← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 137

Sashe 93

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida suka gaisa da Amadu yayi mashi ansha ruwa lafiya kafin ya wuce da ita har cikin gidan don yana son yi ma gwaggo barka da shan ruwa, a zaure ya tsaya yace mata ta shiga ta fad'i ma gwaggon zai shigo, cike da zumudi ta shiga cikin gidan lokacin gwaggon na kwance a tsakar gida tayi shimfida ga maganin sauro ta kunna agefe don ba wutan Nepa, a gefenta ta aje tuwon tana sanar mata cewa tare da Ya Handsome take yana zaure yace zai shigo, da sauri gwaggon ta tashi zaune tace mata tace ya shigo don a kimtse take, da gudu taje tace ance ya shigo, a tare suka shigo tana gaba yana baya lokacin gwaggo ta fito daga d'akinta ruk'e da darduma ta shimfida mashi tana ce mashi sannu da zuwa, bayan ta gama ta nuna mashi alamar ya zauna saida ya cire takalmanshi agefe kafin ya hau ya zauna ita kuwa Fatuu can gefe inda sauran kayan bud'a baki suke ta nufa ta fara bubbud'awa tana fad'in " Gwaggo Allah yasa dae baki cinye komai ba kin rage man" har saida Haisam ya d'an kalli inda take sai kace ba yanzu ta gama cin abinci ba, shuru gwaggon tayi mata suka shiga gaisawa da Haisam tace bari akawo mashi abun ta6awa, tana k'okarin mik'ewa ya dakatar da ita yace yanzu ya gama cin abu tace to ai ko ruwa yasha nan ma yace ya gode tace to ta kyaleshi yanzu amman dole yazo shan ruwa kafin agama azumin, d'an Murmushi kawae yay kafin ya d'an d'aga kai ya kalli Fatuu dake can gefe sai ta tsakura wannan ta ci wannan acikin ranshi kuwa mamakin yadda take cin abinci yake yanzu ya gano dalilin dayasa ta tashi hankalinta daya sata yin azumi dole, godiya gwaggo ta fara yi mashi game da azumin dayasa Fatuu take yi tace ita sam bata san rashin hankalin da take yi kenan ba da tuni ta tsawatar mata don duk atunaninta in tayi azumi cikakkene, nan ma dae d'an Murmushi yayi ita kuwa fatun tana jin abunda gwaggon ke cewa ta taso tazo inda suke, agefenta ta zauna tace,
"Gwaggo ni ce banda hankali?",
" ina kika ganshi fa" ta bata amsa cikin harshen fulatanci, turo baki tayi da hausa tace "Wllh Allah inada cikakken hankali kuma ga Ya Handsome nan ki tambayeshi kiji don shi yasan inada hankali" jinjina kai gwaggo ta shiga kafin tace " dama ai yanzu yana daga cikin wad'anda zasu fad'i rashin hankalinki Fatuu" jin hakan yasa ta fara kukan shagwa6a tana d'an tuttura kafa, girgiza kai gwaggo tayi tace "yanzu shi wannan abun da kike ai duk cikin hankalinne ko, ke sam ba ranar da zaki girma ne?" turo baki tayi ba tare data ce komai ba idonta akan Haisam daya d'an sadda kai yana kallon k'asan gidan, d'agowa yay ya d'an kalleta suka hada ido ya d'an girgiza kai kafin ya kalli gwaggo yay mata sallama yana kokarin mik'ewa, atare suka rako shi gwaggon na k'ara yi mashi godiyar dawainiyar da yake masu, suna zuwa bakin zaure ta koma ciki ita kuma Fatuu ta rako shi har waje dama bata cire hijab d'in jikinta ba, suna fitowa kan hanya yace ta koma tayi tsaye bakin hanyar tace sai ya tafi zata koma, har ya d'an wuce shagon Amadu ta kwala mashi kira,

"Ya Handsome",tsayawa yay ya juyo ya kalleta,
" ai gobe dae ba Azumi ko?" shiru ya danyi da farko sai kuma ya d'aga mata kai alamar eh, kawae sai gani yay ta fara yin rawa, bud'a ido yay alamar mamaki aikuwa tana ganin hakan dayake akwae haske ta ruga tana ta dariya, girgiza kai kawae yay daga haka ya nufi gida.

Washe gari da bata yin azumi sam bata yarda taji yunwa ba,duk wani abun ci data gani sai taci, tunda safe kafin ta tafi makaranta ta cinye duk abunda suka rage haka bayan antaso data je gidan Hajiya bunu bunu taci wani abu wai daga yau sai bayan kwana biyu Saude nata mata dariya, da yamma data koma gida ma tana taya Gwaggo aiki tana cin abubuwan da aka fara na bud'a baki ba tare da ta 6oye ba kamar yadda take yi da don yanzu gwaggon tasan yau ba ranar yin azumi bace har gwaggon nace mata wannan kafin asha ruwan ma ai saita cinye komae sai da tayi da gaske ta hanata. Haka taci gaba da yin azumin duk in tayi biyu sai ta huta kwana d'aya kuma bata k'ara yima Haisam korafi game da azumin ba gudun kada yay fushi da ita sai dae in yana bata wuya tai ma su gwaggo ko Saude korafin, ana saura kwana takwas agama azumi bayan gama sallar asham yace mata ta shirya gobe karfe 10 na safe zai kaita inda za'a gyara mata kai, lokacin zai rakata gida kaman yadda kusan kullum yake rakata don yanzu da angama sallar saita koma part d'in hajiya daga baya ya rakota sa6anin da tare da Haulat suke tafiya gida da angama sallar yanzu kuwa tun a Masallacin suke rabuwa suyi ma juna saida safe, cike da murna ta amsa mashi da to sai kuma ta tuna goben ranar yin azumi ce hakan yasa ta rokeshi akan ya barta ba sai tayi gobe ba tunda fita zasuyi, da farko k'in yarda yay ganin yadda ta marairace mashi ne kuma ba wuri daya yake son suje ba yasashi ce mata in ta yarda zata rama shi next tayi ukku sai ya amince, cike da zumud'i tace to ta yarda ahaka suka rabu,

**** **** *****

Washegari tunda sassafe ta tashi don fitar da zasuyi na ranta shiyasa da tayi sallar Asuba ta kasa komawa, kuma dama tunda ya gaya mata tana isa gida ta sanar ma gwaggo tace karta tada ita sahur don bazata yi azumi ba, tana tashi shaf shaf ta share tsakar gidan tayi wanke wanke don indae bata azumi ita ke yinsu in tana yi kuma gwaggon ke kama mata wani abun kaman wanke wanke sai suyi tare in tana gida wani lokacin ma ita kad'ai ke yi ita Fatun sai ta share duka gidan don tuni anyi masu hutun Islamiyya, tana gamawa ta fad'a bandaki tayo wanka bayan ta gama ta nufi d'aki don ta shirya, Misalin k'arfe 9:30 saura ta gama shiryawa cikin jar jallabiyarta harda su makeup ga jan janbaki tasa abakinta tayi kyau sosae ba kamar yanzu da skin d'inta ta canza saboda mayukan da take amfani dasu sun fito da ainihin kalarta don bana bleaching bane, koda ta lek'a yi ma gwaggo sallama isketa tayi tana bacci hakan yasa ta fito ta tafi don tasan ta sanar da ita tun jiya, lokacin da ta fito wajen wayam ba kowa duk anata baccin safe ko kawu Amadu ma bai tashi ba dama yanzu bai bud'e shago da wuri wani lokacin ma yan kawo kud'in kankara ne ke tada shi dole, ta Gate tabi don k'aramar kopar arufe take har Officer na zolayarta cewa da ganin wannan kwalliyar bata azumi tace mashi tana yi daga haka tai wucewarta don a k'agare take da su tafi, da sallama ta shiga cikin falon nashi don abud'e ta iske kopar sai dai koda ta shiga bai acikin falon hakan yasa ta zauna don ta jirashi tunda tasan lokacin daya dibar masu zasu fitan bai idasa ba kuma koda wasa bata ta6a shiga Bedroom dinshi ba don bata ma ga fuskar yin hakan ba a wurinshi, shiru shiru har bayan wani lokaci bai fito ba hakan yasa ta gaji da zaman ta d'an kwanta a d'ayan 6arin kujerar, nan da nan sanyin Ac ya bugeta ta fara d'an gyangyadi dama jiya bata samu isasshen bacci ba saboda zumudin yau tayi, jin sanyin Ac d'in yayi mata yawa don har kafafunta sun fara rawa yasa ta mik'e ta daukko throw pillows d'in dake akan kujeran ta rufe kafafunta dasu ta linke hannuwanta akirji nan da nan ba tare da ta ankare ba bacci mai karfi yai awon gaba da ita,

Karfe goma daidai ya fito cikin falon jikinshi sanye da rantsatstsen Voile Coffee Brown haka takalmanshi da agogon hannunshi ma duk Coffee ne, Ma sha Allah shine abunda na fad'a yayin da yake nufo cikin falon da tafiyarshi ta kasaita, tsaye yay d'an nesa da ita yana kallon fuskarta fuskarshi d'auke da d'an Murmushi don ganinta da yay yasashi k'ara fahimtar yadda take son agyara mata gashin, kai idonshi yay kan kafafunta da ta jera throw pillows lokaci guda ya fadada Murmushinshi had'i da d'an girgiza kai, juyawa yay ya koma Bedroom dinshi, bada jimawa ba ya fito hannunshi d'auke da lallausan farin Duvet, saida ya cire pillows d'in sannan ya lullu6a mata shi har zuwa cikinta daga haka ya juya ya nufi dakin lab d'inshi ya fito hannunshi ruke da wata bak'ar laptop ya zauna a inda ya saba zama ya fara operating dinta bayan ya daurata kan c-table,

Bacci sosae Fatuu take yi, duk in tayi motsi sai ya d'aga idonshi ya kalleta sai kuma taci gaba, saida ta d'auki kusan awa kafin ta fara motsi sosae, a hankali ta fara bud'e idanunta kafin ta idasa ware su sosae, kuri tayi tana kallon Haisam dake ta daddana computer da mamaki tace "Ya Handsome" gira ya d'age mata kafin ya d'aga ido ya kalleta, mik'ewa tayi zaune idonta akan duvet d'in dake jikinta tace "Ya Handsome kai kasa man wannan abun?" kai ya daga mata alamar eh sai kuma yace " kina jin sanyi ne",
" to munje wurin gyaran gashin ne?",
shiru yay jin wata tambaya mara kan gado, can kuma tace "Wai ashe bacci nayi, to mun fasa zuwa ne" jinjina mata kai yayi ba tare daya kalleta ba yace "Yea, time d'in ya wuce yanzu ina abu ne",
kaman zatayi kuka tace "to ai ba laifina bane tunda da sassafe nazo kaine baka fito ba ka ganni ba har bacci ya kwashe ni",
" Yanzu laifi nane kenan tunda ni nace kiyi bacci ko?" ya d'ago ya kalleta tai narai narai da idanu har kwalla ta fara taruwa,
Chapter 93 · 0% Book details