← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 137

Sashe 2

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shi abun naki na nawa ne? ya tambaya."Awarar dubu da dari biyar ce gashi ta zubar da ita duka yar kadan ce bata baci da k'asa ba,inaga ma ko ta d'ari biyu bata wuce ba,wllh gidansu zanje sai anbiya mu ta k'ara fashewa da kuka,da alama taji zafin abun sosai, Sigh yayi kafin yace"You know what,ku kyaleta kawae tunda bata jin mgn in kun k'ara zuwa kun kai karanta zata k'ara zubar maki da abu,calmly yayi maganar,Hannu yasa a cikin aljihun wandon suit din jikinsa bak'ar Wallet ya fiddo mai kyaun gaske ya bude,Kudi ya kirgo sababbi fil kamar lokacin aka buga su,mik'ama yarinyar yayi wadda ke tsaye ta kafe sa da idanu tasa hannu da sauri ta kar6a,aje fasassan bokitin tayi a kasa ta fara kirga kudin dubu ukku ta gani da tsananin mamaki ta d'ago lokacin har ya juya da sauri tace"Yallabai kudin sunyi yawa ai" Hannu yad'an daga ba tare da ya juyo ba yace"ku siya sabon bucket da sauran" ya cigaba da tafia wurin da motarsa take,
Mai tallan kuwa har lokacin juya kudin take da mamaki hakanan bai santa ba ya bata har dubu ukku da sauri tabi bayansa tana fadin "Yalla6ai,yalla6ai..." lokacin har ya kama k'ofar motar zai bude jin yadda take ta faman kiransa da yallabai yasa shi juyowa"What again? Ya tambaya da kosawa,"umm dama².... ta kama inda-inda sakamakon kafeta da ido da yayi,ya lura da yadda ta dabarbarce,dan sakin fuska yayi yace"Uhum ina jinki dama me? Dama so nike in tambayeka in innarmu ta tambayi wanda ya ban kudin wa zance mata? ta k'arasa maganar tana sunnar da kai k'asa"just tell her wh....ki fada mata abunda ya faru kawai"ya juya zai shege cikin motar, da sauri tace "ai tana iya cewa k'arya nike ni na tsara hakan kullum tana ce mana kar wani ya bamu kud'i bamu san shi b,ko yace zai siye mana yayi mana abunda bai dace ba"ta gama maganar kanta a kasa,
d'an murmushi yayi na gefen fuska wurin ya lotsa alamar yana da dimple,yaji dadin maganar da tayi ko ba komai hakan ya nuna rashi ne yasa suke tallan ba wai ra'ayi ko son kudi na wasu iyayen, Juyawa yayi yabude motar ya shige ya jawo kofar ya rufe,tana dai ta kallonsa don gaba daya komae yayi burgeta yake sai da yayi ma motar key kafin ya bude Glove box din gaban motar kudi ya kirgo dubu biyu juyawa yayi ya mik'a mata da d'an murmushi a fuskarsa yace "ki hada da wannan ki kai ma Mom din naki" Maida hannunsa yayi ya murza key din jikin motar tana dai ta kallonsa da tsananin mamaki sai da motar ta tashi sannan glass din murfin motar ya fara rufewa sama a hankali juyawa yayi ya kalli yarinyar da har lokacin take tsaye tana ta faman binsa da idanu "Ki ce ma Mom din naki dan gidan HAJIYAR SENATOR ne ya baki" daga haka ya ja motar fuuuu,
"Hajiar Sanata! Yarinyar ta maimaita da mamaki had'i da rike ha6arta da hannunta daya,sai kuma ta saki wata irin dariar farinciki da sauri ta juya komawa tayi inda sauran Awarar ke a zube k'asa tace "bari in kara dan kwashe wadda batayi k'asa sosae ba da ansa cikin mai k'asar zata fita ko mu sai muci" a saman marfin bokitin ta zuba mai kasar,mikewa tayi da dan gudu-gudu ta koma cikin lungun da suka fito tun da farko.

Yarinyar data 6arar da Awarar ce ta lek'o da kanta daga cikin zauren gidan da ta 6uya,round face gare ta mai dauke da madaidaicin hanci mai dan tsawo tana da dan kumatu,idanuwanta kuwa suna da dan girma sam baza'a kira su da k'ananu ba,tana da gashin gira wanda yake kwance lub haka kuma gashin idonta nada tsawo gazar-gazar bakinta madaidaici ne le6anta na k'asa nada dan fad'i sosae,kalar fatar ta kuwa fara ce sai dai ba sol ba,Amman kana kallonta zaka kirata da fara, sai da ta waiwaya hagu da dama ta tabbatar ba kowa kana ta fito,cikin sand'a take tafiya tana yi tana waiwaye har ta iso bakin lungun daidai inda ta 6arar da awarar,tsayawa tayi tana kallon sauran awarar dake a k'asa, Kafarta tasa tana tattake awarar tana cewa"Gobe ma ta kara sawa a doke ni" ta fada a fili tana mummurguda bakinta gefen kumatun ta na lotsawa sosae alamar tana da dimples, jin k'arar mota ta taho a bayanta yasa tayi saurin juyawa hadi da d'an tattare Skirt dinta da hannayenta biyu tana shirin rugawa ganin ba motar mutumin d'azun bace yasa ta saki skirt dinta tace "In ma shine yazo banjin tsoron sa koda kuwa Aljani ne ehee" ta fad'a lokacin da ta fara tafia ta miki hanya tana yi tana waiwayen bayanta tana watsa hannuwa gami da turo baki,

Yar tafiya tayi kafin ta iso bakin wani Gida wanda keda shafen plaster ba fenti a jikin bangon gidan daga gaban gidan akwae k'atuwar kwata wadda ke zagaye da gaban gidajen layin saidai a rufe take da slabs daga d'an gefen kofar shiga gidan akwae Kiosk a saman rufaffiyar kwatan gaban gidan,shiga cikin zauren gidan tayi wanda keda K'ofa da kuma Window a cikinsa da alama irin d'akin zauren nan ne,

A bakin kofar shiga cikin gidan ta tsaya,dan leka cikin tsakar gidan tayi wanda yake wayam ba kowa,dawo da kanta tayi cikin zauren ta rik'e habarta da hannunta na dama tunani ta shiga yi "Ba'a kawo karar tawa bane?kodai sun zo har sun tafi" jinjina kai tayi a fili tace"Inma an kawo k'arar tawa nasan abunda zance,cewa zan yi tsokanata tayi,ta kuma yiman daria harda gwalo wai sun sa an bige ni" ta k'arasa maganar tana faman mummurguda baki dimples dinta na lotsawa,
A hankali tasa k'afa cikin gidan mai dan matsakaicin girma wanda kasan shi ke malale da siminti gaba daya,d'akuna biyu ne a cikin gidan wanda kofofin su na kallon juna,dakin da ke a bangaren dama babban daki ne yayin da na bangaren hagun k'arami ne a jikinsa kuma kicin yake wanda shine a farko in ka shigo gidan daga bangaren hagun,sai dan fili wanda da gani wurin yin Wanke-wanke ne a gefe daga tsakiyar filin akwae yar Bishiya,daga nan kuma sai Band'aki da ke a can gefe bangaren da kofar shigowa take,
Shiga tayi cikin gidan a hankali tana yin sand'a "Daga ina kike? Aka jefo mata tambaya daga bayanta,cikin yar razana ta juya,wata farar dattijuwar mata ce mai dan tsayi,sam bata da jiki sai dai ba siririya bace sosae tana da tsagun yan baka a bakinta,tsaye matar take da buta a hannunta da alama daga band'aki ta fito "dake nake Fatuu" ta k'ara fada da muryarta irin ta fulanin da suka ji hausa sosae,in'ina fatun ta fara yi,ta rasa mi zata ce don tunani take ko an kawo karar abunda tayi ma mai tallar Awarar nan,"Halan kina can wurin jawo man fitinar da kika saba ko" ta k'ara jefo mata tambaya,da sauri fatun tace "A'a gwaggo.." tana ta faman zare ido "to ki fadan ina kika je don na lek'a neman ki da kaina baki a waje" Goggon ta fada ta kafe ta da idanu,"Umm... gidan Hajiyar Sanata naje gaishe ta" taba gwaggon amsa da alamun rashin gaskia a fuskar ta,"Allah yasa da gaske kike don banga ranar da garin Allah zai waye har rana ya fadi baki jawo mun fitina ba" jin hakan yasa fatun gane ba'a kawo k'arar abunda tayi ba" da karfin gwiwa tace "Allah gwaggo daga can nake fa" gwaggon tace"to wannan d'amarar da kika ci da gyalen ki ta mene?" "ba komai kawai gyalen ne ya ishe ni yana ta fad'uwa shine na kulle shi anan" tayi maganar tana kokarin kwance gyalen daga kugunta,
gwaggon taci gaba da magana"Ai in ance kisa hijabi sai ki k'iya sam bakya son sa hijab ke kinfi son gyale gashi ko yafawar ma baki iya ba kullum yana ruke a hannu ko daure a k'ugu,to ina amfanin hakan in anyi magana kice ke baki saba sa hijab a kauye ba" ta karasa maganar tana shiga cikin gidan,
"Allah gwaggo hijab din shak'e ni yake fa, ni ban saba sawa ba,acan ruga fa wani lokacin ko gyalen ma ba sawa muke ba" ta karasa maganar da sigar shagwa6a tana bin bayan gwaggon "Ai sai ki tayi tunda anfad'a maki nan ma kauyen ne, da kina son sa hijab din ai da yanzu kin saba dashi yaushe rabon ki da kauyen kusan shekara ta ukku kenan fa, kawae dai kin fi son kisa gyalen yadda zaki ji dadin nemo man fitina,Kullum cikin daukko man magana kike nikam na fara gajiya wllh kuma zan yi maganin ki indai baki bari ba tunda na lura sam duka bai maki" ta k'arasa maganar lokacin da ta iso bakin kofar dakin da ke a bangaren dama, d'aga labulan kofar tayi ta shige harda butar da ke a hannunta,ita kuwa fatun labulan kofar da ke kallon wadda gwaggon ta shiga ita ma ta daga ta shige,dakin baida girma sosae, akwae Gado irin na karfe mai spring yana da bakin fenti da katifa wadda aka rufe da tsohon zanin gado,A bangon dake kallon gadon kuwa wardrobe ce mai gida biyu da kananun gidaje a kasa suma guda biyu,ta dan ji jiki sannan yar madaidaiciya ce ba mai tsawo ba,a samanta akwae jakunkuna,daga gefen ta kuma dressing mirror ne kalar ta shima karami ne wanda hannuwan drawers din jikin shi wasu duk sun balle haka mirror din jiki dan guntu ya rage,akwai leda shimfide a dakin wadda ta ji jiki don duk wasu wurare sun farfashe,Saman gadon ta fada hadi da fadin "Washh" sai kace wadda tayi wani uban aiki banda neman rigima,tunani taci gaba da yi "ko sai yaushe zasu kawo kara tan..." k'wafa tayi a fili tace"Allah yasa su kara sawa a doke ni wllh nasan abunda zan yi masu...."Muryar gwaggon tace ta katse ta"fatuu fito ki tankade man garin can na cikin kicin yamma tayi in samu in daura girki......,Fatuu ko bakya jina ne wai? cikin d'aga murya tace "Ina ji fa,gani nan fitowa.." mik'ewa tayi ta nufi k'ofa sai faman k'unkuni take tana jujjuya kai alamar bata son yin abunda aka sata yi.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*

*STORY*
&
*WRITTEN*
BY
*OUMMU IMAM*

*Free page3️⃣&4️⃣*
Chapter 2 · 0% Book details