← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 137

Sashe 116

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"to ko in had'o maka tea?" Tk d'in ya tambaya, shiru ya d'anyi sai kuma ya d'aga mashi kai alamar eh, cike da jin dadi ya nufi hanyar fita shi kuma ya fara cin abincin ba'a dau wani dogon lokaci ba Tk ya kawo mashi tea d'in ya zauna yana mashi yar fira har ya gama ya dauke abubuwan abincin kafin yayi mashi saida safe, cigaba da abunda yake yayi wayarshi ta fara ringing ya kai hannu ya d'auka, Murmushi ya saki ganin mai kiran nashi wato Hajiya, handsfree yasa ya aje wayar agefe hajiyar tayi mashi sallama,
"Sweetheart hope u'r work" ya fada idonshi akan screen,
"Lafiya lou nike kaifa?"
"Same" ya bata amsa a takaice,

"Yau mi kaci ne?" ta tambaya, har saida ya d'anyi Murmushi kafin yace mata abinci, tace "da safe kaci abinci?" yace mata eh yaci a wurin aiki, ta tambayi da rana fa yace mata yaci a gidan Abbas,
"To yanzu da daddare fa?" ta sake tambaya, d'an girgiza kai yay kafin yace "in kin damu da wannan ki dawo mana" a d'an fad'ace tace "nima ai nan d'in kaman akan k'aya nike kawae banda yadda zanyi tunda an fi karfi na" dariya yayi har hakoransa suka bayyana kafin yace gidansu ne k'ayar tace eh mana,
"Pls tell me kaci abinci yanzu kuwa, kodae insa Saude ta dawo ne dama don nasan tukur ya iya dafa abinci shiyasa nike kyaleta sai na dawo itama ta dawo amman yanzu ko don kai inaga zan sa ta dawo kawae tunda a gaban idona ma ba son ci kake ba balle yanzu da bani ba kuma mai dafa makan" d'an ta6e baki yay kafin yace ta kyaleta kawae sai ta dawo tace to ya fad'i mata abunda yaci yanzu,

"Zarah ta kawo man" daga jin muryarta taji dadin hakan tace "yauwa naji dadin hakan wllh sun kyauta Allah ya saka, in kana son wani abun zaka iya sa tukur ma yayi maka don ya iya dafa abinci sosae" amsa mata yay da owk daga nan suka ci gaba da yin hira yana daddana Computer din. Washe gari Friday misalin Karfe bakwae Fatuu ta zo part d'inshi ganin bai cikin parlon yasa ta kware baki tana yin sallama sai gashi ya fito cikin suit Maroon Colour, sakin baki tayi tana kallonshi hakan yasa yay mata wani kallo mai kaman harara ta saki Murmushi, k'arasowa yay cikin falon ya zauna ganin tayi tsaye yace mata ta zauna mana sannan ta zauna ta gaidashi tana ta Murmushi dae, bayan ya amsa ta nuna mashi d'an basket da ta d'aura kan c-table tace "gashi nan abun kalaci ne na kawo maka" d'an waro ido yay ya kalli basket d'in kafin ya maido idon kanta calmly yace "breakfast dis early?" tura baki tayi tace "to ba aiki zaka tafi ba shiyasa ai na kawo maka da wurin" still idonshi akanta yace "ban iya breakfast a wannan time en" wani kallo tay mashi sai kuma ta juya mashi bayan kanta tana fad'in "Allah sai kaci shi" bin ta da kallo yay da d'an murmushi akan fuskarshi sanin in ya biye mata haka zasuyi ta jan magana kuma so yake ya tafi yasashi cewa ta had'a mashi amman d'an kadan in yaci da yawa zai iya yin amai ne da sauri ta kalleshi ta washe baki tace to, had'a mashi ta shiga yi dama an sako cup da spoon don ruwan tea ne acikin flask da ledar biredi mai kyau sai kayan hadawa madara da milo da sugar a gefe sai kuma soyayyen kwae rufe cikin bowl, komi sai ta tambayeshi in yayi bayan ta gama ta koma ta zauna kan carpet tana wasa da yatsunta shi kuma yana cin breakfast din a nutse can ya tambayeta ita ta yi breakfast dinne tace a'a sai ta koma gida, jinjina kai kawai yay don sauri yake, yana gamawa yace ta tafi da kayan tace ai ance in ya d'iba ta kaima Tk sauran ya amsa da owk yana nufar Bedroom dinshi, brush ya sake yi kafin ya fito ya shiga d'ayan d'akin bada jimawa ba ya fito hannunshi ruk'e da bak'ar jaka ya nufo falon, saida ya kira Tk a waya lokacin baima tashi daga bacci ba yace mashi in ya tashi yazo part d'inshi ya d'auki breakfast cike da girmamawa ya amsa mashi kafin yayi mashi adawo lafiya, ce mata yay tazo ya ajeta gida ta mik'e da sauri tabi bayanshi,

Ana gama sallar Juma'a gwaggo tace ma Fatuu taje taga in Haisam ya dawo daga aiki lokacin ta ci gayun juma'a da d'aya daga cikin jallabiyun da Najeeb ya siya mata ash colour tasha adon duwatsu sai salki take, koda taje bai dawo ba sai kawae ta dawo ta d'auki rigar da gwaggo tace ta ba Haulat cikin kayan da aka siya matan da su kayan shafa ta tafi kaima Haulat, sosae tayi farinciki tana ta faman godiya harda innarsu sai washe baki haulat take don sam bata da jallabiya dama, sosae kuma ta yaba ta jikin Fatun gab da la'asar ta dawo gida ta k'ara zuwa ta duba ko haisam d'in ya dawo ta iske bai dawo ba,sai bayan sallar la'asar Amadu ya shiga yace ma gwaggo gashi nan ya wuce dayake tace in yaganshi ya sanar mata,zumbur Fatuu ta mik'e dama suna zaune a tsakar gidane don inuwa ta sauka, Kitchen ta nufa ta d'auki kayan abincin ta tafi kai mashi, da sallama ta shiga cikin falon saidae bai ciki sanin bai dade da dawowa ba yasa tayi tunanin kilan wanka yake, wuri ta samu ta zauna bayan ta d'aura basket d'in a saman c-table shiru bai fito ba hakan yasa ta d'auki remote ta kunna tv taci gaba da kallo abunta tun tana zaune har ta d'an kishingida sai can bayan wani lokaci ya fito cikin Sportswear suna had'a ido ya bud'a mata ido ita kuma tayi mashi dariya, wuri ya samu ya zauna ta gyara zamanta dama a d'ayan bangaren inda take zama ta zauna gaidashi tayi kafin tace "nayi kyau ko?" kai ya d'aga mata tace "cikin kayan da abokin nan naka ya siya manne wai ya sunanshi?" shiru ya d'anyi sai kuma a hankali ya furta "Najeeb" jinjina kai tayi ta kuma cewa "amman dai yana da kirki kaman kai hakanan bai sanni ba ya kashe uban kud'i ya siya man kaya,Allah ya saka maku da Alkairi ya saka ku a Aljanna ku duka" acikin ranshi ya amsa fuskarshi da d'an Murmushi don yadda tayi Maganar kaman ba ita tayi ta ba,
"Yace yana gaidaki ya tafi d'azun" taji ya fad'a, da sauri ta kalleshi tace "kenan ya tafi kasar da yace man can yake?" kai ya d'aga mata tace "wayyo Allah ya kaishi lafiya" amsa mata yayi da amin ta nuna mashi basket tace ga abincinshi nan ta zuba mashi, shiru yayi yana kallonta har saida ta maimaita mashi sannan yace yaci abinci a wurin aiki tace to sai yaci da daddare, d'aga mata kai kawae yayi alamar to, sai kuma yace in taje gida ta fad'i adaina wahalar yin abinci dashi tunda yana ci awurin aiki da safe kuma baiyin breakfast da wuri tace "to da daddare fa?" yace "nafi son light food so Tk zai man wannan" jinjina mashi kai tayi can ya mik'e yace mata zai tafi gym,mik'ewa tayi itama tace "inzo in raka ka" girgiza mata kai yay yace "yawon zai yi yawa" daga haka ya nufi dakin lab ya d'aukko jakarshi ya fito suka fita tare, saida ta raka shi har parking space ya fiddo bike dinsa tace don Allah ya d'anata amman sai ya girgiza mata kai alamar a'a, tadashi yay ya fara tafiya a hankali yace suje suka tafi tana gefenshi sai tura baki take saboda yak'i goyata shidae sai murmushi yake kawae ahaka har suka je daidai gidansu sannan yasaka helmet ya fuzgeshi da gudu tana ta kallonshi har ya 6ace ma ganinta,tana shiga gidan ta nufi gwaggo dake zaune ta shiga fad'i mata abunda haisam d'in yace game da abincin da ake kai mashi, yar dariya kawae tayi tace ma Fatun ta kira mata shi a waya, farko data kira bai d'auka ba sai lokacin ta tuna tace mata ai fa ya fita yanzu da k'atoton mashin d'inshi kilan bai sauka ba, bayan wani lokaci sai gashi ya biyo kiran ta mik'a mata wayar, d'auka tayi ta kanga ta a kunnanta yana jin muryar gwaggon ya gaisar da ita ta amsa tace mashi taji sako wurin Fatuu ai ta d'auka anzama d'aya yana murmushi yace mata hakane tace kuma a ina yaga in uwa tayi ma danta abu yake zama wahala, nan ma dae Murmushi yayi kawae cike da zolaya tace mashi kodae bai jin dadin abincinne yaji shi ba irin wanda ya saba ci ba, wannan karon har saida yayi yar dariyar da itama taji sautinta yace mata ba haka bane tace to dole za'aci gaba da kawo mashi ai na d'an lokaci ne ko in yaje aikin ya rink'a cin kad'an in ya dawo sai ya k'ara, cike da girmamawa ya amsa mata da to kafin yayi mata godiya sukae sallama,
Chapter 116 · 0% Book details