← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 137

Sashe 8

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*BY OUMMU IMAM📲*

*Free Page7️⃣*

Da d'an hanzari ya nufi Part dinsa bayan ya fito daga part din hajiar,hango T.k yayi cikin Parking spot yana ta faman goge motar daya dawo da ita,hakan yasa ya juya shima ya nufi Parking space din ya d'aga ma T.k hannu alamar yazo,da sauri T.k ya daura dan towel d'in saman motar ya nufo sa tun kafin ya k'araso wurin shi ya d'an daga murya yace "My bag" hadi da yi masa alama da hannunsa wato ya d'aukko masa jaka.
Juyawa T.k yayi da dan gudu gudu ya nufi part d'insa,shikuma ya shiga cikin Parking space din yana kokarin fiddo da Bike din,daidai lokacin da ya fito dashi cikin harabar T.k ya dawo d'auke da jakar,wata katuwar jakar goyo ce sandar racket ta leko ta cikin jakar ya rataya hannunta daya a bayansa,saukko da jakar yayi yana kok'arin mika masa ya tsaida shi,alama yayi masa da hannu ya bud'a jakar hakan yasa T.k ya aje jakar kasa sannan ya bud'e.
Umarni yayi mashi da ya fiddo masa takalman ciki,T.k yasa hannu ya fiddo da wasu kambos masu kyau ya mika masa kana ya zuge zip d'in jakar,
D'an jujjuya su yayi da alama basu yake son sawa ba,sai kuma ya juya hannunsa ya duba agogo,ganin lokaci yaja yasa ya duk'a don yasa takalman cire na kafarsa yayi sannan yasa kambas din,ya mike lokacin da ya gama daura igiyoyin takalmin ya haye saman Bike din ya zauna sosae,shi kam T.k sai faman kallon mashin d'in yake ko kyaftawa bai yi,
Hannu Haisam ya mik'a ya ciro helmet (hular kwano) daga saman kan bike din yana kokarin sawa a kansa,juyawa yayi ya kalli T.k wanda ke tsaye k'ikam da jaka a hannu ya k'ura masa idanu.
Yace"Yadae T.k,ko zaka d'ana ne? da sauri T.k yace "Ah yalla6ai wannan ai sai ku,yafi karfina" yayi maganar yana daria,d'an murmushi Haisam yayi yace"Saboda me yafi karfin ka baka iya mashin ba? Da sauri T.k yace "Na iya yalla6ai irin dai namu wanda aka saba hawa,banda wannan ni tsoronsa ma nike wllh ko goge sa nike sai inta ganin kaman zai fad'o ya danne ni, shiyasa duk in ina goge shi ban yarda na duk'a k'asa" ya karasa maganar yana ta faman daria,shima Haisam din yar daria yayi,ya mik'a masa hannu lokacin da ya gama sa hular alamar ya bashi jakar,da sauri T.k ya mik'a masa,ya amsa ya goya ta a bayansa sosae,d'an juyowa yayi ta cikin hular yace,
"Ka shirya soon zaka d'ana don bai yiwuwa kana masa wahala amman baka ta6a hawa ba" yayi maganar da sigar tsokana hakan kuma na nuni da yana shiri da T.k din har suke magana haka,
Zaro ido T.k yayi sosae yace "Nidai yalla6ai wallahi na yafe" ya d'an daga hannunsa, shikam Haisam daria yake ta cikin hulan ganin yadda T.k ya zaro ido yana mamakin yadda kowa ke tsoron bike din wanda shi kam sarrafa sa yake tamkar ya hau keke,don sun saba yin gasar tsere dashi a U.S,A daidai lokacin ya kunna bike d'in yana murza shi, kararsa ta karad'e cikin gidan ji kake wani "BHUUMMM²...." da sauri T.k yaja baya,yayin da d'aya daga cikin Officers din bakin gate ya mik'e da sauri ya kama gate din yana sliding din sa,dayan kuma yace"Bari mutum ya matsa kar a d'ebi kwanyarsa yanzun nan" gaba d'aya suka sa daria,A daidai nan kuma Haisam ya taho da gudu,da sauri Officer din daya bude Gate yayi tsalle sai gashi a gefe guda,gaba d'aya ya basu daria sosae harda Haisam din wanda ya fice.
Hajiya dake zaune a Parlour tana jin k'arar Bike din tasa hannu ta rufe kunnuwanta har saida ya fice kana ta bud'e,girgiza kai tayi a fili tace
"Allah Ya Tsare".
________________________________
Fitowa daga cikin dakin Fatuu tayi,kofar d'akin gwaggo ta nufa sarai fa taji abunda gwaggon tace tayi amman saboda jan magana taje kofar d'akin tana cewa "gwaggo gani" daga cikin d'akin gwaggon tace "baki ji mi nace kije kiyi bane? "Eh" taba gwaggon amsa,
"Kije cikin kitchen nace garin tuwo na nan cikin roba kiyi sauri ki tankad'e" Juyawa tayi ta nufi kicin d'in wanda ke a gaban dakinta tana ta faman zum6ura baki tana k'unkuni da gani bata son yin tankad'an.
Daukko garin tayi ta fito kofar kicin din ta aje robar da karfi duk don jan magana,ta koma ta daukko tray din silver da rariya shima ta sake shi k'asan yayi k'ara sosae,daga cikin daki gwaggo tace"A'ah Fatuu lafian ki kuwa? Cikin turo baki tace"fad'uwa yayi" gwaggo tace "Yi maza ki gama to",
Zaunawa tayi k'asa dirshan ta fara yin tankad'an fuska daure,fitowa gwaggo tayi don ta fara had'a wutar yin tuwon a bakin k'ofa ta tsaya cak tana karema Fatuu kallo wadda duk tayi dama dama da gari har a kumatun ta,gashi duk ta zuzzubar a k'asa,karasowa inda take gwaggo tayi tace "Yanzu don Allah garin ne kika yima haka,kuma miya kai gari har a fuska?Shiru Fatun tayi sai faman d'aure fuska take,"ba da ke nike bane? Sannan tace"Ni fa bamma san ya zuba ba" "To mi akai miki kike ta faman d'aure fuska,hala tankad'en ne baki son yi? "A'ah" tace sannan taci gaba da magana tana turo baki "kema ce gwaggo wllh....sai kuma tayi shiru, "Nima ce mi? Gwaggo ta tambaya tana kallon ta da mamakin jin tace itace to ita mi tayi kuma.
"Sai kiyi ta faman yi mana tuwo,sai kin kashe mu dashi" hannu gwaggo tasa ta rike baki alamar mamaki tace"Ni din ce zan kashe ku da tuwo,har da yaushe yaushe nake yin tuwon da zai kashe ku, Amman wllh fatuu baki da godiar Allah sam,ko yau da rana ba shinkafa da wake nayi maku ba?"
"To ai baki yin shinkafar ne muci ta har dare sai ki tayin tuwo da daren,kuma wani lokacin ma har da safe sai kice wai shi za'a ci" tayi maganar tana ta turo baki.
"To bazan yi shinkafar har daren ba tunda bake ke nemo man kudin shinkafar ba,iya fitina kawai da asara kika iya siyo man,inma baya ga sharrinki ba sai ina nan da yamman nike samun yin tuwon ba,Kuma in bama samun wuri ba acan k'auyen naku ba tuwon kuke ci ba rana da dare wani lokacin har a d'umama da safen gwarama ni,in anci da safe ana had'awa da wani abun,ko ke ai sai kin gadama kike ci da safen ko" tana ta magana har ta shiga cikin kicin ta fito da murhu ta nufi can bangaren d'akinta wani dan fili ne anyi rabin katanga ba'a ida ba akwae keji da yan kaji a ciki ta aje murhun ta fara d'aukko itace daga gefen cage din tana sawa acikin murhun,
"Wallahi mu bama yin tuwo rana da dare,wannan ai sai su Yaaya dasu Altine,mu fa kinsan yan gayu ne a gidan,don mu har shayi da biredi muke sha,kuma ana mana shinkafa da miya har da naman zabbi ehe" Ta karasa maganar tana murgud'a baki don tasan gwaggon ba ganinta take ba,
Daga inda gwaggo take tana kok'arin daura tukunya saman murhu tace "Ai sai ki tattara ki koma can din kici gaba da shan shayi da shinkafar tunda ni nan kashe ki zan da tuwo" da d'an fada fada tayi maganar,itakam fatuu sai ta kyalkyace da daria tace "Ai ko na tafi sai kinje kin dawo dani,don nasan baki iya zama ba tare dani ba"
Girgiza kai kawai gwaggo tayi,don tasan inta biye mata haka zatai ta mata surutan banza da wofi "In kin gama kije ki wanke man tsakin kuma ki sauri",
"To" fatun tace tana kokarin mik'ewa,don taga kaman ran gwaggon ya 6aci ta kuma sani sarai mi zai iya biyo baya,Wanke tsakin take yi a wurin da ake wanke wanke ta fara magana"Gwaggo fushi kika yi?
ta6e baki tayi tace"Uhm,inyi fushi dake ince nayi fushi da wa,ai da mai cikakken hankali ake fushi...."da sauri Fatuu tace "Wayyo gwaggo ni d'in ce banda cikakken hankali,wllh inada hankali na" ta k'arasa maganar tana ta turo baki,
Chapter 8 · 0% Book details