← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 137

Sashe 37

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tsaye Haisam yayi cikin center din yana haska gidajen wurin da fitilan wayansa,kokari yake ya gano ko akwai kango a wurin,sai dai a iya haske-hasken da yake baiga wani kango ba yawancin uncompleted buildings din dake layin duk arufe suke da kofofi wasu Gate,dan k'ara gaba yayi yana ci gaba da haskawa har yazo kusan karshen layin baiga kango ba hakan yasa ya fara tunanin ko he was wrong about d girl..."

Daidai saitin kafafun fatuu Goga yazo ya fara kokarin cire belt din tsohon jeans din jikinshi,duk da rirriketan da sukai bai hana ta girgixa kai ba tana dan motsa kafafunta kad'an saboda danne su da Gaye yayi,ga wani gurnani da take,ganin goga na k'okarin cire wandonsa yasa ta k'ara karfin gurnanin da take yi......

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching love story_

_*BY ZAINAB LALUH📲*_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

*3️⃣0️⃣*

Juyawa haisam yayi da niyyar barin layin gurnanin da fatuu ke yi ya sauka cikin kunnuwansa abun ka da dare gari yayi tsit da sauri ya juya baya trying to locate inda abun ke fitowa,yana d'an kara taku ya ga kofan shiga wurin wanda take bude ba kofa daidai lokacinne kuma fatuu ta kara k'arfin gurnanin,da sauri ya kutsa kai without second thought ya nufi inda yake jin abun na fitowa,
".....dallah Gaye ka riketa da kyau,wai ya zaka bari k'aramar yarinya tafi karfinka ne,na gaya maka idan kai bazaka yi ba mu wllh sai munyi......."
Wannan maganar ta Goga ita tayi ma Haisam jagora zuwa dakin da suke,yana isa bakin kofan d'akin ya haske su da fitilan wayansa da take da haske sosai lokacin goga na niyyar afka ma fatuu,ai suna ganin an haskesu su duka suka nufi windunan wurin da gudu zasu dire,cikin zafin nama haisam ya bisu yana k'okarin kamo goga wanda ke gudu saman wandonsa rik'e da hannunsa,cakk haisam ya tsaya sakamakon wani rad'adi daya ji tun daga kasan kafarsa har tsakiyan kansa,a hankali ya maido kafansa ta dama baya ya haska kafan hagunsa don a jikinta ne yake jin rad'ad'in,kwalba ce ya taka ta hudo ta k'asan takalminshi ta shige cikin kafan sosai,a hankali ya duk'a yasa hannunsa na dama yana kokarin cire kwalbar,sai dai ba karamin yanka tayi masa ba radadi yake ji sosae,runtse idanunsa ya yi yasa hannu ya cije lip dinsa na k'asa da k'arfi ya fisgo ta,har saida yayi dan sound a hankali"ahhh..." saboda azabar da yaji,aikuwa nan da nan jini ya fara zubowa kaman yana jira...

Ita kam fatuu tana ganin duk sun ruga ta fara kiciniyar kwance hannuwanta cikin sa'a d'aurin ya saki ta samu ta fiddo hannuwanta a gigice ta mike ko tsayawa kwance bakinta bata yi ba ta nufi hanyar fita cikin rashin sani saboda kidimewa da tayi ta kaima bango karo a tunaninta nan ne kofar fita,taga-taga tayi tayo baya gabadaya zata fad'i,ganin haka yasa Haisam da ke haskata tun lokacin data mik'e tarbota cikin zafin nama don ba k'aramin buguwa tayi ba,ba kamar goshinta ji kake wani K'UMM!,
Sosai ya rungumeta ganin tana ta son kwacewa ta gudu a hankali ya dan duk'a yakai bakinsa saitin kunnanta wanda kanta ke saman cikinshi cikin calm and cool voice yace "is okey,u are safe now" lokaci guda ta gane voice dinshi hakan yasa ta lafe ajikinsa ta kankameshi sosae jikinta sai faman rawa yake da gani ta razana sosae,yayin da shi kuma azaba da radadi keta damunsa a tafin kafarsa haka ya daure ya kai hannu ya kwance hanki din dake rufe da bakinta ya jefar cike da kyankyami don k'auri kawae yake,

bayan wani dan lokaci ganin ta daina kermar ya janyeta a hankali gefe guda ya haska mata tasa takalmanta ya duka ya d'aukko gyalenta dake agefensa ya d'an yarfe shi sannan ya mika mata,ta amsa ta yafa shi saman kanta wanda tuni gashinta ya warware yayi kaman fanka don tana da cikar gashi sosai,a hankali yace"mu tafi"yayi maganar yana haska mata hanya,da kyar ya daga kafansa ya fara tafiya duk da zafin da take masa haka ya daure ya rik'a takata a hankali jini naci gaba da zubowa saboda taka tan da yake,
Tana gaba yana bin ta a baya yana haska mata hanya har suka iso bakin kofan fita daga ginin gidan,yana k'okarin sa kafanshi a hankali ya fita yaga ta juyo da sauri zata koma ciki tsayawa yayi yana kallonta ganin haka yasa da sauri tace"lemunana zan daukko" ji yayi kaman ya fizgota ya wawwanka mata mari saboda haushi da ta bashi,tsawa ya kwatsa mata yace"C'mon leave this place...!bakinki ne lemun" da sauri ta juya taci gaba da tafia sumi-sumi.
Tana zuwa k'arshen lungun gidan Hajiya ta juya zata karya kwanar gidansu Haisam dake can bayanta saboda a hankali yake tafiyan ya dan d'aga murya yace"muje gidan hajia" ba musu ta juya ta nufi gidan,ta riga shi isa hakan yasa tayi tsaye a bakin kofan parlonsa,bayan d'an lokaci ya k'araso tana ganin ya shigo part din ta tura kopan falon da sauri ta shige,tsayawa yayi bakin tap din da ake ba flowers ruwa ya wanke kafan da takalmin wanda gaba daya kalansa ta koma ja saboda jinin da kafansa keta fitarwa har lokacin,abunka da dan madara,tana shiga ta nufi can gaban armchairs inda tayi kneel down d'azun ta durkushe,

Shigowa yayi bai ko kalli inda take ba a hankali ya nufi kujera ba tare daya cire takalman kafansa ba ya zauna,hannu ya kai ya dauki tissue box ya 6allo mai d'an yawa ya ninninkata kafin ya tura kasan foot dinsa dake zubar da jini,bayan yayi hakan ya mike ya nufi hanyar bedroom d'insa yana dan jan kafan a hankali,binsa da kallo fatuu tayi ta d'an yamutsa baki alamar tausayi,sai da ya shige sannan ta juyo,fitowa yayi hannunshi rike da dan first aid box na karfe ya tsaya ya kunna fitilan sama don ba haske sosai kafin ya nufo cikin parlon,komawa yayi inda ya tashi ya zauna,ita dai fatuu sai binshi da ido take,
d'age kafan yayi saman table ya bude akwatin ya fiddo d'an scissors ya fara yanke bakin wound din da kwalbar taji masa,ganin haka yasa fatuu cije hakora tayi wani d'an sauti"shuuu! Sai lokacin yayi mata kallon kasan ido hakan yasa da sauri ta sunkuyar da kanta,dressing din ciwon yayi ya nad'e saitin ciwon da bandage,
Bayan ya gama ya d'ago ya kalleta itama kallon shi take,alamu yayi mata da kanshi tazo da sauri ta mike ta matsa gab dashi ta duka cotton ya ciro ya dangwali spirit ya mika mata yace"goge nan" ya fad'a yana nuna mata gefen bakinsa,hannu na rawa ta kar6i audugan ta fara goge inda ya nuna mata sai dai sam ta kasa goge jinin dake a wurin wanda har ya fara bushewa,wata cotton din ya ciro ya dan duk'u yayi mata alamu da hannu ta matso da kanta,goge mata jinin yayi kafin yace"kije wancan room din da kika je d'azun ki wanke face dinki ki ciccire abubuwan dake a kanki ki kulleshi"yadda yayi maganar kaman an masa dole,

Da sauri ta mik'e ta nufi d'akin don yin abunda yace tayi,kaman sabon kamu haka kan ya mayar da ita,a hankali ya cira kai yana kallon bayanta har ta shige d'an guntun tsoki yayi kafin ya mik'e ya daukko dustbin ya kwashe cottons din da sauran abubuwan ya zuba ya maida shi wurinshi ya dawo ya rufe box din bayan ya maida komai ciki,jingina bayansa yayi yad'an kwanta jikin kujeran,

Fitowa tayi bayan duk tayi yadda yace gefen c-table ta durkusa saida ya dau wasu seconds sannan ya d'ago ya kalleta fuskan nan babu yabo ba fallasa hakan yasa tasha jinin jikinta,goshinta ya kalla wurin yayi ja amman bai fashe ba,dawo da kallon yayi cikin idanunta ganin yadda ya d'aure fuska yasa tayi saurin sunkuyar da kanta,can ta d'an d'ago taga har lokacin kallonta yake kasa dauke idanunta tayi itama ta rinka kallonshi tana motsa baki kaman zata ce wani abu sai kyakkyafta idanu take,
yatsansa ya mik'a ya nuna mata fridge"je ki daukko" sumi-sumi ta nufi fridge din ta bude ba tare da ta tsaya za6a ba kawai ta daukko guda ta juyo,kafin ta k'araso inda ta tashi ya mike yana nuna mata hanyar fita,ta juya ta nufi kopan shi kuma ya bi bayanta a hankali yake taka kafar,
Chapter 37 · 0% Book details