam ya fad'a ba tare da ya kalli tk d'in ba,rufe masa kopar yayi bayan ya amsa mashi da toh,sai da yayi Warming d'in Motar kafin ya fita daga cikin parking space din,shima tk fitowa ya yi ya tsaya gefe guda yana kallon Motar,da gudu ya ja Motar ya fice daga gidan su officer na d'aga mashi hannu ya sakar masu Horn.
************,
Tafe take ta raba hanya biyu tana ta tafiya sai dai yau tafiyar tata da yar natsuwa ba kaman yadda ta saba wurga k'afafu ba in tana tafiya,horn d'in da aka yi mata da k'arfi ne yasa ta koma gefen hanyar da sauri ba tare data waigo ba,cigaba da tafiya tayi aka k'ara yi mata horn d'in aikuwa a fusace ta juyo cike da tsiwa ta bud'e baki zata yi magana,tana yin arba da Bak'ar Motar dake a bayantan ta kasa magana,bin ta kawae tayi da ido ba tare data san ko waye a ciki ba,slowly glass d'in kopar gaban ya fara sauka k'asa,tana yin arba da fuskar Haisam tasa duka tafukan hannayenta ta rufe baki alamar mamaki,jingina kanshi yayi ajikin headrest d'in seat yana kallonta fuskarshi a sake,
"Ya Handsome ashe kaine kake ta man horn" fatuu ta fad'a bayan ta cire hannun,
"Yea,ni ne za'ai ma masifa" ya bata amsa,
Tura baki tayi"ni fa ba masifa zanyi ba,da naji an k'ara yi man horn dinne shine na juyo ince ai na kauce",d'an ta6e baki yayi don yasan ba gaskiya ta fad'a ba,
"Kin samu sauki ne zaki school?"
"Eh,kuma ma in ban je ba ni kad'ai za'a bari agidan",
jinjina kai yayi"Ok,get into d car",
hannu ta d'aga tana nuna motar tace"in shigo kace?" kai ya d'aga mata alamar eh,matsawa tayi ta kai hannu zata bud'e kopar baya taji ta a rufe,komawa tayi saitin haisam tace"Ya handsome tak'i bud'ewa ko ba ta nan ake shiga bane?",daga yadda ya kwantar da kanshi ya daga mata kai alamar eh,
"To ta ina ake shiga?",ta tambaya,
yatsanshi guda ya d'aga sama,zaro ido tayi"kenan ta sama ake hawa?",gyad'a kai yayi,cike da mamaki take kallon saman Motar can tace"itama kaman jirgi ce kenan ta,to mi zan taka in hau,ko itama tsani ke gareta?" Still yayi yana kallonta ganin da gaske ta d'auka ta saman ake hawa,tunanin ranar da zata daina wauta ya shiga yi tana ganin handle ajikin kopan bayan amman take tambayan ko bata nan ake shiga ba,ganin tana ta kallonshi tana jiran amsa yasashi cewa"ke zaki hau da kanki",
hannu tasa ta ruke ha6arta ta fara tunanin yadda zata hau saman Motar,kallonshi tayi tace"Ya Handsome kodae ka idasa sauke glass d'in sai ka matsa man in shigo ta nan inda kake",wani kallo ya bita dashi kafin ya kai hannu ya bud'e k'ofofin ta gaba,juyawa yayi yace"ki shigo",
"Ta ina?"ta tambaya,
"Ta ina kika san ana shiga Mota?" hannu ta d'aga ta nuna mashi k'opa,kai ya gyad'a mata alamar tanan zata shigo,da sauri ta kama handle din ta ja sai gashi ta bud'e,shigewa tayi ta rufe kopar da karfi don kar yace bata rufu ba irin rannan,tsakiyar backseat d'in ta zauna ta kame wuri guda,wani irin ni'imtaccen sanyin Ac had'e da kamshi suka fara ratsata sai faman sakin Murmushi take,d'aga kai tayi suka had'a ido da Haisam ta cikin madubin gaban Motar,dariya tayi mashi tace"ashe wasa kake man kace ta sama ake shigowa",
shi dae kallonta kawae yake bai ce komai ba,
"to na shigo Ya Handsome mu tafi",
D'age mata gira yayi ta cikin madubin"ina?"
zaro ido tayi"ba kai kace in shigo ba,ai nayi zaton Makarantar zaka kai ni fa",
K'ara gyara kanshi yayi a jikin headrest,
"yeah can zan kaiki amman in kin zauna a inda ya dace",cikin rashin fahimta tace"to a ina zan zauna?"hannu ya kai ya d'auke jakarshi da yatsanshi ya nuna mata kujerar dake a gefenshin tace toh,maimakon ta bud'e Motar ta fita ta zagaya sai ta kutsa ta tsakankanin kujerun gaban,har saida haisam yaja gefe guda,zaunawa tayi a kujeran gefen nashi ta kalleshi,
"to na dawo",
kai ya d'aga mata ya maida jakar baya daga haka ya ja Motar suka fara tafiya,
"Ki sauko bag d'in mana"yace mata ganin ta takure don da jakar a bayanta ta zauna,curo jakar tayi ta aje ak'asan seat din,
"wllh sanyin ya fi yawa anan gaban"ta fad'a tana lullu6e jikinta da hijab dinta,hannu ya kai ya rage mata Ac din ba tare da yace komai ba,curo hannuwanta tayi daga cikin hijabin jin sanyin ya rage ta kalli haisam da idonsa na akan hanya cikin natsuwa yake driving din,
"Ya Handsome"ta kira Sunanshi,d'age mata gira yayi alamar amsawa ba tare da ya kalleta ba,
"Wai kaima abun dubiya ne ka kawo man jiya?"shiru ya d'an yi kaman ba zaice komai ba, ganin tayi kasak'e tana jiran amsarshi yasa shi cewa"ko nayi laifi ne?",
Da sauri ta girgiza kai"a'a ba kai laifi ba,kawae dae naga kayan da yawa nasan ka kashe uban kud'i amman naji dadinsu wllh,kasan mi?" kai ya girgiza still idanunsa na a kan hanya,
"Duka fa ice cream d'innan roba ukkun ni kadae na shanye su,na bar masu Yoghourt din,amman su d'aya d'aya suka d'auka aka bani sauran roba d'ayan ka ganshi ma nan a jakata zani Makaranta dashi harda ma fruit na d'ebo,naso ma in aje ice cream d'in shima roba d'aya amman na kasa saida na shanye shi duka tun jiyan sannan hankalina ya kwanta"ta k'arasa tana ta dariya,
sai lokacin ya d'an kalleta yace"kina shan sanyi da yawa zaki ciwo fa",
langa6ar da kai tayi cike da shagwa6a"to ai bakina ne bai man dad'i shiyasa da nasha naji yana da d'an banzan dadi na kasa hakuri saida na shanye shi duka"d'an Murmushi yayi ya cigaba da driving,
"Thank u so much Ya Handsome mai kirki,May Allah give u more Money"yadda tayi turancin gwanin dad'i ba kaman da yake Muryarta har yanzu akwae d'an sautin fulani dama kuma in bafullatana tayi turanci sound d'in ba dai dadi ba,
Juyowa yayi ya kalleta"Ameen yar fillo" fuskarshi d'auke da Murmushi yayi maganar,turo baki tayi sai kuma tayi dariya tace"ai kai Yayana ne ko kace man hakan bazan ji haushi ba",
cigaba yayi da driving fuskarshi a sake,can tace"Wai Yaya Handsome kasan makarantarmu ne?naga muna ta tafiya kuma baka tambayeni inda take ba,
"Kaman haka"ya bata amsa,
"to ya akai kasan Makarantarmu?ko ka ta6a kai wata ne?ko kana da Budurwa acan ne?"
"bani da ita",
"Budurwar?"kai ya daga mata alamar eh,
"To ya akai baka da ita?baka ta6a cewa kana son wata bane?",yace"yea",
"kuma wata bata ta6a cewa tana sonka ba Ya Handsome?kai ya daga mata alamar eh,jinjina kai tayi"nasan akwae masu son ka kawai tsoronka suke ji balle su gaya maka kasan fa ko Ya Handsome,wllh in Mutum bai sanka ba da ya ganka zai yi tunanin kai masifaffe ne mara kirki,nima da farko nayi tunanin hakan"shiru ta d'an yi kafin taci gaba,
"Don dae ni k'arama ce da sai ka so ni,kuma ma ni ko na gama Secondary Skul ba zan yi aure ba sai na zama likita na fara aiki ma",
Wani kallo ya juyo ya yi mata kafin ya maida idon kan hanya yace"to ko in jira ki ne?",
zare ido tayi"ka jirani har in zama likitan?"
"Yeah,
"tabb lokacin ai ka fara zama tsoho",d'an jinjina kai yayi da d'an Murmushi yace"ba zaki so tsoho ba kenan",
"Gaskiya lokacin fa ni nazama babbar Budurwa kuma sai in auri tsoho,kuma kai ai yanzu yakamata kayi budurwa ko kayi aure kaima kaman abokinka,in kana so sai in yi ma Budurwa a Makarantarmu, a Ajinmu akwae wata Sofiya Moussa tana da kyau,kasan mi?" Haisam da yayi still yana saurararta ya girgiza mata kai alamar a'a,
"Itafa Safiyar buzuwa ce yar Nijar baka ganta ba fara ce sosae tana da gashi,kuma doguwa ce,nasan in ta ganka da gudu zata amince don yan Makarantarmu ko Malami suka gani mai kyau mai yin gayu sai su fara sonshi kaga sunata rububinshi balle kai,in gaya mata kana sonta?"
D'age gira yayi ya d'an kalleta itama shi take kallo tana jiran amsarshi yace"wa kenan?"
"Safiyar",
girgiza mata kai yayi"bansa ki ba",
gyad'a kai tayi tace"shikenan dama ba lalle ma ka sota ba don k'aton baki ne da ita kuma hak'oranta sun d'an turo haka,gata bata da jiki wllh kaman sandar suluka take,cewa ma akai na fita kyau sosae fa kawae dai tafi ni fari sosae don ita har tayi kaman zabaya kuma ta fini tsawon gashi amman na fita yawan gashi,kuma ni duk in za'ai wani abu a makarantar ana za6ar masu kyau harda ni ake sawa ko a House d'inmu in za'ai inspection nice Flower Girl",jinjina kai yayi ba tare da ya ce mata komae ba,
shuru sukai na wani d'an lokaci can tace"Yaya Handsome kayi kyau sosae wllh,wannan kayan in ka sasu k'ara yin kyau kake ko ranar dana fara ganinkan nan ka sasu kayi kyau kaman Aljani,akwae irinsu na mata ko?"kai ya daga mata alamar eh, tace"aikam nima
idan na zama Doctor irinsu zan rinka sawa"jinjina kai ya k'ara yi daga haka suka iso bakin Main Gate na shiga kwalejin gwamnati ta yan mata dake a Katsina.
*_💖A SANADIN MAKWABTAKA💖_*
_*(Love and Destiny)*_
_*BY ZAINAB LALUH*_🌹
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
*4️⃣6️⃣*
.......
Suna shiga ta cikin gate d'in fatuu ta kalleshi,"lah Ya Handsome ashe da gaske kasan makarantarmu ɗin" Murmushi yayi baice mata komae ba yana ci gaba da shiga cikin Makarantar gaba d'aya hankalin Mutane ya dawo kan Motar ba kamar Students dake ta faman shigowa,
"Yauwa Ya handsome wannan gate ɗin na farko ne section dinmu",
Juya kan Motar yayi yai horn don a idasa bud'e mashi d'ayan 6arin gate d'in,lek'owa Maigadi yayi koda yai arba da Motar da tai horn d'in da sauri jiki na kerma ya shiga bud'e d'ayan side d'in don a zaton shi Babban bak'o ne yazo Makarantar kamar yadda aka saba yin Manyan Baki,kutsawa yayi cikin Makarantar ya nufi gaban Admin Block inda akai parking wasu motocin ciki harda ta Principal ya parker shima ba tare da ya kasheta ba,
kallon fatuu yayi tare da lumshe ido"here we come",calmly yayi maganar,
yar dariya tayi ta kai hannu ta ɗauko jakarta dake aƙasan seat,
"Zarah"taji ya kirata,