← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 137

Sashe 104

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lah ga Haulat gidanmu zata mutafi idi tare" Fatuu ta fad'a da sauri, burki yaja ya tsaya tana niyyar kai hannu ta bud'e kopar taga ya sauke mata glass d'in hakan yasa ta lek'a kanta ta kwala ma Haulat d'in kira, koda ta juyo taga Fatuu bud'a ido tai tana kallonta cike da mamaki, da hannu tay mata alamar ta taho hakan yasa ta nufo Motar, alamar ta shigo tai mata ta kai hannu ta bud'e kopar baya ta shiga, har sai da ta lumshe idanunta kafin ta daidaita zamanta yaja suka tafi, gaidashi tay tayi mashi barka da sallah ya amsa mata a hankali, bayan sun isa a waje can gefen Masallacin ya parker Motar don Area d'in wurin dankam take da Motoci bayan sun shiga sashen Mata suka nufa anan kuma suka hango su gwaggo don suma basu dad'e da isa ba, Alhamdulillah anyi salla an gama lafiya sai gaishe gaishe Mutane keyi suna yima juna barka da sallah da kuma fatan anyi ibada karbabbiya yayin da wasu suka fara daukar hotuna ciki harda su Tk da Amadu Fatuu na hango su taja hannun Haulat don suje suma ai masu hoton, Hajiya kam tuni Jama'a suka zagayeta suna ta yimata barka da salla, sosae take farinciki cikin fara'a take amsa ma Mutane don yin sallar anan ba k'aramin nishadi ta samu ba yayin da wadanda basu san wacece ba ke tambaya ana fad'a masu matar tsohon Ministan tsaro ce mahaifiyar Senator Ali Adamu Zakee kuma Mamallakiyar HAZ FOUNDATION, gidauniyar tallafa ma Marayu da gajiyayyu da kuma koya sana'oi, bayan masu kawo mata gaisuwar sun lafa ne Tk yazo yace bari yay masu hotona, sosae sukae Hotunan harda wanda Masu daukar hotuna wato photographers dake cikin Masallacin Hajiya tasa suyi masu, ganin anata hotuna ba Haisam ne yasa Fatuu wawwaigawa ko zata hangoshi amman sam bata ganshi ba hakan yasa ta fita daga cikin masallacin ta nufi Motarshi aikuwa sai gashi a ciki ya d'an kwantar da kanshi kafarshi guda ya zurota waje don kopar a bude take yanata latsa wayarshi, ba komae ne yasashi dawowa cikin Motar ba illa kallonshi da ake tayi shi kuma ya tsani kallo ba kamar Mata wasu har nunashi suke suna fad'in da gani ba d'an Nigeria bane, cikin Masu kallonshi harda Boss Bature can na hangota ta saki baki tana kallonshi har tana fadin " bala'i kuji wani wanda yaci uban Baby Junaid kyau🤣,

Koda Fatuu tace mashi yazo suje ana yin hotuna girgiza mata kai yay alamar bazaije ba don shi baison yan d'auke dauken hotuna hakan a wurinshi ma kauyanci ne shiyasa in ba dole ba bai tsayawa ai ta yi mashi hotuna barkatai, jin bazaije bane yasata cewa to yayi masu ita dashi, da farko ki yay ta fara mashi magiya sannan ya shiga Camera d'in yay mata alamar tazo, ida fito da d'ayar kafarshi yay taje gefenshi ta d'an kwanto da kanta ya daukesu gaba d'aya sun d'anyi Murmushi, rok'onshi tay ya mik'e ya daukesu ta d'an jingina dashi tana dariya gashi tayi can k'asa ba tsawo amman dai ba k'aramin kyau hoton yay ba, ba kamar daya kasance sunyi shigar fari da bak'i ne,

( duk mai buk'atan ganin hotunansu yay ma Munah Bature Magana don a Masallaci d'aya sukai sallar wato Banu Commassie Masjid dake a GRA, can na hangota ta la6e ajikin wata bishiya tana d'aukarsu ba tare da saninsu ba, kwalelenki dae😹).

**** **** ****

Bayan sun bar Masallacin saida suka biya gidan Sarki, bayan sun fito daga gidanne gwaggo tace ma Amadu ya hau keke napep yaje ya amso mata aikin abinci data bada sai ya iskesu gida, Hajiya na jin haka tace to ba a Mota suke ba miyasa bazasu biya su amsa ba kawae gwaggon tace ai kada a 6ata masu lokaci Hajiyar tace ai ba wani abu bane suje kawae, bayan sunje sun amshi abincinne suka nufi gida lokacin tuni su Fatuu sun koma don suna baro gidan sarki Haisam ya wuce dasu gida ana sauke Haulat itama ta sauka tabita gidan nasu don tayi ma innarsu barka da Sallah, sosae Innarsu haulatu ta yaba da wankan Fatuu har barka da salla ta bata Haulat ta zubo masu abinci suka ci, su gwaggo na komawa gida ta zuba dukkan abincin tuwo, waina, Alkubus acikin Manyan Warmers taba Amadu ya kaima Hajiya, lokacin da ya kai mata sosae tai farinciki da abincin ba kamar Alkubus d'in ya burgeta don yayi kyau ya tashi sosae nan da nan tace ma Saude ta zubo masu su ci, kan kace mi gidan hajiya ya cika da yan yawon salla duk wanda yazo aka bashi barka da salla sai ya ruga ya fad'i ma abokanansa, haka iyaye mata duk wadda taji cewa Hajiya anan tayi Sallah sai ta zuba abinci tace akaimata nan aka cika hajiya da abinci sai faman farinciki take tana sawa ana daukarta hotuna da yaran unguwa daga baya kuma iyayen suka rinka shigowa suna yi mata barka da shan ruwa da fatan anyi salla lafiya.

( zaka kasance acikin farinciki matukar kaima kana sanya Mutane farinciki kuma Allah yana cigaba da taimakon bawansa matukar bawan na taimakon na kasa dashi)

Ana yin sallar Azahar Fatuu ta canja kaya tasa fitted gown dinta don kuwa da gwaggo ta amshe tace bazata sakasu ba sai taje takai kararta wurin hajiya tace gwaggo ta amshe mata kayan da Ya Handsome ya dinka mata tace wai bazata sasu da salla ba hakan yasa Hajiyar kiran gwaggon a waya ta tambayi dalilin amshe kayan gwaggo tayi mata bayanin irin dinkin da fatun tasa akayi mata, karshe dae Hajiyar tasa gwaggon ta bata kayan tace tunda an riga an dinka ba yadda za'ai sai hakuri, wurin gwaggo taje ta d'aura mata kallabi, da tace bata d'aurawa daga baya kuma ta amsa tana d'aura mata tana k'orafin yadda rigar ta kamata, d'auri mai kyau tayi mata ga gashinta ta faka shi ya sauka abayanta don ma gwaggo ta lankwashe shi, tana komawa d'akinta tasa takalmanta ta dauresu ta kuma sanya sarkar da Haisam ya siya mata wadda tamkar gold haka take, d'aura gyalenta tay akan kafad'a ta d'auki yar jakarta mahadin takalman daga haka ta fito ta nufi gidan Hajiya, ta k'aramar kopa tabi ta nufi part d'in Haisam, tana shiga cikin falon taja ta tsaya a bakin kopa tana bin Mutanen dake a cikin Falon da kallo wad'anda maza ne guda ukku kowannensu yaci gayu cikin sabuwar shadda gaba d'aya falon ya k'ara hadewa da wani irin hadaddan kamshi mai bugun zuciya, wurga ido taci gaba da yi tana son hango Haisam saidae babu shi acikinsu,

"Welcome Mom Zarah ki shigo mana" taji wani cikinsu ya fad'a hakan yasa takai idanunta da sauri kanshi, Abbas ne yana sanye cikin galleliyar shadda ash ya d'an kishingida ajikin kujera dama gaba dayansu suna akan L-shape ne ga kayan abinci birjik kan c-table da alama basu dad'e da gama ci ba don duk ga lemu nan acikin glass cups an rage, koda tay arba da Abbas sai kawae ta sakar mashi Murmushi don yanzu sun saba dashi sosae, mayar mata da martanin Murmushin yay ya nuna mata armchair alamar taje ta zauna saida ta duk'a ta cire takalmanta kafin ta nufi kujerar don ta zauna yayin da sauran Mutum biyun suka bita da ido, gaishe dasu tai gaba d'aya bayan ta zauna suka amsa banda Mutum d'aya da shi jinjina mata kai kawae yay fari ne don duk yafi su haske saidae sam bai kai Haisam ba yana sanye da farar shadda ya aje hularshi gefe kaman dae sauran suma duk sun cire hulunansu hakan kuma ya bayyanar da yalwatacciyar sumar kansu, d'ayan kuma za'a iya kiransa da Chocolate yana sanye da Brown shadda wadda ta hau fatar jinkinshi sosae har sun so sajewa, gaba d'ayansu ba mummuna kuma kallo d'aya zakai masu kasan yan hutu ne don shi mai farar Shaddar wato Saleem babanshi ne Deputy Governor na yanzu sai mai Brown shaddar wato Najeeb shi babanshi ba mai mukamin gwamnati bane saidae shahararren mai kudine a Katsina wanda idan za'a lissafa masu kudi a Nigeria to tabbas za'a fade shi, gaba d'ayansu Abokan Haisam ne tun yarinta don shi Saleem d'in ma tare su kae karatu akasar waje.

"Mom Zarah ina barka da Sallah na?" Abbas ne yay Maganar, juyawa tai ta kalleshi ganin ita yake kallo yasa ta rufe bakinta da tafin hannunta tana dariya,
"Ba Dariya na tambayeki ba, ko bazaki bani bane?"
girgiza mashi kai tayi alamar zata bashin yace to ta bashi, mik'ewa tay ta nufi inda yake ta fiddo yan d'ari biyu guda biyu sabbi dama yanzu Tk ya bata su ta mik'a mashi, mik'o hannu yay ya amsa yace ya gode har zata juya yace ta tsaya shima ya bata, sabbin yan d'ari biyar guda hudu wato 2k ya miko mata, da tak'i Kar6a yace to shima ga nata baiso hakan yasa ta amshi nashin tace ta gode tana niyyar sake juyawa taji ance "Mu don ba'a sanmu ba kenan baza'a bamu ba",
da sauri takai idonta kan sauran Mutum biyun nan take ta gane wanda yay Maganar wato Najeeb saboda shine ke kallonta shi Saleem wayarshi yake daddannawa, mik'a mashi wanda Abbas ya bata kawae tayi don wani irin kallo yake binta dashi,

"No ba nashi nike so ba, muma naki zaki bamu" ya fad'a yana wani lumshe mata ido dama kuma haka yanayin idonshi yake sai yaso yake waresu, murya na d'an rawa tace "ai ba sauran irin wanda na bashi yan k'anana ne suka rage"
"No problem muna so" ya fad'a, hannu na rawa saboda kwarjinin da yay mata ta bud'e cikin jakar ta fiddo naira hamsin guda biyu da yan ashirin suma biyu naira d'ari da Arba'in, mik'a mashi su tayi duka sai ya cire hamsin d'aya da ashirin wato naira 70 ya bata sauran yace taba Saleem d'in da kanta, d'an matsawa tay ta mik'a mashi ganin bai kalleta ba yasa tace "gashi" a wani slow ya d'ago da kyakkyawar fuskarshi yabi kud'in da take mik'o mashin da kallo kafin ya d'aga manyan idanunshi ya kalleta,
Chapter 104 · 0% Book details