← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 137

Sashe 30

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cire plate din da aka rufe abincin yayi ya tsaya yana kallon shi wanda spaghetti ce tasha vegetables da busasshen kifi sai kamshi ke tashi,da sauri ya d'ago yana niyyar tsaida Saude dake k'okarin shigewa cikin corridor"hey...." Hajia ta juya da sauri tace"je ki abunki" kafin ta juyo tana dan harararsa"in ma zaka cinye ka cinye don ba abunda za'a rage,wato dazun don kaga can aka bika dashi shine ka tsakura kace azo a dauke ai dama nace zamu hade da daddare ne" haisam dake ta kallonta yana dan cizon lip d'insa na k'asa had'i da dan murmushi yace "did i say anything?" A tsiwace tace"But u'r about to....haka kurum don ka jaman sharri iyayenka su zo su ga ka rame suce hakanan na matsa ka dawo wurina ashe bana baka abinci" Haisam couldn't help it but laugh,sai kace ta daukko wani k'aramin yaro wanda baisan ciwon kansa ba,itama dariyar take taci gaba da kallonta da har yanzu ake shirin da take kallo,shi kuma ya fara cin abincin.

Tunda ta amso abincin ta dawo d'aki ta kasa cin wani na kirki yan lomomi ne tayi taji duk ya fita ranta ba kuma don bata jin yunwar ba,sai don hankalinta daba a kwance ba,tunaninta yadda zata fita yanzu ba tare da gwaggo ta hanata ba don dole fa taje taba mutumin nan hakuri da daren nan,tsam ta mik'e hannunta dauke da plate din abincin ta maida kicin ta rufe a tsakar gida tayi tsaye tana zullumin zuwa tambayar gwaggon daga baya dai ta nufi d'akin gabanta nata faduwa,d'aga labulan d'akin tayi ta shiga da yar sallama gwaggo da har ta kwanta amman bata yi bacci ba ta d'ago da kanta tana k'okarin kunna fitilan wayanta "fatuu,djam? ta tambayeta,Matsawa tayi kusa da gadon tana kallon gwaggon tace"d..dama gidan hajia zanje" cike da mamaki gwaggo tace"gidan hajiya da daren nan,me zaki je yi?",
"Un..dama jiya ne dana je tace in koma yau zata bani sako,to dana dawo islamiyyar safe ban lafiya sai d'azun dana dawo ta yamma naje sai na iske bata nan ta fita ita da t.k amman Aunty Saude tace man in koma in ta dawo don kafin ta fitan saida ta aikota tazo ta kira ni ta iske ban dawo daga islamiyyar ba" ta k'arasa maganar sai faman zare ido take gabanta naci gaba da bugawa da k'arfi,ba don ba haske sosai ad'akin ba da tuni gwaggo ta gane k'arya take shirga mata don har yar zufa tayi,

sanin dama hajiyar na aikowa kiran fatuu wani lokacin yasa gwaggo cewa"to miyasa tun dazun baki je kinga ko ta dawon ba,kika bari dare yayi har haka tara fa ta kusa inma bata yi ba..." da sauri ta katseta "ai ina niyyar dana gama sallah in koma sai kuma kika dawo" gwaggon tace"to ki maza kije ki dawo karfa ki zauna har Amadu ya tashi" cike da farin ciki tace"ah bazan zauna bama" daga haka ta fice ta nufi hanyar fita ko hijab bata yi tunanin taje tasa ba iya d'an bakin gyalenta na gado ne a saman kanta ga kan yayi wani tum saboda gashinta dake a kwance ba kitso yayin da jikinta ke sanye da riga da skirt na material da alama tana son sa riga da skirt,gidan hajiya ta nufa duk da fargabar da take ji hakan bai hanata tunkarar gidan ba don tasha alwashin a daren nan sai taba mutumin nan hakuri.

Sauran kad'an haisam ya k'arasa cinye abincin wayarsa ta hau yin wata kara alamar notification,sanin karar ko ta miye yasa da dan sauri yakai hannu kan hannun kujerar yadau wayan yana dubawa lokaci guda yanayinsa ya canza da wani irin expression mai kaman mamaki kaman bacin rai yake kallon videon fatuu dake sand'a tana tunkarar falonsa,lokaci guda ya furta"Again...! jin haka yasa hajiya juyowa tana kallonsa "ince dai lafiya ko?"ta tambaya,"Yea,nothing" ya bata amsa yana k'okarin mik'ewa don ya yanke a ransa sai yaje yaji mike kawo ta part dinsa,ganin yana kokarin tashi Hajia tace"wai mike faruwa,gashi nan yanayin fuskar ka ya canja kuma ka ki ka sanar dani" d'an murmushi yayi"nace ba komae Sweethrt,just wani sako ne na tura shine aka sanar dani bai shiga ba zanje nai resending" ya fadi mata hakanne don ta kwantar da hankalinta,
tace"to baka sha zo6on ba", "kar ki damu zan sha lemu inna koma can" dan 6ata rai tayi ta fara korafi "shikenan baza'a bar mutum ya huta ba,yini guda mutum nata faman latse,latse haba" yar daria yayi yace"to dama mai nema ina yaga hutu sweethrt" yana gab da fita daga falon tace"zaka dawo muyi hira ko? d'aga mata hannu yayi yana juya shi alamar a'a yace"ki ci gaba da kallon ki saida safe tomorrow is Monday and early to bed early to rise.." daga haka ya fice hajiya na fadin"Allah ya tashe mu lpy toh".

Da sauri ya nufi part dinsa don baison ta fice kafin ya isa,

A hankali fatuu ta kama handle din kopan ta turata kad'an sannan ta turo kanta tana leken cikin falon,a iya hangenta bata hango mutum ciki ba sai computer da ta gani ajiye saman table hakan yasa tayi tunanin ko ya shiga cikin d'aki ne,fiddo kanta tayi waje ta shiga tunanin ko har yayi bacci ne,to yanzu ya zata yi ita?wata zuciyar tace anya kuwa yayi bacci,ai da ya rufe kopa,can kuma tace k'ilan kuma bai rufe kopa tunda akwae jami'an tsaro a bakin gate.....a daidai lokacin haisam ya shigo cikin part din har ya iso bakin balcony din bata ji motsinsa ba,k'ara tura kopan tayi tana sake lek'en cikin falon taga ko ya fito,cike da mamaki haisam ke kallon bayanta yama rasa tunanin da zai yi akanta babban abunda ya d'aure mashi kai shine mike kawo ta part d'insa?miye hadinshi da ita,sannan yama akai tasan inda yake,fuska a matukar d'aure tamkar bai ta6a daria ba ya tattaka stairs din ya haye"Excuse me!"yace mata,
a firgice fatuu ta juyo don sam bata ji motsin shi a bayanta ba balle tasan dashi a wurin,a tsananin tsorace take kallonsa ganin ya daure fuska tamau,wani irin bugu zuciyarta ta shiga yi lokaci guda ta fara ja da baya,atunaninshi rugawa zata yi kaman yadda tayi dazun hakan yasa a kausashe yace"kina guduwa zan sa aje har gidanku a kamo ki,gida mai kiosk right?" hannu fatuu ta shiga yarfawa jin abunda yace,kenan da gaske ne duk abunda Gaye ya fada mata,don dama yace mutumin ya tambayeshi kwatancen gidansu,lokaci guda ta rude ta kid'ime ta shiga fadin"innalillahi....nashiga ukkuna"tana ta faman yarfa hannu kamar wadda wuta ta kona.

*💖ASANADIN MAKWABTAKA💖*

_A heart touching love story_

_*BY ZAINAB LALUH📲*_

*Paid Book*

*2️⃣6️⃣*

kama handle din kopan yayi ya tura kafin ya juyo fuskan nan ba wasa ko kadan yace"biyo ni! a hankali ta fara jan k'afafunta kaman wadda kwai ya fashe mawa a ciki tabi shi ciki kaman yadda ya bata umarni,haisam na shiga ya wuce saman kujera wurin da ya zauna d'azun da Abbas yazo,ita kuwa fatuu tana shigowa wani ni'imtaccen sanyi had'i da daddad'an kamshi suka kai mata karo,zaro idanu tayi baki bud'e ta shiga bin ko'ina na falon da kallo,ba komai yafi dauke mata hankali ba face chandalier(fitilan sama) yadda take d'auke da sarkoki masu kyau,tunda take bata ta6a ganin irin fitilan a zahiri ba sai acikin film din yan kasashen waje,ita bata ma ta6a tunanin akwae irinta a Nigeria ba,gaba d'aya ta saki baki tana ta kallonta har gyalenta ya zamo ya tsaya kan tudun gashinta dake fake,

Ganin bata k'araso cikin falon ba kuma yaji lokacin da ta shigo yasa haisam waigawa ya kalleta,tsayawa yayi yana kallon ikon Allah kaman ba itace ke kerma ba,bai ce mata komai ba ya juya yai powering laptop up ya jingina da kujera ya jira tagama booting kafin ya fara daddanata kuma har lokacin fatuu bata daina kalle kallen da ta ke ba,ganin bata da niyyar shigowa ga dare nayi shi kuma yana son yaji abunda ke kawota part din nasa yasa shi daukan wayarsa ya d'an bubbuga gefenta a saman c-table,aikuwa firgit fatuu tayi ya juya ya dan kalleta ya had'e giran sama da ta kasa,hakan yasa da sauri ta nufo cikin falon can gaban red armchairs ta wuce tana isa gefensu kawai ta zube saman gwiwowinta tayi kneel down,

baice mata komai ba yaci gaba da operating laptop d'in hakan yasa ta samu daman cigaba da kallon fitilar da alama ba k'aramin daukan hankalinta tayi ba,a hankali ya d'ago idanunsa ya dan kalleta sai kuma ya mik'e ya nufi bedroom dinsa tabi bayansa da kallo har ya shige kafin ta maida kallonta kan fitilar dai,

bai dau lokaci ba ya fito hannunsa dauke da wani k'aramin kwali,daidai bakin corridor ya tsaya ya kai hannu ya latsa wani switch lokaci guda hasken fitilar da fatuu ke kallo ya dauke,sai kuma ya k'ara latsa wani lokaci guda hasken wasu fitilun ya gauraye gidajen dasu T.V suke ko wane gida na pop cast din na d'auke da fitila hakan ba k'aramin kawata wurin yayi ba,ai kuma sai ta maida kallon nan wurin har wani dan dukar da kai take,ita mamakinta daga ina hasken ke fitowa don ba'a ganin fitilun sai dai hasken kawai,komawa yayi ya zauna ya fara kokarin bude kwalin da ya fito dashi hakan yasa fatuu ta maido hankalinta kanshi tana so taga minene a ciki,screen glass ne ya fiddo wanda yake sawa in zaiyi aiki da dare don yai protecting idanunsa daga illar hasken screen,binshi da kallo fatuu tayi lokacin da yasa glass din don ba karamin kyau yayi masa ba tamkar fashioned glass haka yake,kasa d'auke idanuwanta tayi sai kallonshi take tun daga saman kanshi har kasan kafafunsa cikin ranta tana ta mamakin yadda akai hajiya ta haifi mai kama da yan kasan waje ita da take bak'a kuma ba wani kyau ne da ita sosae ba,shikam ji kyau kaman shi yayi kansa ta ayyana a ranta,ga dogon hanci ba kaman na hajiyan ba d'an mai fadi dashi,ji yayi a jikinsa tana kallonsa hakan yasa ya yi mata kallon kasan ido suka had'a idanu,da sauri ta sadda kanta kasa don sai taga kaman harararta yayi,tana ta wasa da yatsun hannunta gabanta na cigaba da faduwa.
Chapter 30 · 0% Book details