← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 137

Sashe 90

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Karfe takwas da rabi Gwaggo ta tada ita don tayi shirin islamiyya don yanzu da safe suke zuwa karfe 9 saboda anyi hutun boko kafin itama islamiyyar abasu hutun ranar Laraba, lokacin da ta shirya ta fito cikin Uniform direct gidan hajiya ta wuce, tana zuwa part d'in haisam ta iske kopan shiga falon a kulle lokacin da ta tura, shiru tayi tana tunanin k'ilan bai tashi ba, ko ta tafi sai anjima sai kuma ranta ya bata yau ba lalle Aunty Saude ta kyaleta ba batare da ta tafi islamiyya ba kuma lokacin da za'a taso rana ta fara gara ta bashi hakuri in ya yarda sai ta karya azumin kawae, Knocking kopar ta fara yi ahankali, jin ba'a da shirin bud'e mata yasa ta k'ara sautin bugun amman shiru har ta fara tunanin ko dai ya tafi aiki ne, har ta juya taji an bud'e kopar hakan yasa ta waiwayo da sauri, tsaye yay jikinshi na sanye da sleeping dress riga da wando Army green ba k'aramin fito mashi da farinshi kayan sukai ba, da ka kalli fuskarshi zaka gane daga bacci ya tashi, kallonta ya rink'a yi daga sama har k'asa fuskarshi a d'aure hakan yasa tayi saurin sunnar da kai k'asa, juyawa yay ya koma cikin falon ya zauna kan kujera had'i da d'age kanshi sama don har ya fara sara mashi, a rayuwarshi ya tsani yana bacci a tasheshi, bama wanda ya ta6a gigin yi masa hakan, ko Hajiya take da bukata awurinshi indae tasan yana bacci bata tadashi ko acan Abuja ma indae ba abu na gaggawa ne ya taso ba wanda dole dole sai ya tashin shine aka tashinshi, in kau ba haka ba duk wanda ya tasheshi sai ya fuskanci bacin rai, shi kanshi yasan yana d'aga ma Fatuu kafa sosae don a yadda ya taso da wani ne tabbas sai ya fuskanci bacin ranshi koda da dalili duk da itama fuskarshi ta nuna,

Tsaye tayi awurin ta kasa shiga ciki saboda yadda taga ya daure fuska tunani ta rink'a yi kodae ta tafi amman kuma tana bukatar rokonshi don lokacin da za'a taso islamiyya tasan rana tayi kuma indae tana azumin tasan sai tasha wahalar dawowa gida, wannan tunanin yasa ta fara tafiya ahankali kaman mai yin sand'a ta shiga cikin falon, ganin yadda ya d'age kai sama yasa taji tsoron k'arasawa ciki tai tsaye daga gaban kopan tana kallonshi,
Bayan wani d'an lokaci taji yace "Just to interrupt my sleep?" da wata irin murya mai kaushi yay Maganar, shiru tayi tana kyakkyafta ido, jin bata amsa mashi ba yasa ya d'ago kan ya kalleta, ganin kallon da yake matanne yasa ta matsa zuwa gefen kujerun ta tsugunna, yar sheshsheka ta fara yi kafin ta fara magana,
" Ya Handsome da..dama..don Allah zuwa nayi in rok'eka ka kyaleni in rink'a yin azumi kwana daidaya, wllh jiya kusan mutuwa nayi ko islamiyya ma banje ba saboda ban iyawa a d'akin Aunty Saude na wuni lokacin da aka sha ruwa kuma har amai nayi" ta k'arasa cikin karewar murya tana goge kwalla da hijab dinta,
Sigh yay ya d'an gyara zamanshi kaman bazaice mata komai ba idonshi akanta tana ta nannok'e kai,

"Kinsha ruwan da yawa next time sai kisha kad'an, ko ki fara shan something warm in zaki iya and karki k'ara zama baki je skul ba saboda kina fasting " ya fad'a bayan ya daidaita temper dinshi, d'agowa tayi ta kalleshi still tana murzar ido cikin marairaicewa tace "to zan rink'a yin hakan kuma bazan kara kin zuwa islamiyyar ba amman in rinka yin d'ayan?" girgiza mata kai yay ba alamun wasa tana niyyar k'ara magana ya dakatar da ita da hannunshi yace "Zarah kije karki late" tana jin hakan ta mik'e tana k'ara sautin kukan da take, shiru yay yana bin ta da ido lokaci guda yaji wani abu ya fara ratsa zuciyarshi mai kaman tausayi dama Haisam baison yaga mutum yana kuka don shi Mutum ne mai tausayi sosae ba kaman ita da ta kasance mace kuma ma yarinya saidae bazai iya yi mata yadda take so ba don alamu sun nuna inba hakan aka yi mata ba to bazata ta6a sabawa da azumin ba,

"Zaraah" taji ya kirata lokacin har ta kama handle d'in kopar zata bud'e, da muryar kuka ta amsa tace "Na'aaam",
" wait let me drop u" daga haka ya mik'e ya nufi bedroom dinshi, bai jima ba ya fito hannunshi ruk'e da Car key batare da ya cire sleeping dress d'inba, tana ganin ya fito ta juya ta fita, bayan sun fita daga gidan amota ya tambayeta inda Islamiyyar take ta fara kwatanta mashi, ba tare da sun d'au wani dogon lokaci ba suka k'arasa, tanata faman cin magani tace mashi ta gode kaman anyi mata dole, d'an Murmushin da bai bayyana kan fuskarshi ba yay a fili kuma sai ya tambayeta k'arfe nawa suke tashi baki kumbure tace 11:00 daga haka ta bud'e kopar Motar ta fice, lokacin da taje aji ta makara amman saboda azumi ake yasa ba'ayi mata komae ba, koda taje ta zauna bin ta da ido Haulatu tayi ganin yanayinta, bayan malamin dake ajin ya fitane ta tambayeta mike damunta kaman bazata fad'i mata ba, can da haulatun ta matsa matane ta fadi mata yadda Ya Handsome yasata yin azumin dole duk da bai zamar mata dole ba da kuma irin wuyar da tasha jiya ta k'arasa kwalla na zubo mata tana sa bayan hannunta tana gogewa, ita dae haulatu jinjina kai kawae tayi tace tayi hakuri amman acan k'asan zuciyarta ta masifar jin dad'in hakan don ita kanta ba k'aramin fama take da Fatun ba akan ta daure ta rink'a kai azumi amman sai tace ana wannan uwar ranar zatayi azumi bacin bai zamar mata dole ba wllh batayi don dama sam bata da jumurin yunwa in har kaga bataci abinci ba kuma tana jin yunwa saboda wani dalili to kuwa babban daliline, har aka tashi tana ta bak'in rai don har ta fara complain din yunwa ita dae Haulat d'an Murmushi kawae take, suna fitowa daga cikin islamiyyar ta hangi Motar Haisam, da farko tsaye tayi tana kallon bayan motar kaman bazata je ba saidai tsoronshi da take bazai bari tayi hakan ba kuma ko ba wannan bama tana buk'atar shiga motar don rana ta bud'e sosae, kallon Haulat tayi tace mata suje ga Ya Handsome can yazo daukarta, nufar Motar sukayi Haulat nata jinjina kirki irin na Haisam acikin ranta lokacin da suka k'arasa bakin motar baya haulat ta bud'e ta shiga haka itama fatun sa6anin d'azun da zai kawota agaba ta zauna don tasan baison ba kowa a agaba a zauna baya, yana sanye da Jallabiya fara sol ga d'an kamshi mai sanyi ba mai hawa kai ba na tashi had'i da ni'imtaccen sanyin Ac, suna zaunawa Haulat ta gaidashi tace mashi ya ibada ya amsa da Alhamdulillah ba tare daya kallesu ba daga haka ya tashi Motar Fatuu batace mashi komae ba, lokacin da suka zo center d'in gidansu tana ganin zai nufi gidansu tana tura baki tace gidan Hajiya zasu hakan yasa ya nufi can, bayan yayi parking d'in Motar a Parking Space Haulat tayi mashi godiya ya jinjina mata kai ganin fatun bata yi ba yasa ta d'an zungureta amman sai ta kalleta ta tura mata baki hakan yasa ta bud'e motar ta fita, tana shirin fita itama kamar ance ta d'aga kanta suka had'a ido ta cikin madubin gaban motar, ganin kallon da yay mata ne yasa da sauri tace "An gode" banza yai mata saima ya bud'e motar ya fita bayan ya rufe kopar ya nufi part d'insa, Haulat dake atsaye tana jiran Fatuu tabi shi da ido Allah kadae yasan mi take ayyanawa aranta,

Jin Fatun ta fito ne yasa ta maida kallonta kanta fuska ad'an daure tace "Wllh Fatuu baki san baki san mutunci ba, yanzun mutumin nan yaje har islamiyya ya d'aukko mu amman shine bazaki iya ce mashi angode ba sai ma wani tura baki kike ke ala dole yayi maki laifi daga abun arziki wanda inma kinyi ke zai amfana bashi ba",

" to ba nace mashi ba yay banza dani" ta fad'a tana d'an hararar Haulatun,
" To shi tsaranki ne ko ko ajeshi kikai da sai kingadama zaki ce mashin, kuma dayake tsoronki yakeji sai ya amsa ko" a tsiwace tace "dalla ni ki k'yale ni, Mutum na azumi ki wani cika shi da Surutu" daga haka ta nufi part d'in Hajiya, d'an girgiza kai Haulat tayi cikin ranta ta ayyana samun wuri, a fili kuma da d'an d'aga murya yadda Fatun zataji ta furta "Don kin samu yana kulaki ne ai, amman bari kija ma kanki bake kika sani ba" daga haka tabi bayanta,
Chapter 90 · 0% Book details