Sashe 18
Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haisam ne ya d'ago da kansa ya kalli kawu Mani yace "ina yini Uncle" sannan ya juya ya gaida sauran cikin muryarsa mai cike da natsuwa,a tare harda kawun suka amsa mashi da "Lafiya lau",
"Haisam ne d'an gidan Hajiya" kawun ya tambaya da fara'a "Eah" haisam yace a tak'aice, kawu yaci gaba da magana "Masha Allah,Haisam ya karatun? Kafin ya bashi amsa Hajiya tace"Ai ya gama,yanzu haka yaci gaba da aiki a nan garin yana nan AIRPORT" da mamaki yace "Wai yanzu har ya gama karatun? Kinsan kafin ya tafi nazo nan muka had'u lokacin kike ceman zai tafi yin Master's Degree a U.S"
tace"Aikuwa dai gashi har angama" jinjina kai kawu yayi yace"Time really flies,Allah yasa mudace" hajia tace "Aikam lokaci fa na gudu,Amin ya Allah",sauran ma suka amsa da"Amin",
Kallon Haisam yayi yace "Haisam yanzu sai Aure ko,nasan yanzu ai ka kai 30yrs ko?"yayi maganar yana yar daria,d'an guntun murmushi haisam yayi kafin yace wani abu wayarsa ta fara ringing ya mik'e yace masu"Excuse me.." daga haka ya fice,
Hajiya dake ta fara'a tace "bai ida shekara talatin ba yanzu ya shiga 29yrs yanayin jikin ne sai ka ce yama wuce 30,dama kuma ga daga karfe yana yi,Auren kuma tukunna dai sai nan gaba in zai koma" Kawu yace "karatun zai k'ara komawa ne? tace"Eh zai koma U.S d'in amman ba karatu zashi yi ba duk dama yace zai kara karatun in ya koman,akwai wani babban Company ne daya danganci karatun da yayi na Computer Engineering suna k'era kwamfutoci da sauran abubuwan su na fasaha dai,shine suke son yin aiki dashi,duk da yanzu haka matsayin Agent d'insu yake anan k'asar,to kasan Uban nashi akwai kishin k'asa,da k'in yarda yayi,sai da Haisam d'in yayi mashi bayanin dalilin daya sa yake son yaje can yayi aiki dasu sannan fa ya aminci amman yace sai ya k'ara yima k'asar shi koda na shekara biyu ne,don gani yake suna iya rik'e shi...." a d'an harzuk'e Kawu Mani yace"Very thougthful of him,wallahi Senator yayi man daidai,don ma bansan dalilin daya sa Haisam d'in ke son zuwa ba,da nace dama gaba d'aya ya hana shi,haba! for how long zamuyi tayin shuka su suna girbe amfaninta,sam wallahi mutanen nan basu son cigaban mu,shiyasa da sunga mutumin mu mai hazak'a sai su bukaci yayi aiki dasu,su kuma mutanen mu sam basu kishin k'asar su,what they're after is the money,su dai kud'i kawai,basu tunanin suma su gina tasu k'asar,koda bazamu iya kamo su ba,mu ha6aka tamu kasar ta yadda zamu daina relying kansu,d'an abunda bai kai ya kawo ba ace sai anfita waje" ya d'an tsaya ya sauke numfashi,sannan ya juya kan mutanen da ya zo dasu ya ci gaba"Wallahi Alhaji Sa'idu karka so kaga yadda mutanen nan ke cin moriyar mutanenmu sai ma kaje asibitocin su zaka sha mamaki yawanci sai kaga manyan likitocin da suke masu aiki duk mutanenmu ne....." Hajiya ta katse shi da fad'in "tabbas,don akwai lokacin da muka kai marigayi Minister da yayi wani ciwo kasar Germany,wallahi likitan dake duba shi mutuminmu ne,kuma ma d'an nan Katsina don bayan mun dawo har zuwa yayi duba lafiyar tasa..."Kawu Mani yace "You see...shine maganan da nike,suna can wasu na amfanuwa dasu sun bar mu nan munata fama da rashin k'wararrun likitoci".
Ya juya kan hajia"Wallahi hajjaju mostly likitocinmu yanzu ain't qualified,yan kad'an ne suka san aikin su,wai sai kaje asibiti ko ka kai wani naka,abun haushi kana ma likita bayanin matsalarka sai kiga ya fiddo waya yana googling...wai sai ya tura ma google duk abunda aka bashi shi zai jibga maka kuji fa don Allah wanda ada sam ba haka likitocinmu suke ba k'wazo ne dasu" gaba d'aya suka jinjina kai cike da takaici,
Wanda kawu ya kira da Alhaji sa'idu ya fara magana "A haka kuma wasun nasu sai d'an karan wulakanci,haka zakai ta jin Labaru maras dad'i da suka faru a dalilin wulakanci da kuma sakacin da bai kamata ace ma'aikacin lafiya ne yayi hakan ba,wanda na tabbatar in a k'asar wajen suke yin aikin kwatankwacin hakan basu isa suyi ba,ba tare da an d'au kwakkwaran hukunci akai ba" gaba d'aya suka jinjina kai hadi da fad'in "Sosai kuwa",
Na karshen ne wanda bai kai su girman jiki ba,shima ya fara magana"Wato Alhaji Mani duk matsalolin nan sun fara ne tun daga tushen fara karatun,yadda yakamata ace ana koyawan ba haka ake koyawar ba ayanzu karatun duk ya ta6ar6are shiyasa masu halin sai su d'auke yaransu su tura su kasar waje karatu,su kuma da sun ga mutum nada basira sai su rik'e shi suna biyan shi kud'i masu yawa,wanda yasan baza'a iya biyansa kwatankwacin su ba a k'asar shi dama kuma ba itace a gaban shi ba,taci gaba ko karta ci gaba shi ba ruwanshi,su kuma maras halin da basu da wani zabi da ya wuce dole su tsaya nan suyi karatun a wahale gashi yawancin malaman sun maida karatun kasuwanci,da abunda d'alibi yakamata ya kashe kudi da wanda bai kamatan ba duka kashe kudin yake,gaba d'aya yanzu karatun d'an talaka ya zama wahala yan kadan ne ke iya jurewa su gama,shiyasa in suka fara aikin sai kaga kaman suna ramuwar gayya ne,ba malaman asibitin ba,ba malaman makarantar ba da dai sauransu,kowa bai tunanin duk abunda yayi ma wani zai iya juyewa kan nasa....,
"To Al'amarin kasar tamu dai sai Addu'a kawai amman muna bukatar mu canza halayenmu inba haka ba,haka zamuyi ta zama jiya iyau abubuwa duk suna ta ta6ar6arewa,kowa damuwarsa taya zai samu kudi ba ruwanshi da kasar ta gyaru ko akasin hakan kuma dai ko mun k'i ko mun so k'asarmu ce ba yadda zamu yi,in ta gyaru mu zamu ji dadi akasin hakan ma mune a ciki" lokaci guda su duka sukayi ajiyar zuciya,
Hajiya tace"Allah ya bamu ikon gyarawa gaba d'ayanmu harda shuwagabannin mu,yasa mana tausayin junanmu,Amin" suma suka amsa da "Amin", taci gaba da magana "Shi Haisam ma ba kudi ne zasu kaishi ba,sam ba sune damuwarsa ba wllh,dama yana da burin gina katafaren Company wanda ya danganci technology d'in anan k'asar,to shiyasa yake son yaje yayi aiki dasu don ya k'ara samun Experiences,don bama shine Company na farko da suka yi mashi tayin aiki ba,ko lokacin da yayi Degree d'insa na farko a can k'asar Singapore,akwai wani Company daga k'asar China da suka so yayi aiki dasu Uban nasa ya hana yace ya dawo nan gida yayi aiki,to lokacin ya fara a matsayin Engineer mai zaman kansa daga baya ya fara aiki ak'arkashin Ministry of Communication Technology,
Kawu Mani yace "haba ni daman nasan badai kud'i ne zasu sa Haisam din son yin aikin ba,ashema babban dalili ne,aikuwa gara yaje kinga sai ayi abunda ake cema ban gishiri inbaka manda" ya d'an dakata kafin yaci gaba"Ai sanata akwai kishin k'asa,wallahi nike gaya maki hajiya da Allah zaisa ya zama shugaban k'asa da munji dadi" dariya hajiyar tayi, ya juya wurinsu Alhaji Sa'idu yace "Allah daba k'aramin adalin shugaban k'asa za'ai ba mai kishin cigaban kasarsa,ga dai misali nan kan Iyalinshi" suka jinjina kai had'i da fadin "gaskiya ne" ita kam hajiya dariya kawai take tace "tau da kamar wuya dai ya fito takarar shugaban k'asa,don takarar Senator d'in ma da yaya ya fito sai da mutane suka taso shi gaba da kyar ya aminci,haka da tenure d'insu ta kare ma so yayi yaki ci gaba,a cewarshi yafi son ya cigaba da aikin shi da kuma kasuwancinsa".
Kawu yace "Ai shugaban k'asan ma sai a matsa masa ya fito in Allah yasa da rabo sai kiga ya zama,ni ba don komai bama wallahi sai don fatan samun sauk'in matsalolin nan da suka yima k'asarmu katutu..." ajiyar zuciya Hajia tayi tace "Allah dai ya za6a mana dukkan abunda yafi zama alkhairi" gaba d'aya suka amsa da "Amin ya Allah".
"Oh munata tattauna matsalolin da in shekara zamu yi ba lalle mu gama ba,an barku ko ruwa ba'a kawo maku ba" hajiya tace tana kallon su Alhaji Sa'idu da murmushi,suma murmushin suka yi,ta kalli Kawu mani tace "ga Abinci can saman table,dama bamu dad'e da saukkowa ba nida Haisam,don da ana gama sallan juma'a ku ka zo ma a tare zamu ci"
Kawu yace"Wallahi nan naso muyi sallar juma'an,to bamu gama abunda muka je yi ba da wuri,dole acan dai mukayi" hajiya tace"Wani wuri kuka je ne? Yace "Eh,Ministry of Agriculture muka je" tace "Allah sarki,ya noman ana tayi ko? Yace "Eh,Alhamdulillah muna ta k'okartawa"
"To Allah ya k'ara taimakawa,wasu yankunan ma naga noman ya gagaresu saboda matsalar rashin tsaron nan,gona ta ma da ke hannun baban tukur bara ai noman bai samu ba,Allah ya kawo masu d'auki da mu gaba daya" suka amsa da "Amin"
"Jama'a ku tashi kuci abinci don Allah" ta fad'a tana kallon su Alhaji sa'idu,Kawu Mani ne yace "ai inaga Hajiya kaman a sakko mana dashi nan zai fi" tace to,ta fara kiran Saude,daga cikin corridorn da bedrooms suke Saude ta fito tana yafa kallabinta,hajiya ta bata umarnin ta kawo masu Abinci cikin parlor,ta juya ta fara kawo masu,kafin ta gama jerawa Kawu Mani ya juya yana tambayar hajiya"hajjaju ya wajen mutanen Lagos,hajiya Maryam da k'waran mijinta kwana biyu bamu gaisa ba? Daria hajiya tayi tace "suna nan lafiya lau",a lokacin Saude ta gama serving abincin saman lallausan Carpet d'in parlon bayan ta gaishe su tace masu"Bismillah" suka amsa da "to" had'i da yi mata godia,ta juya ta koma ciki Hajiya ma tace masu zata d'an shiga ciki kafin su gama.
*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
*Mallakin*
⬇️
*ZAINAB LALUH*🌹
*(Oummu imam)*
*Littafin A Sanadin Makwabtaka 300 ne,ga mai bukatar ci gaba da karanta shi bayan angama Free Pages sai ya tuntube ni ta wadannan numbers din 09016265659 ko 09013804524,pls just whatsapp banda phone call,Thanks🤝*
*Free page1️⃣6️⃣&1️⃣7️⃣*