← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 137

Sashe 67

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ashe bak'o akayi",
ba yabo ba fallasa ya amsa mashi"umm wata ya kawo kuma ma kaman d'an uwan Hajiya ne don naga suna gaisawa",
gyada kai yayi can kuma yace"naga ma har alheri yayi maka,ai sai ka d'an samman wani abu tunda ba rabona, dama wllh fankan fayau na tashi tun jiya nike istigfari ashe ta wajenka arzikin zaizo" ya k'arasa da d'an murmushi akan fuskarshi,shi kam wanda aka ba kudin tunkan ya k'arasa maganar yake wurga mashi harara,k'okarin saka ma kud'in acikin aljihunsa ya fara yi Horn d'in da akayi ne yasasu d'aga kansu su duka,a wani irin slow glass d'in kopar driver ya sauka,zuro da santalelen hannunsa yayi yai alamar kira,don sonkai irin na wasu Mutanen da sauri mutumin da aka ba kudin ya nufi motar,alamar bashi yake kira ba yayi masa da hannun nan take yaci burki yai turus awurin shikam wanccan bawan Allah sai yayi tsaye bai tunkari motan ba gudun kada ace shima bashi ake kiran ba,haisam dake hangensa ta side mirror ganin bai taho ba yasashi zuro da kanshi ya yi masa alamar yazo da kan nashi aikam da sassarfa ya nufe shi,yana zuwa haisam ya mik'o masa kud'i masu yawa shima yan dubu dubu da gani sunfi na wancan yawa sosae,hannu na kerma ya kar6a nan take ya durkushe yana mashi godiya harda hawayen farinciki,alamar ya mik'e yayi mashi daga haka glass d'in ya fara rufewa sama yana gamawa yaja Motar mutumin na ci gaba da yi mashi godiya,ko kallon inda wanccan yake bai yi ba ya nufi d'an d'akinsu na gadi,

Uhmm har na tuno da baitin wakar Naziru sarkin wak'a da yake cewa,
*_in rabo ya tsago da kai,kuma abun ya tabbata da kai,Rabbi ne yace saida kai in saida kai kawae sai da kai,in abun yazo babu kai,rabbi ne yace babu kai,in babu kai kawai babu duk duniya ba mai sa dakai.....😍_

Duk wannan abun akan idonsu Principal da sauran malaman dake a wurin harda ma wasu Students ɗin,Murmushi principal d'in tayi bayan Haisam ya fuce ta furta"That's haisam",ba k'aramin burge duk wanda ke a wurin yayi ba,kallon Fatuu dake tsaye itama tana kallon abunda ya faru principal tayi ta kirata da sauri ta taho wurinta ta tsaya a gabanta,bin ta da ido tayi ta shiga tunanin tasan yarinyar a Makarantar,kuma tabbas ta santan don irinsu fatuu masu k'okari yawanci zaka ga duk an sansu a makaranta ba kamar ita dake a English Club na Makarantar,

"Which class are u?" principal d'in ta tambayeta,
"Am in class 3c"ta bata amsa,jinjina kai tayi ta waiga gefenta in da discipline master yake tare da wasu prefects da zasu fara taren yan makara bada jimawa ba,
"Malam Mahadi ka kaita Class"da sauri yace"Ok Ma",kallonta yayi yai mata alamar su tafi ta wuce gaba yabi bayanta daga haka principal d'in da sauran malaman da suka rako ta suka nufi cikin Admin block din,

Tafiya take hankalinta kwance sai fanan shan kamshi take,yayin da wasu Students din keta faman bin ta da kallo,shi kanshi discipline master din kanshi ya d'aure,tsananin mamaki yake ta yadda akai yarinyar keda dangantaka da Senator Ali don yafi kowa sanin halin fatuu a Makarantar shiyasa kullum cikin yi mata horo yake ita kuma tana ganin ya tsaneta ne,kasa daurewa yayi ya dawo daga gefenta yace"dama kina da alak'a da Senator Ali?",
d'aga kai tayi ta kalleshi sai kuma ta sauke kan fuska adan d'aure ta furta"eh",
jinjina kai yayi can kuma ya sake cewa"Amman ya kike dashi ne?"shiru ta d'an yi tana tunanin amsar da zata bashi, tsoronta kar tace ita d'iyarshi ce ace kuma shi yasan ya'yanshi tunda gashi ya sanshi,

"Kawu nane shi"ta fad'a cike da fargaba,
"ke yar Daura ce?"da sauri ta d'aga mashi kai alamar eh,
"To amman ya akai kike wannan makarantar"turo baki tayi"to ita ba makaranta bace?"shiru yayi ya rasa amsar da zai bata,lokacin da suka iso bakin class d'insu har ciki ya shiga da ita Malamin English dake da period d'in farko tuni ya shiga kuma shima ya ga lokacin da aka kawo Fatun, hannu discipline ya d'an d'aga mashi"Sannu da aiki malam",amsa mashi yayi da"Yauwa",kallon fatuu yayi"jeki ki zauna"ta amsa da toh ta nufi seat d'insu sallama ya yi ma malamin ya juya ya tafi,saida ta isa seat d'in nasu sannan ta tuna da Haulat ganin bata a zaune sai d'ayar da suke zama atare ita kadae dama su ukku suke zama,

Sai da malamin yaci kusan rabin first period sai ga Haulat ta shigo cikin ajin da yar sallama,nufo cikin ajin tayi sumimi sumimi zata wuce,

"From where are you?" taji Malamin dake yin note a allo ya fad'a,tsaye tayi duk tasha jinin jikinta,juyowa yayi ya kalleta,
"Baki ji bane,daga ina kike?" cikin en ina tace"daga bakin gate tare mu akai",
"Ok ki fita idan na gama kya shigo",
Magiya ta fara yi mashi tana rokon ya barta ta zauna,daka mata tsawa yayi"I said get out!kinsan kina son ki zauna a class kika ƙi zuwa da wuri",
Jiki a sanyaye ta juya zata fita fatuu dake kallonta duk bata ji dad'i ba don sai taga kamar laifinta ne da bata biya mata ba kallon Malamin tayi Cikin sanyin murya tace"Sir pls Sorry,Wllh tare muke zuwa kullum da wuri",wani kallo yayi ma fatun ta d'an marairaice mashi fuska dama suna shiri da ita saboda k'okarinta gashi tana a Club din shi,juyawa yayi yaci gaba da yin rubutu,

"Go and sit down"yace ma haulatu da har tasa ƙafarta guda waje,juyowa tayi ta dawo ciki tana zuwa saitin shi tace" thank u sir",kai ya d'aga mata ta nufi seat d'insu don ta zauna,suna had'a ido da Fatuu dake ta faman sakar mata Murmushi ta galla mata harara ta fara k'okarin fiddo English Note Book d'inta don tayi copying note d'in da malam ke yi,fatuu kuwa sai faman k'umshe dariya take don tasan laifin da tayi ma haulatun.

Tun bayan da haulat ta shigo basu samu damar yin magana ba don Malamin English din double period gareshi yana gamawa kuma Malamar dake da Next period ta shigo har saida akayi break sannan fatuu ta kalli haulat,

"Sorry k'awata wllh Mantawa nayi in biya maki saboda...." a harzuk'e Haulat ta katseta"Yar rainin sense,ba dole ki manta dani ba ankawo ki cikin had'addar mota,sanyin Ac ya ratsaki ta ina zaki tuna da wata Haulatu"fashewa Fatuu tayi da dariya,
"Ya akai kika san a Mota aka kawo ni?",

Dan ta6e baki Haulatu tayi"harma wanda ya kawo ki na sani ba Dan gidan Hajiyar Sanata bane?"da sauri fatuu tace"shine ya akai duk kika sani wai?",

"Inata jiranki naga baki zo ba kuma nasan kin tabbatar man yau zakizo to don kar mu makara yasa na nufi gidanku ina zuwa bakin kopar gidan Umar na gidansu Bello yace man wani mai mota ya tsaya kin shiga kun tafi,ina jin hakan na juyo na nufi bakin hanya inata tunanin ko waye ya d'auke ki don sam ban kawo d'an gidan hajiya araina ba,koda nazo bakin hanya wani Mutum yace man Bus ta wuce baki ji takaicin dana ji ba dole na hawo mashin koda na iso har an fara taren yan makara,a bakin gate d'inne naji prefects nata Maganar Motar da aka kawo ki suna kuma zuzuta Mutumin da ya kawo kin,kinsan fa A.Sp Asma'u Kabeer har tambayata tayi wai ya kuke dashi.....", katseta Fatuu tayi da sauri,"ya kika ce mata muke dashin?",
Dariya haulat tayi"Yo cewa nayi Yayanki ne",

"Yauwa Allah gwara da kika ce masu hakan yan sa ido kawae,wai kinga yadda aka rink'a bin Motar da ya kawo nin da ido sai ma da ya fito zai gaisa da Principal ashe ya santa innalillahi!ke kinga kuwa yadda ake kallonshi",

"Ai naji ance wai har kud'i yaba masu gadi,Binta Musa duk ta rud'e wai yadda ya kira Baba maigadi mai kirki ya bashi abun kaman a film..." da sauri fatuu ta amshe"Wllh baki ga uban kud'in da ya mik'o mashi ba,dafa inaga Maigadi Masifaffen hana shi yaso yayi wanda aka bashi aikau ashe Ya Handsome d'in na kallo shine ya kira shi shima ya bashi",

"Ai in gaya maki suna can sun rud'e sai faman santinshi suke yi anga Mijin Novel,Labour Prefect Binta Musa ma wai zata zo kamun k'afa a wurinki,kinsan ma lokacin da aka samu a layi za'a kaimu muyi punishment ita tasa ni in gudo wllh sauran na can suna shara wasu na wankin toilet,ke hardae Sp Ni'imatu Abdullahi da take miskila saida ta tanka akanshi wllh",Wata Mahaukaciyar dariya Fatuu tayi,
"Ƙyale banzar tazo d'in,yama za'ai Ya handsome ya sota da fuskarta kaman an ƙona baƙar leda",hannu Haulat ta kai ta d'an bugi kafadarta"wllh baki da kirki fatuu,aikam tana da kyawunta daidai gwargwado kawae don dai tana bak'a sosae ne,kuma ba ita kadai ke son nashi ba Asma'u Kabeer ai ba laifi tana da kyau kuma wankan tarwada ce...."

"Allah yasa wankan kada ce wllh Ya Handsome ba abunda zaiyi da ita,ce man fa yayi shi baida budurwa",
ita dae haulat dariya kawae tayi tace"wai bazamu fita break bane sai an dawo",

"Wane break ai yau a aji zamu yi break d'inmu basai munsha wahalar fita ba"Fatuu tayi Maganar yayin da ta kai hannu ta d'aukko jakarta ta zage zip, fiddo abubuwan dake aciki tayi ta d'aura su saman desk,bin yoghourt da fruit da k'aton biscuit d'in haulat tayi kafin tace wani abu Fatuu ta fara bata labarin kayan dubiyar daya kai mata jiya da daddare da biscuit had'i da kud'in daya bata lokacin da ya kawota,

"Kai Amman Mutumin nan yana da Mugun kirki wllh...." katseta Fatuu tayi"Mugun kirkin ma,ba kinga kayayyakin daya siya man ba lokacin da kika zo gaida ni",
"Gani kai,nida har na samu rabona,da wani ne kika ma laifin da kikai mashi tun farko ko kallonki ma zai sake yi ne in ma bai d'au mataki akanki ba kenan,amman shi ji abun arzikin da ma yake maki wllh yaji dadi,ga kyau ga kudi ga kirki ko nayi rantsuwa bazan yi kaffara ba samun irinshi a wannan lokacin zaiyi Matuk'ar wahala wllh", Murmushi kawae fatuu ke saki ta bud'e masu biscuit da yoghourt d'in suka fara ci,
Chapter 67 · 0% Book details