Sashe 123
Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Yauwa to tunda a jirgi ne ma kaga sai kace a biyo nan da kai zaka d'auki k'anwarka in kuka zo sai a zuro man igiya yadda ake yi a film sai kawae mu tafi in muka koma gida sai in kira su gwaggon in sanar dasu ni na koma gida" shiru yay kawae yana binta da kallo kaman zai yi dariya a shagwa6e ta langa6ar da kai tana ce mashi don Allah da bud'ar bakinshi sai ce mata yay "yaushe zaki girma Zarah" wani kallo tayi mashi tace "bana girman ba" d'an shaking head d'inshi yay alamar a'a bata girma ba ta tura baki tana cewa ita ai ta gaji da garin ne gida take son dawowa yace ta kwantar da hankalinta kaman gobe ne, ganin suna ta Magana bai ganin komae sai shuke shuke yasashi tambayarta tana ina ne tace tana bakin gari nan keda network ta juya wayar tana nuna mashi wurin yace bata jin tsoro ita kadae tace tsoron mi ai koda daddare zata iya zuwa wurin ba abunda zai sameta, yar hira suka k'ara yi yace ta koma gida Magrib ya kusa tace to amman kar ya kashe zata tafi suna hira har tazo inda ba Network yace owk, tafiya take ta raba hanya biyu tana bashi labarin garin nasu da yadda kowa ke mamakin girman da tayi a haka har tazo inda ba Network kiran yay disconnect da kanshi lokacinne kuma aka danna wani irin Horn mai karfi a bayanta har saida ta tsorata ta juya da sauri, da mamaki take bin Motar da tayi mata horn d'in da kallo wadda peugeot ce 406 irin wadda ta fasa ma glass lokacin da haisam ya mareta saidae ba Colour d'insu d'aya ba Wannan Navy blue ce, ganin tayi tsaye kan hanyar yasa na cikin Motar sauke glass a harzuke yace "ke mahaukaciyan inane nan d'in d'akin uwarki ne da zaki raba hanya biyu anata maki horn bazaki matsa ba!!" da hausa yayi mata Maganar don daga yanayin shigarta ya fahimci ba lalle in yar rugar bace, sototo tayi tana binshi da ido da alamar mamaki a fuskarta taji ya k'ara cewa "bazaki tashi man a hanya ba sai na bi ta kanki ne",
a fusace tace "to shine sai ka zagar man uwa dake kwance cikin k'asa" bud'e Motar yay a fusace ya fito, dogo ne sosae don har yafi haisam tsawo saidae sam baida jiki yana sanye da jeans da t-shirt kallo d'aya zakai mashi ka gane bafullatani ne daga yanayin fatar jikinshi dake fara sannan sumar kanshi ma a nad'e take duk da bata da tsawo sosae kallonta yay a k'ule yace "Who d hell are u da baza'a zageki ba!" kallon up and down tayi mashi kafin tace "to wllh duk da an hana ni rashin kunya bazan kyaleka hakanan ka zagar man uwa ba don haka badae uwata ba" kallon mamaki ya bita dashi yace "badae zagina zaki ba!" tace "ai baka ji na zage kaba ko amman dae kasan in Mutum ya zagi iyayen wani bai rama ba to nashi ya zaga don haka taka ka zaga" a fusace ya idasa fitowa tana ganin hakan ta fara tattare rigarta dama akwae dogon wando a ciki nan take ya gane guduwa zatayi hakan yasashi tsayawa suna kallon kallo ta kumburo mashi baki, juyawa yayi ya koma cikin Motar dama a kunne take ya rufe tana dai tsayen bata kauce ba aikau ba zato ba tsammani yayo kanta da Motar tayi tsalle gefe guda hakan baisa ya kyaleta ba yayi kanta gadan gadan aikuwa ta watsa a guje don ta lura yafita hauka kan kace mi tayi mashi nisa don hanyar akwae yashi ya hanashi yin gudu sosae yana ganin ta 6ace ma ganinshi ya wani daki steering Motar yaja dogon tsoki abunda yafi bashi takaici wai ace wannan yar kankanuwar yarinyarce zata zageshi jan Motar yay ya k'ara yin gaba kafin ya karya wata kwana,
Ranar laraba tunda sassafe gwaggo tayi sallama da kowa bayan an had'a mata sha tara ta arziki su Fatuu ne yan rakiya saboda Baffanta ne zai kaita jimeta a Motarsu Hijet da suke kai kaya kasuwa daga can sai ta hau Motar Katsina ko Kano, ita da Fatuu da kamalu da Mino ne abaya sai gaba Baffanta da Amadu Fatuu harda kukanta na atafi da ita, banza gwaggon tayi da ita sai yadikko ce ke rarrashinta tana cewa tayi hakuri ta k'ara kwanan masu biyu basu gaji da ganinta ba kuma in ta tafi ai sai an k'ara ganinta ko, Bayan sun dawo daga raka gwaggo kwance tayi saman gadon tana matsar kwalla a haka bacci yay awon gaba da ita lokacin data farka ne yadikko ta nuna mata abun karin kumallonta, bayan ta wanko bakinta rai a jagule take tsakuran abincin ganin tak'i sakin jiki yasa yadikkon ce mata tayi sauri ta gama ta shirya suje cin Kasuwar babbar hanya ita dasu mino tace bari ma tayi ma Kamalu Magana don tasan duk sati yana zuwa sarin rake, tana jin hakan ta d'an ji sanyi bada jimawa ba yadikkon ta dawo tace tayi ma Kamalun Magana zasu tafi tare, wuraren karfe sha biyun rana sun gama shirin zuwa kasuwar Fatuu tasha ado da shaddar da haisam yayi mata da babbar salla sosae yadikko da k'annenta ke yaba kayan bata 6oye mata ba tace ai Ya Handsome ne yayi mata don dama kullum ne sai tayi masu firarshi kaf ta basu labarin abubuwan da yake mata sosae suke yaba kirkinshi da kakarshi Hajiya, cike da tsokana yadikko tace kodae saurayinta ne don wannan hidiman tayi yawa, da sauri ta girgiza mata kai tace a'a ita ai bata da saurayi don karatu take son yi ta zama likita kuma shima baiyin soyayya koda ma zaiyi bazai yi da ita ba tunda ita karama ce shi kuma babbane kuma d'an gayu ita yadikko dan ta6e baki kawae tayi, itama Mino kwalliyar shaddar tayi cikin kayan da aka bata gwanin sha'awa yadikko ke kallonsu inda so samu ne Fatun ta dawo hannunta saidae ita kanta tafi mata sha'awar zama acan hannun gwaggon, lokacin da suka fito tsakan gidan gaba daya wadanda ke wajen sakin baki sukae suna kallonsu ciki harda Altine da tayi ado da kayan fulani suma zasu cin kasuwan ko ta kansu Fatun bata bi ba sukae fucewarsu a waje suka samu Kamalun harda ma Amadu shima yayi gayu da kananun kaya ba 6ata lokaci suka kama hanya, tun akan hanyar ake ta faman binsu dana mujiya don ba'a saba ganin irin shigar da suka yi ba wasu mutanen da basu iya hakura har tambayar Kamalu suke wai bak'i sukae ya basu amsa da eh wadanda suka san Fatuu kuma ya gaya masu itace da al'ajabi suke kallonta koda suka isa kasuwar ma nan ma dae abun kallo suka zama sai kace ansamu tv anan kuma suka hade da Jibo Mutumin da shine sanadin komawar Fatun Katsina wato wanda ta jefar ma Akuya ta mutu, yana sanye cikin shigan Fulani riga da wando da takalma fatalo shima kasa hak'uri yay ya tambayi Kamalu bak'in binni sukae yana dariya yace ya kalli Fatuu da kyau ya santa, k'ura mata ido yay saidae sam ya kasa gane wacece har saida Kamalun yayi mashi bayani sannan ya ganeta, cike da al'ajabi yake kallonta baki bude harda cewa ai shi yaga Mata wllh a tsiwace Fatun tace mashi Allah ya kyauta ta aureshi ko maza sun k'are mi zatayi dashi yadda tayi maganan yasashi cewa da kwarankwatsa itace kuwa sudae su Kamalu nata dariya, zagayawa sukae cikin kasuwa suka danyi siyayya yawanci duk abubuwan ci ne akafi saidawa su Awara, kosai, rake, danyen nono harda madarar shanu da kuma kayan noma sai yamma liss suka koma gida don daga kasuwar zagaya garin sukae har k'oramar dake bayan gidansu suka je mai tarin ni'ima da wadatar kayan itatuwa suka yi hotuna.
_____________