← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 137

Sashe 35

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Don Allah yaya handsome kayi hakuri kar kayi fushi,wllh bansan irin wannan lemun bane" kwalla ce ta fara gangaro mata a daidai lokacin ya d'ago da kansa yana kallonta itama shi take kallo tana matsar kwalla,gently yace"is okey,amman ki rage yawan surutu mara amfani" da sauri ta d'aga kai alamar toh,alama yayi mata da hannu tazo ta mike a hankali ta tsaya gefensa ya d'aga gwangwanin lemun ya fara magana a nutse"akwai lemu kala kala,wani a roba,wani a can,wani a kwalba,wasu manya wasu k'anana,so ba iya wad'anda kika sani bane lemu kawai,kar ki k'ara ganin wani yana shan wani kalan lemu da baki sani ba kice giya,Understand?" Da sauri ta daga kai,ya ci gaba"abunda yasa nace baki bukatan sa,Energy Drink ne,kuma yana da d'an karfi ne",
bude baki tayi da mamaki tace Energy..! Yace"yea,ko baki san miye energy ba?da sauri tace "nasani,is the ability to do work" cike da confidence tayi maganar d'an murmushi yayi,hakan yasa itama tayi "mi kenan yake nufi?, Tace"karfi,karfin yin aiki,shi kake sha kenan shiyasa ka ke da power?" ta fad'a tana nuna damtsen hannunshi dake a murd'e,banza ya mata taci gaba"don dai kace in aka roke ka abu bakayi da nace kabar lemun da zaka bani yanzu sai nima ka samo man iri wannan din,wallahi aiki yawa yake man,inna dawo daga makaranta sam ban hutawa ba kaman gwaggo in tana nan,fatuu yi tankad'e,fatuu dibo ruwa,fatuu fito ki shara,komai ni",

Murmushi ya sake yi yace "wannan ai ba wasu aiki bane,and being a girl dole ki koya irin wannan aikin..." tace "to ai sai in mutum aure za'a masa sannan ni kuma fa ba yanzu zanyi ba sai nan da dadewa,ba na fada maka..." da sauri yace "yea,is a child abuse,je ki daukko wani zan kawo maki wannan din" tace "toh,ta juya,ya bita da kallo,kafin ya maida kallon kan t.v.
Lemu fanta ta daukko ta dawo ta zauna a inda ta tashi,ta rike lemun tana d'an wasa da robar sai faman murmushi take da ka kalli fuskarta zaka san tana cikin tsananin farin ciki,sai kallon haisam take wanda idanunsa ke kan tv,juyowa yayi suka hada ido kaman jira take ta d'aga lemu daya tace"Allah yaya hansome kana da kirki wllh,kafi kowa na duniyar nan kirki,wai har kudin shanu gomaa ka yafe tabb,nagode thank u so much,God bless you" ta k'arasa maganar tana noke kai,gyara zama yayi ya d'an kwanta yana kallonta,
"in kuma kika karya promise din,na dawo nace ban yafe ba sai kice ni mugu ne,nafi kowa rashin kirki a duniya,right? Girgiza masa kai tayi tace"a'a ai wannan ni naja ma kaina kuma,bama fa zan kara ba tunda nasan da nayi zaka sani,ai nagan ma abubuwan da ke fadi maka abu in akayi baka nan" yace "a ina?" Juyawa tayi tana nuna dakin da taje yin fitsari tace"a cikin dakin naga wani abu babba mai uban wayoyi ajiki,kuma ma naga wasu jajayen abubuwa manne a bango,bokayen turawa ne ko?" shiru ya mata,ya lura ta cika tambaya ta rashin kan gado ita kanta ba kan gadon gareta ba,ganin tana ta kallonshi alamar jira take ya bata amsa,ya d'age gira yace"bokayen fulani ne" da farko waro ido tayi waje cike da mamaki,can kuma sai ta gane gatse ne yayi mata don gwaggo ta saba yi mata,hakan yasa ta d'age kafafunta ta tura kanta ciki tana daria gyalenta ya zamo kasa,

Dago kanta tayi a hankali suka had'a ido dashi tana murmushi tace"ashe kaima ka iya irin abun gwaggo"banza ya mata,ganin ta rungume lemun yace"kisha mana" girgiza kai tayi tace"ba yanzu zan sha ba,dashi zanje makaranta gobe in yi break" jinjina kai yayi sai kuma yace"je ki k'aro wani" daga na hannunta tayi tace"ai wannan ya ishe ni"
"What about ur friend,bazaki bata ba,ko ba school daya kuke ba?" tace"wai haulatu,ajin mu ma daya kuma seat dinmu daya da ita,tare ma muke yin break din,ai sai mu raba" shiru yayi yana tunanin halinta ne haka bata da had'ama ko kuwa don yace bai son roko shima" je ki daukko mata wani,in nace kiyi abu just do it banson jayayya" da sauri ta mik'e tana cewa"yi hakuri yaya handsome,taje ta daukko coca-cola ta dawo tana daria ta nuna mashi tace"ita haulatu tunda bak'a ce sai in bata wannan ni kuma tunda fara ce sai in sha wannan jan" ta koma ta zauna hadi da rungume roban lemunan,shidai dan murmushi yayi kawai kafin yace"karfe nawa Uncle din naki ke kulle shagon? tace "k'arfe tara da rabi ko goma cikin sanyi amman da zafi kaman yanzu yana kaiwa har sha daya" time ya duba a wayansa yaga 9:50,yace mata "shi zai zo ya tafi dake ne? tace "a'a haka gwaggo tace dai kar na bari ya tashi,amman in ban koma ba har ya tashin zata aiko ya tafi dani" jinjina kai yayi kawae yaci gaba da kallo,can ya mike don ya gaji bacci yake son yi,gashi gobe akwae aiki,ya wuce bedroom dinsa tana ta kallon bayan shi har ya shige,tana ganin ya shige ta kyalkyace da dariyar farinciki,tana tillah robobin lemun hannunta tana cafewa.

Sanye cikin jallabiya mai gajeren hannu ash color ya fito,komawa yayi inda ya tashi ya zauna yana kallon yadda take wasa da robobin lemun,dagowa tayi suka hada ido tayi dan murmushi a hankali tace"Yaya handsome" shiru yayi kaman mai tunanin wani abu kafin yace"ba sunana haka ba" sakin baki tayi da mamaki tace"amman ai haka naga ansa a jikin riganka" yace"yeah,but wannan rubutu ne kawai",
"ya sunanka to?"ta tambaya, d'an k'ankance idanunsa yayi yace"Haitham" cike da mamaki ta rika maimaita duka sunan,haisam da handsome can tace"ai to duk d'aya ne ko wancan da turanci wannan da hausa ko"d'age gira yayi yace"koh? Jinjina kai tayi"eh mana,kuma ni nama fi iya fadin handsome din kuma ai shi ya dace da kai,baka san mi yake nufi bane?" ta fad'a tana daria,dan murmushin gefe kawai yayi baice komai ba,daman saida yayi tunanin zata iya cewa sunan daya ne.

Kallon time ya k'ara yi a wayansa lokaci guda ya mike yana fadin"it's already late,tashi na raka ki" toh tace ta fara kokarin mikewa hannuwanta rungume da lemunan,ta wuce gaba yabi bayanta daidai bakin kofan fita ta juyo da murmushi tace"in ringa zuwa ina gaida ka?"daga mata kai yayi alamar eh,daga haka suka fice.

Unguwar shiru ga duhu saboda an dauke wuta,gidaje kad'an ne gaban su ke dauke da hasken wutar generator da suka kunna wasu kuma solar saidai gaban gidan hajiyan yafi ko ina haske saboda fitulun jikin gidan da suke akunne gaba daya,ko alluran mutum ta fad'i a wurin zai iya ganinta,gaban shagon Amadu ma akwai hasken kwai mai caji ga wasu mutane biyu a tsaye suna siyayya,suna kaiwa daidai rabin bangon gidan hajiyan yaja ya tsaya agaban fence itama tsayawar tayi tana kallonshi hannu yasa ya shafi forehead dinshi gently yace"Good nyt" murmushi tayi itama tace"to good night yaya handsome" jinjina mata kai ya yi daga haka ta wuce.

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching love story._

_*BY ZAINAB LALUH📲*_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

*2️⃣9️⃣*

Haisam na ganin ta kai k'arshen katangar ya juya ya nufi gida don yaga akwai mutane gaban kiosk din.
Tana gab da isa shagon Amadu taja ta tsaya tana tunanin wani abu sai kawai ta juyo ta nufi lungun dake tsakanin gidajen su da gidan hajia,daidai haisam na niyyar shigewa kwanar gate kaman ance ya juya yaga tasha kwana saboda hasken da ya haska lungun da tabi,tunani yayi a ranshi ina kuma yarinyar zata da daren nan,juyowa yayi ya tsaya yana kallon hanyar data bi,a hankali ya fara tafiya ya koma hanyar daya baro,daidai lokacin da ya kai karshen bangon ya juya yana kallon lungun lokacin ta karya kwanar dama ta shige ya daina ganinta,tsaye yayi yana ta kallon inda tabi yana cigaba da tunani,can ya ayyana kilan aikenta akai bata je ba sai yanzu,"ai kuma cewa tayi ta tambayi zata zo gidan hajiya don ta baka hakuri",wani bangare na zuciyarshi ya ayyana mashi can dai ya d'an ta6e baki hadi da d'age kafad'a daga haka ya juya ya koma gida.
Chapter 35 · 0% Book details