← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 137

Sashe 20

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haulat ce keta faman sauri da yamma zata islamiyya don ta makara sakamakon aikenta siyen gero da Innarsu tayi,tana k'okarin shiga lungun da zai kaita har islamiyyar taji daga gefenta ana magana "Ke,ke yar liman wait" da sauri ta juya tana kallon mai maganan,ya nufota yana wata irin tafiya irin ta nigas,da mamaki haulat ke kallonsa tana tunanin ita miye had'inta da Gaye da zai tsaida ta,yana k'arasowa yace"Ke dalla tambayanki zanyi kike ta faman zare ido uwa mujiya" ita dai haulat shiru tayi tana jiran jin abunda zai ce,ya ci gaba "dama tambayanki zanyi k'awarnan taki an kamata tana can cikin cell ne ko har anyi gaba da ita? cikin rashin fahimtar zancen shi haulat tace "wace kawar tawa kuma? Wata yar iskar daria yayi yace "kina da wata k'awa ne bayan Aljanar yarinyar nan mara jin magana, kullum ba tare nike ganinku ba" nan take ta gane Fatuu yake nufi don duk in suna tare suka had'u dashi Aljana yake cema fatun,da sauri haulat tace "to mitayi da za'a kai ta cell kuma? tayi maganar cike da fargaba tana ta zare ido, rik'e ha6a gaye yayi yace "wai kina nufin baki san aika-aikar da aljanar nan ta aikata ba...? da sauri haulat ta girgiza masa kai alamar a'a, jinjina kai yayi yace"tabb,to wllh ruwa ta 6allo ma kanta don ina tabbatar maki sai taje gidan yari..." da sauri haulat ta dafe k'irji tana salati tace"don Allah Gaye ka gaya man abunda tayi,ni sam wllh bansani ba" sai da ya gyara tsayuwa ya karkace baki yace "to bari kiji wani mutum ne jiya hakanan Aljanar nan ta jefar masa glass d'in bayan mota,gaba daya ta dagargaza glass din don wannan glass din yayi konden..." cikin tsananin tashin hankali haulat tasa hannuwanta duka biyu ta rufe bakinta ya ci gaba "atoh kima fad'a mata ta shirya don comfat (confirm) in ba'a biya shi ba har yakai k'ara na rantse da Assamadu sai taje fursun,yo motar fa ba k'aramar mota bace,to tsaya ma kiji,mai motar dan gidan Hajiyar Sanata ne kinsan kuwa ba'a k'aramar harka a gidan nan......" daga haka ya kad'a kai yayi gaba abunshi,

kasa motsawa haulat tayi na tsawon lokaci da k'yar ta juya taci gaba da tafiya a hankali gabanta sai fad'uwa yake tamkar itace akace zata gidan yarin,cikin zuciyarta kam mamaki kawai take na abunda fatun ta aikata,ashe asarar da take nufin mutumin yayi kenan,"tabb lallai Fatuu bata da hankali!" ta fad'a a fili tana jinjina kai.
A daidai bakin ajinsu ta tsaya tana tunanin shiga don tasan ta makara gashi akwae malami cikin ajin,can dai tayi shahada ta kutsa kai tare da yin yar sallama,d'an kallonta malamin yayi yaci gaba da bayanin da yake hakan yasa haulat yin saurin shigewa ta nufi wurin zamansu sai dai ga mamakinta Fatuu bata a wurin,tunani ta fara yi a ranta bayan ta zauna"to Fatuu bata zo bane? Kodai anje an kamata...wani irin bugu gabanta yayi da sauri ta d'ago da kanta a lokacin kuma ta hango fatun acan dayan bangaren,tunda haulat ta shigo ta wuce Fatuu ta ganta a ranta tace "da nice na makara da ya buge ni,ni da kowa ya tsana"ta saci kallon malamin ta d'an hararesa kafin ta juya inda haulat take nan take suka had'a ido don tunda ta hango fatuu take ta kallonta cike da al'ajabin abunda gaye yace zai sameta,murgude fatuu tayi mata ta juya,haulat ta girgiza kai cike da tausayinta,ta kuma fahimci dalilin da yasa fatun ta canja wurin zama don ta saba hakan da d'an abu ya hada su wanda bai kai ya kawo ba sai ta canja wurin zama sai tagadama ta dawo ko haulat taje ta bata hakuri sannan ta dawo,haulat ce kad'ai ke iya jure halin fatuu don ta karanci halayenta tsab shiyasa ma bata biye ta.

Haulat ce keta sauri ta isko Fatuu don da aka tashi ta tsaya copying rubutun da malam yayi bata nan daga littafin wata kawarta da suke zama tare,ita kuwa Fatuu ana tashi tayi gaba abunta don guje ma haulat din take karta k'ara tambayarta game da asaran da tace Mutumin daya raba su fad'a yayi don tasan halinta wani lokacin nacin tambaya ne da ita kuma karshe inta gano tana iya zuwa ta fadi ma gwaggo "Fatuu!fatuu ki tsaya" haulat dake biye da ita a baya tace,ganin bata da niyyar tsayawa yasa haulat yin dan gudu tasha gabanta,cak fatuu ta tsaya fuska ad'aure tace "miye haka zaki wani shage gaba na" kasa magana haulat tayi don k'arfin halin fatun mugun mamaki yake bata ta aikata irin wannan babbar ta'asar amman hankalinta akwance,tsoki fatuu taja tana kokarin bin ta gefen haulat din,taji tace "To ai yanzu nasan abunda kike 6oyewa hajia" da sauri fatuu ta kalleta sama da k'asa tace "ni mi nike 6oyewa? Haulat ta jinjina kai cike da takaici tace "asarar da kika ce mutumin nan yayi na tambayeki wace asara ce kika k'i fad'a man to yanzu nasan komai,ke yanzu fatuu abunda kika yi kin kyauta?hakanan ki jefar ma mutum mota har ki lalata masa glass....."katse ta Fatuu tayi da fad'in "naje na fasa d'in,dama nasan ai sai kin bi diddigi don kin saba sa man ido,to na fasan kuma ko gobe ya k'ara shiga harkata har ya d'aga hannu ya mareni sai na kara ja masa asara don ni ba ai man na kyale ehe" daga haka ta kad'a kai tayi gaba,cikin d'aga murya haulat tace "to kinsan wanene kika fasa ma gilashin mota.....? a fusace ta juyo tace"ina ruwana da ko waye,Allah yasa d'an sarkin makkah ne" ta juya taci gaba da tafiya abunta don ita tayi tunanin tambayarta haulat d'in tayi,cike da takaici haulat tai tsaye tana kallon bayanta a fili tace "lallai Fatuu bata da hankali wllh bata san bala'en da ta jawo ma kanta bane,tama k'i ta tsaya ta saurare ni...." girgiza kai tayi ta fara tafiya tana ta sak'e sak'e a ranta "ko dai inje in sanarma gwaggo don tasan halin da ake aciki..." girgiza kai ta sake yi da sauri a fili tace "kai a'a,bai kamata ta fara jin wannan mummunan labarin daga baki na ba gaskia" can kuma tace "to wai ma ni ina ruwana da zan damu,ita wadda ta aikata laifin ma ko a jikinta,kawai dai ba dad'i ne kana tare da mutum wani mummunan abu ya same shi,to amman tunda ita taja ma kanta ai ita ta sani" ta watsa hannuwa,daina bin bayan fatun tayi,ta canza hanya,lokacin da fatuu zata sha kwana ta juya bata ga haulat d'in ba ta6e baki tayi a ranta tace gwara da nayi mata haka inba haka ba sai tace zata zo ta gaya ma gwaggo,a fili tace "inma tazo ta fadan sai in k'aryata ta tunda dai ba a gabanta akayi ba kuma bata da shaida" tayi k'wafa tace "ta sake ta gaya ma gwaggo wllh 6atawa zamu yi ba ruwana da ita" tayi maganar tana mummurgud'a baki,To hajia Fatuu ba dai yau kika fara fadin haka ba,kuma ko kun 6ata da kanku dai kuke shiryawa don keda haulat sai Allah.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

*Mallakin*
⬇️
*ZAINAB LALUH*🌹
*(Oummu imam)*

Free Page1️⃣8️⃣

Gwaggo ce ta fito daga cikin kitchen lokacin ba'a dade da gama sallar isha ba,hannunta d'auke da d'an kwanon silver madaidaici rufe da murfinsa asaman shi kuma bakar leda ce dauke da wani abu an kulle, tsayawa tayi ta fara kwala ma fatuu kira "Fatuu,fatuu,Worei mi lilma", leko kanta tayi ta jikin labule tace" ina zaki aike ni?" hajia zaki kaima tuwon nan nasanta da son tuwon dawa" da sauri ta fito jin za'a aiketa wurin Hajiyar Sanata,hannunta rik'e da k'aramin bak'in gyale ta fara k'okarin cire hijab d'in islamiyya dake jikinta tana fad'in "dama kwana biyu banje ba wllh...."

Gwaggo tace"to miye na cire hijab d'in kuma,kibarta mana" turo baki tayi tace"ni nafi son in sa gyalen kinga na fi shan iska ma",
gwaggo tace "A daren nan zaki sa wannan figaggen gyalen da iyakarsa kafad'a,to bar aiken ni bari in mik'a mata da kaina..." da sauri tace "a'a to yi hakuri nabar hijab din" tayi maganar tana d'aga hannu alamar ban hakuri,
gwaggo ta mik'a mata kwanon tace "kiyi maza ki kai mata kidawo,sauran kuma ki tsaya shiririta sai tsakan dare ki dawo" dariya tayi ta amshi kwanon ta rungume tana fad'in yanzun nan zan dawo kakus, Gwaggo tace "to ki d'aura akai mana salon miyan ta zubo ta 6ata maki hijab din",
fatuu tace "bazata zubo ba zan kula" abunda gwaggo bata lura ba fatun ta 6oye gyalen da ta hanata sawa a kasan hammata shiyasa tak'i daura kwanon aka don kar ya fad'o ta gani,

A zaure ta aje kwanon k'asa ta cire hijab din ta sagale ta jikin windon d'akin kawu Amadu tasa gyalen kana ta nufi gidan Hajia.
Chapter 20 · 0% Book details