← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 137

Sashe 110

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

.......tana komawa gida ta iske gwaggo ta dawo dama makwabta ta shiga, cike da zumudi ta sanar mata game da zuwan haisam cin indomie gwaggon tace to tayi sallar magrib sai taje ta amso wurin Amadu ta amsa da to,bayan ta gama sallar ta tambayi gwaggo guda nawa zata amso tace to kuma ba'a san nawa zata ishe shi ba ko abari yazo sai ta tambayeshi Fatun tace to, mikewa tay ta nufi kitchen ta fiddo d'an gas d'insu da zatayi amfani dashi ta aje acan gefen kicin d'in, komawa tayi ta fiddo tukunya da sauran abubuwan da zatayi amfani dasu duka ta aje, attarugu da albasa ta de6o bayan ta wanko su ta daukko d'an turminsu zata jajjaga gwaggo tace karfa ta cika tunda ba'a san ko yana son su ba tace ai kad'anne dama haka take masu in zata dafa ma Amadu saboda bai son ganinsu zak'o zak'o ba kaman Albasar, bayan ta gama ta kwashe su acikin wani d'an bowl ta rufe ta aje awurin sauran kayan ta koma kusa da gwaggo ta zauna ana fara kiran sallar isha ta mik'e tayi, tun bayan data gama ta zuba ma kopar shigowa ido tana dakon zuwan Haisam shiru shiru har bayan wani d'an lokaci bai zo ba hakan yasa ta fara mita can dai tace bari taje taga miyasa bai zo ba har yanzu, tana shirin mik'ewa gwaggo ta dakatar da ita tace ta kyaleshi tunda yace zaizo ai zaizo ne k'ilan wani uzurin ya tsaidashi, tana rufe bakinta Amadu ya lek'o ta cikin zaure yace ga Yaya Haisam nan zai shigo zumbur Fatuu ta mik'e ta nufi hanyar zauren tana fad'in ya shigo kawae mana, atare da shi suka shigo tana gaba yana biye da ita a nutse yake tafiyar jikinshi sanye da riga turtle neck da jeans sai faman juyawa take tana kallonshi bakinta a washe suka karasa ciki, fitowa gwaggo tay hannunta ruke da k'atuwar darduma tana mashi maraba ta nufi can gefen d'akin Fatuu ta shimfida mashi, bayan ta gama tace ya zauna saida ya cire takalmanshi a gefe kafin ya hau kan dardumar, gaisawa suka shiga yi gwaggo na mashi an dawo lafiya da tambayar ya ya baro sauran yan gidan da Hajiya, a nutse ya rinka bata amsa Fuskarshi a sake,

"Ya Handsome indomie nawa zan dafa maka?" Fatuu da tay tsaye k'erere a gefenshi ta tambaya,shiru bai bata amsa ba hakan yasa ta k'ara cewa "kaji Ya Handsome guda nawa zata ishe ka?" kallonta yay da d'an Murmushi ya d'aga mata dogon yatsansa alamar guda d'aya tana ganin haka ta zaro ido tace "d'aya kuma, amman dae babba ko?" girgiza mata kai yay a hankali ya furta "small pack" bud'a baki tay sai kuma ta tura shi cike da shagwa6a tace "kam ya za'ai k'araman indomie ta ishe ka" gwaggo dake d'an Murmushi ta amshe da fadin "adai dafa babba ko d'ana Haisam k'arama d'aya ai bazata kosar da Mutum ba...." da sauri Fatuu ta katseta "kuma ma tun Abuja fa bai k'ara cin wani abu ba nidai Allah manya guda biyu zan dafa maka ka ci ka koshi" tana kai Maganar ta nufi hanyar fita, har ta shige zaure sai kuma ta lek'o da d'an d'aga murya ta tambayeshi harda kwai ya daga mata kai alamar eh sai kuma tace "to guda nawa kwan?" kafin ya bata amsa cikin harshen fulatanci gwaggo tace ta amso ukku Fatun tace to tare da juyawa ta nufi waje shagon Amadu, bata d'auki wani dogon lokaci ba ta dawo ruk'e da bak'ar leda ta aje gefen sauran kayan kafin tasa hannu ta cire hijab d'in jikinta ta kaita can gefen tabarmar da gwaggo ke zaune ta aje tana niyyar komawa wurin da zata yi girkin gwaggo tace ahaka kai ba kallabi zata yi dahuwar, da sauri tace au ta manta ta nufi d'akinta ta dauro kallabi, bayan ta fito ta d'auki tukunyar taje ta debo ruwa ta kunna gas d'in sannan ta daura, cike da nuna kwarewa take dahuwar nan da nan k'amshi ya gauraye wurin lokacin data kusa gamawa,
"Ya Handsome ka fara jin kamshi ko?" ta juya tana tambayarshi da yake tsakan gidan fayau yake da hasken globe mai caji, kai ya d'aga mata yana Murmushi gwaggo ma dake zaune tana mashi fira jefi jefi itama Murmushin tayi, tunawa tayi bata dafa kwan ba hakan yasa ta tambayeshi ta soya mashi ko yafi son dafaffen yace ta soya, bayan ta dahu ta shiga kicin ta daukko plate mai kyau tana fitowa gwaggo tace ta sake wanko shi kafin ta zuba, ba 6ata lokaci ta wanko shi tazo ta juye indomie d'in ta nufi inda haisam yake tace ya fara ci kafin ta soya mashi kwan kada ta huce ya jinjina mata kai, mik'ewa gwaggo tay don yafi sakewa yaci ta nufi d'akinta, kicin Fatuu ta shiga ta d'aukko fraying pan da duk abunda zatayi amfani dashi saida ta daurayo su kaman yadda gwaggo tace tayi d'azun sannan tazo ta fara had'a kwan bayan ta zuba ta juya ta kalli haisam ganin baici yasa tace yaci kada ta huce mana, aje wayar yay gefe guda ba tare daya ce mata komae ba ya d'auki fork d'in cikin indomin ya d'ebo yar kadan ya kai baki ya fara ci a nutse,
"Ya Handsome ya kaji, da dad'i ko?" maimakon ya bata amsa sai ya mik'a yatsanshi yana mata nuni da kwan da take soyawa da sauri ta duk'a ta juya bayan kafin ta d'ago tana k'ara tambayarshi da dad'i indomie d'in jinjina mata kai yay ta washe baki ta shiga kod'a kanta tana cewa ai ta iya dafawa don kawu Amadu ma inta dafa mashi har santi yake shidai haisam jinjina mata kai kawae yake yana d'an cin indomie din can suka fara jin k'auri alamar kwan na k'onewa, a rud'e ta juya gun kwan koda ta juyashi har bayan ya yi bak'i amman ba sosae ba, kashe gas d'in tayi da sauri kafin ta juyo a sanyaye tana kallon haisam da shima kallonta yake fuskarshi a sake kaman zai dariya,
Chapter 110 · 0% Book details