Sashe 71
Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Juyowa yayi bayan ya gama rubutun yace"kuyi copying wannan,tomorrow i will explain it",amsa wa sukai da"Ok sir" nuna dayan 6arin board d'in yayi ya tambayesu sun gama kwafar rubutun suka ce eh,hakan yasa ya goge wurin ya rubuta Assignment,a Wayarshi ya ringa kallo Question d'in yana rubutawa a Allo,bayan ya gama rubutawa suka tambayeshi suyi copying Assignment d'in yace masu a'a ba nasu bane,kallon Fatuu yayi yace nata ne Assignment d'in ta tabbatar gobe tayo shi ta kawo mashi kuma a Allo zata yi ma yan ajin bayanin yadda ta fidda shi in kuma ta kasa to duka filin dake gaban classes d'insu ita zata share shi ta kuma wanke duka toilets dinsu har tsawon sati guda sannan ya k'ara mata da bugu,k'ank'ance idanu tayi tana kallon Assignment d'in da ya batan kafin ta kalleshi tana tura baki tace"ai baka yi mana irinshi ba",
"Eh nasani,kece zaki yo shi kiyi ma sauran yan ajin bayani,ga amsar da nike so ki samo nan na rubuta a k'asa in dae amsar da kika samu bata yi daidai da ita ba to baki yi shi daidai ba" cike da isa yana wani shan k'amshi yake mata Maganar daga haka ya kwashe kayanshi da yayi amfani dasu ya kalli sauran yan ajin yace"Till we meet tomorrow" ya fuce abunshi,
Mik'ewa tsaye Fatuu tayi tana k'are ma Assignment d'in kallo,sam bata san ta ina zata fara yinshi ba bare har ta gano amsar daya rubuta a k'arshen,lokaci guda ranta ya k'ara 6aci ta harzuka juyawa tayi tana kallon yan ajin da suma ita suketa kallo tun bayan da malamin ya fita nan take ta fara zuba masu ruwan bala'e tana yi tana buga desk ta kuma ci alwashin indae har bata yo Assignment d'in daidai ba yasata yin abunda yace wllh kowa sai taci ubanta,tun tana masifar a k'asa har abun yakai ga hawa saman desk yadda zata ji dadin ganin kowa kuma kowa ya jita,gaba daya kowa yayi tsit ba wanda ya tanka mata don sun san halinta sarae bata iya fad'an cacar baki ba sai nakai bugu kamar yar dambe da mutum ya tanka mata yanzu ta hau shi da bugu koda kuwa ya girme mata haka zatayi suka kan mutum ta mak'alkale shi kaman biri,Haulat dai girgiza kai kawae take don tasan in tayi irin wannan zuciyar bata jin lallashi,saida tayi mai isarta don kanta ta hakura ta saukko daga saman ta zauna saman seat taci gaba da kwafar rubutun tana yi tana kwafa had'i da tsoki,
sai bayan da aka tashi ne lokacin da Bus ta saukesu Haulat ta fara bata hakuri ta nuna mata duk laifinta ne da batayi Magana ba tunda ba ita kadae ta gaji ba kuma ba wanda yasata tace mashi hakan dama dole zai ga tayi mashi rashin kunya ne data k'yaleshi yai tayi har ya gama ya fita,shiru tayi bata ce mata komai ba,
"Yanzu to shi Assignment d'in daya bakin kin iya ne?" Haulat ta tambayeta,nan ma shiru tayi mata kaman bazata ce komae ba can kuma tace"ko ban iya ba sai na dage nayi shi ko don in bashi kunya,mugu kawae ai da biyu ya bani shi bacin yasan bai mana shi ba,baki ga ma a wayarsa ya kwafe shi ba" kai Haulat ta d'aga"Eh nagani,Allah ya taimake ki kiyi shi daidai",a hankali ta amsa da Amin,adaidai nan suka rabu da Haulat d'in, Fatuu tayi gaba ita kuma ta shige kwanar gidansu.
Tun bayan data koma gida ta baje a tsakar d'akinta tanata faman kokarin yin Assignment d'in,saidae sam ta kasa,har wani textbook d'inta na maths ta duba wai taga ko zata ga irin tambayar amman ina ko mai kama da ita bata gani ba gashi matsalar ma bata san sunan topic d'in Assignment d'in ba balle ta duba table of contents na text book d'in ta gano page din da akayi irin topic d'in ko zata samu koda shigen tambayar ne,duk ta had'a uban gumi,k'arshe data gaji ta buga littafin da kasa tana ta faman huci ga uwar yunwa dake faman cinta don dole ta mik'e ta nufi Kitchen ta zubo abinci,bata wani ci na kirki ba taji duk ya fita aranta don hankalinta ba'a kwance yake ba bata da burin daya wuce taga tayi Assignment d'innan ba kuma don tana tsoron hukuncin da za'a mata bane sam ta saba da Wannan kawae so take ta k'ure Malamin da sauran yan ajin,can ta tuna da bata yi sallah ba zuciyarta ta raya mata k'ilan ma shiyasa ta kasa yin Assignment d'in,zumbur ta mik'e taje tayo Alwala tazo tayi Sallah data gama harda yin Addu'ar Allah yasa tayi shi daidai,bayan ta gama ta k'ara d'aukko littafin Maths d'in don ta k'ara gwadawa ko tayi daidai amman ina ko steps d'in dama zata bi har tasamo irin amsar daya batan bata sani ba,duk da hakan bata sare ba taci gaba da jagwalgwalawa a paper in tagama taga baiyi ba sai ta yaga paper din ta ciro wata ahaka sai da ta yaga fefofi masu yawa da abun ya isheta sai kawae ta zabga uban tagumi fuskarta a yamutse ta rasa yadda zatayi tai solving dinshi,tana cikin wannan yanayin Kawu Amadu ya fad'o mata arai aikau zumbur tayi ta mik'e ta nufi waje duk da batasan ko ya dawo bama don bata ji motsin shigowarshi ba kuma bata ji ya shigo d'aukar Abinci ba a kicin,tana zuwa zauren taga kopar d'akinshi a rufe alamar bai dawon ba,komowa tayi cikin gida amma ta d'an ji sanyi cikin ranta don zuciyarta na tabbatar mata da k'yar inba shi zai iya fidda mata shi ba tunda shi d'an Senior ne kilanma su anyi masu irinshi dama kuma yana yi mata Assignment in bata iya ba,cike da kwarin gwuiwa ta koma daki don ta jira dawowarshi,can ta mik'e tace bari taje tayi wanka kilan kafin ta gama ya dawo.
Bayan tayo wanka ta shirya cikin riga da skirt na atamfa ko mai bata shafa ba burinta kawae taji Kawu Amadu ya dawo,zaune tayi ak'asa ta tasa littafin Assignment d'in agaba tayi zugudum ahaka ta fara gyangyad'i amman taki bari baccin ya d'auketa duk da tana jinshi sosae,tana hakan ta jiyo k'arar bud'e d'akinshi aikuwa a sukwane ta rarumi littafin Assignment d'in da biro tayi waje,tana zuwa d'akin nashi ta banka ko sallama babu,lokacin yana cikin cire Uniform d'inshi don har ya cire rigar daga shi sai singileti amman bai kaiga cire wandon ba,kallonta yayi fuska amurtuke,
"Kina da hankali zaki shigo man d'aki haka ko sallama babu!" shiru tayi tana kallonshi fuska a yamutse, ganin hakan yasashi cewa"lafiya?",
cikin yar en ena tace"Daman tun d'azu nike jiranka Assignment ne don Allah zaka yi man ni nayi nayi amman na kasa",yar harararta yayi"shine don baki da hankali daga dawowana zaki banko man d'aki ko,to banyi ki futa ki ban wuri",ta6e baki ta fara yi kaman zatayi kuka ta hau yi mashi Magiya,fuska a d'aure yace ta fita to ya gama cire kaya,da sauri tace to,ta juya ta fita,abakin kofar d'akin nashi ta tsaya bayan wani d'an lokaci ta kware baki tace"in shigo ka gama?"banza yayi mata ta k'ara maimaitawa,jin shiru yasa ta d'an lek'a kanta cikin d'akin lokacin yana tsaye daga shi sai d'an boxer shorts amman sai cewa tayi"Kawu ka gama ne in shigo"a fusace ya kai hannu ya rarumo jakar Makarantarshi zai jefo mata tana ganin hakan ta janye kan da sauri,
ci gaba tayi da tambayar kawu ka gama in shigo,daga wajen ta maida abunma kamar wak'a,d'an guntun tsoki yaja lokacin daya gama shiryawa yace"in kin gadama ki kawo man Abinci",da sauri ta amsa da toh,
Kawo mashi Abincin tayi harda ruwa masu sanyi,tana ajewa a gabanshi ya d'an rankwashi kanta"shegiya dayake buk'ata kike awurina harda su ruwa baccin kullum sai nayi fama dake kafin ki kawo man" ya k'arasa Maganar yayin da yake zaunawa a gefen yar katifarsa, itama zaunawa tayi ak'asa hannunta guda tana d'an sosa inda ya rankwashetan,fara cin abincin yayi ita kuma tayi mashi k'uri da ido,yana cikin ci ya kware ya hau yin tari ta hau yi mashi sannu,a fusace ya kalleta bayan tarin ya lafa"Sannun ubanwa,kin k'ura man wad'annan idanuwan naki uwa na mujiya ba dole in kware ba ko ki daina kallona ko ince banyi wllh"turo baki tayi ta juyar da kanta gefe har ya gama cin abincin,
"Kawo muga Assignment d'in in zan iya ko kya tashi kiban wuri kin wani tsareni sai kace wanda yaci maki bashi"da sauri ta mik'a mashi Littafin bayan ta bud'o daidai inda Assignment d'in yake,kar6ar littafin yayi ya k'ura idanu yana kallon tambayar da za'a fiddan,
"Wannan wane topic ne,Quadratic Equation ne ko mi?"yayi tambayar had'i da kallonta,watsa hannuwa tayi tace "wllh nima ban sani ba ya dae ce wai ga amsar da za'a samo nan ak'asa in ba'a samo irinta ba to ba'ayi daidai ba,amman na duba ma Quadratic equation d'in da akayi mana naga kwata kwata basu kama da wannan har a textbook d'ina na Maths na duba banga wanda yayi ko shige dashi bama" k'ara kallon Question d'in yayi kafin ya d'ago yace"to shi wannan din a wane topic yayi maku shi?",
"Bansani ba,kawae tambayar ya bada" jinjina kai yayi"aikau dae wllh dakyar in zan iya yinshi nima don gaskiya ba'ayi mana irinshi ba,amman bari dai in duba textbook d'ina nima muga ko za'a samu irinshin"da sauri tace to,don da har gabanta ya fad'i,