← Book details Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 137

Sashe 55

Asanadin Makwabtaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wani zaka kawo ma
computers ne? Abbas ya tambaya,
"yeah,wani company ne a lagos suka ban contract zan je nayi masu aiki but sai kayan sun iso"haisam ya bashi amsa,
"Allah ya kawo su lafiya,ya bada sa'a,kaga ba don mun koma aiki ba ai danayi rakiya"

d'an murmushi haisam yayi yace"ai in zanje zan bi flight d'in yamma ne ran friday,inason yin komae within weekend zuwa Monday sai in dawo,kagan just rana d'aya ne bazaka aikin ba" Abbas yace"alright sir,zan dauki excuse,Allah ya kaimu"

"Ameen" ya amsa,daga haka Abbas ya fara kokarin mikewa"bari na wuce Zakee inason zan biya round din Gra ne,Allah ya baka lpy ya kiyaye gaba"
mik'ewa haisam yayi,Abbas na fad'in ya bar rakiyar yace ba matsala ai yasamu sauki sosae suje ya rakashi wajen,suna fitowa waje inda yayi parking motarshi ya tuna da wata magana da yake son yi ma Haisam d'in hakan yasa suka haye saman boot d'in Motar suka zauna don suyi maganar,suna cikin tattaunawa kamar ance haisam ya waiga gefensa ya hango Fatuu na tahowa daga bayansu dayake Motar Abbas din gab da shiga kwanar gate din ya parker ta, bata shiga cikin lungun gate d'in ba,underneath his breath yace"here she comes"kallonshi Abbas yayi"wa?"haisam bai kaiga bashi amsa ba ta zagayo inda suke hannunta ruke da bokitin ruwa,jikinta na sanye da riga da skirt na atampa yayin da ta yafa d'an gyalenta na gado saman kai,kitsonta sun zuba gaban kan,har lokacin ba'a idasa kitson ba don daga baya gashin a fake yake yayi tum,aje bokitin tayi a gabansu ta zuba ma Abbas ido shima bin ta yayi da ido yana kallonta.

*💖A SANADIN MAKWABTAKA💖*
_*(Love and Destiny)*_

_*BY ZAINAB LALUH📲*_

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

*4️⃣1️⃣*

A hankali ta fara matsawa kusa da Haisam,a gefenshi ta tsaya,kasa kasa da murya tace"Ya handsome bak'o kayi?"kafin ya bata amsa Abbas ya rigashi"ba bak'o bane dan'uwansa ne Mom zarah"waro ido tayi baki bud'e take kallonshi,mamaki ne ya kamata jin yace mata Mom zaraah,nufo inda yake tayi ta tsaya agabanshi tace"kenan Yaya Handsome ya baka labarina?"kai ya d'aga mata"Eh yace wai munyi sabuwar Mom",tafin hannuwanta tasa ta rufe baki tana dariya alamar mamaki,

"To kai ma sunan mamanka gare ni ne?fatuu ta tambaya bayan ta cire hannun,
"Ba kiji nace ni dan'uwansa bane,ai Mom dinmu daya..." tun kafin ya rufe baki ta fara jefa masa wani kallo irin ban yarda ba d'in nan,
"kenan kana nufin kaima Senator babanka ne?"cike da tuhuma tayi tambayar,kai ya daga mata alamar eh,

Juyawa tayi ta kalli Haisam daya sadda kai yana latsa waya kafin ta juyo tana kallon Abbas wanda ya d'an k'ankance ido fuskarsa d'auke da Murmushi yana d'an girgiza kai,ganin hakan yasa ta buga kafa cike da shagwa6a tace"Wllh ban yarda ba,kamm yo ya zanga wake da shinkafa amman kace man wai gidanku d'aya",Sosae Abbas ke 6a66aka dariya jin abunda tace,tsagaitawa yayi"waye wake waye shinkafar"tana turo baki tace"yo kai da kake baki ai kaine waken shi kuma da yake fari shine shinkafar",

"To ai ni Senator na biyo shi kuma sai ya biyo Mom dinmu, ko baki ta6a ganin senator din bane?" shiru tayi tana kallonshi still bata yarda ba"to amman ni ai shi kadai nasani anan,kuma shima baice man yana da wani dan'uwa ba anan,kuma ko gwaggota da hajiya ma basu fad'i man ba",

"To k'ilan dae bakuyi Maganar da zasu sanar dake hakan bane,amman ni dan'uwansa ne Uwarmu daya Ubanmu daya" ya k'arasa yanata Murmushi,kallonshi kawae take ba don ta yarda ba,ganin yanata faman zabga murmushi yasa ta fara bubbuga k'afa tana jujjuya kai sai kace wata yar k'aramar yarinya,murya kaman zatayi kuka tace"bafa kyau k'arya kuma kai babba ne kasani,don Allah ka fad'i man kai waye"a marairaice tayi maganar,karfin halinta ba k'aramin Dariya yake ba Abbas ba,ganin tana ta masa magiya yace"Owk,bari in fad'i maki gaskiya to daman wasa nike maki,ni Amininsa ne tare mukayi Senior Secondary anan garin amman yanzu mu mun wuce abokai yan'uwa ne"washe baki tayi"daman nasan ba gaskiya kake fad'a man ba,kenan kaima kaman Haulatu ne",
"Wacece haka?Abbas ya tambaya,
"nima Aminiya tace yanzu haka makarantarmu d'aya da ita kaman yayata take" jinjina kai yayi,
taci gaba"muna ta yin anko da Yaya Handsome,kaga shima awurin kakarshi yake nima haka,sannan yana da Amini nima ina da Aminiya"ta kai maganar tana ta dariya duk dimples dinta sun lotsa,shima dariyar yake mata,

"To kai ya sunanka?"
"Sunana Abbas", jinjina kai tayi ta kuma cewa"A nan garin kake?" kai ya daga mata alamar eh,
"To ina ne gidanku?"

"Gidana dae,a Fatima shema Estate nike,kinsan wurin ko?",
"Ina dae jin sunan amman ban ta6a zuwa ba,ka ce anan gidanka yake,kana da aure ne?"
Kai ya d'aga"ina da Aure sunan matata Nafeesat kuma inada yaro guda d'aya sunanshi Abdul"hannu fatuu tasa ta ruke ha6a alamar mamaki,a hankali ta juya ta kalli haisam wanda har lokacin kanshi na k'asa yana latsa waya tamkar bai jin ma abunda suke tattaunawa,
D'an matsawa tayi kusa da Abbas kasa kasa da murya tace"to ya akai shi bai yi auren ba?" Abbas na niyyar bata amsa haisam ya d'ago fuska a d'an d'aure yace"Zaraah!"a firgice ta juya ta kalleshi,"ba aiken ki akai ba?"da sauri ta kai hannu ta d'auki bokitin ruwan ta juya zata tafi,Abbas dake guntse dariya yace"Ah Mom ya haka kuma d'anki ne fa shi ai ke yakamata ki bashi umarni ko"juyowa tayi tana mashi wani kallo"da ya baka labarina bai gaya maka akwae yarjejiniyar gidan yari tsakaninmu ba"daga haka tayi gaba,Abbas kau dariya yasa harda dafe ciki,ganin yadda ruwan keta zubowa yana jik'a mata k'asan skirt yasa shi d'aga murya"Mom ki d'aura saman kai mana"bata juyo ba hannu tasa tana nuna mashi tudun gashinta dake afake alamar bazai bari ta d'aura ruwan akan ba,

K'ara daga murya yayi"to Mom zaraah sai yaushe zamu kara had'uwa mu gaisa",d'an juyowa tayi ganin haisam d'in ya maida kan k'asa yasata dakatawa ta aje ruwan"yaushe zaka k'ara dawowa?"ta tambayeshi,
"Kowane lokaci,ina yawan zuwa ai",
"To kaga wannan gidan mai kiosk shine gidanmu,idan kazo kana son ka ganni nan zaka zo,kace a kira maka Fatuu,in kuma ba wanda zaka aika ka shigo ciki kawae,in kaga gwaggota sai kace mata kai Abokin Yaya Handsome ne wurina kazo...." tana ganin haisam yana niyyar d'agowa ta kai hannu da sauri ta d'auki bucket din ta juya,

Sosae Abbas keta dariya don maganar tata dariya ta bashi wai in bai samu wanda zai aika ba ya shigo kawae yace ita yake nema sai kace wani zararre,kallon haisam yayi wanda ya d'ago yana kallonshi don duk maganganun da suke yana jinsu dama shima Abbas din bakinshi sake yake,d'an ta6e baki yayi yana girgiza kai,Abbas yace"yo kai H,zakee ashe Mom d'in naka kwarkwar ce"gaba daya suka sa dariya,

Bayan ya tsagaita da yin dariyar yace"let me take my leave zakee,magrib ma ya kusa",atare suka saukko daga kan boot d'in,Abbas ya zagaya side din driver shi kuma haisam ya tsaya a other side d'in,
"Gaskia Abbas kaci mota,motan ya tsufa,wai a haka yan matan naka suke shiga?" Har Abbas ya kai hannu zai bude kopar motan ya dakata"yo kar yarinya ta shiga in akwae kamarta a gidansu"fuskarsa d'auke da murmushi yayi maganar,

"I thought so,sai dae babun"haisam ya fad'a da murmushi daga haka Abbas ya bud'e motar ya shige suka sake yin sallama yaja Motar bayan ya tafi haisam ya juya ya koma gida.

_____________________

Washegari Juma'a,misalin karfe 11 na safe Hajiya ta kira gwaggo tace mata in Fateema ta dawo daga Makaranta tazo zasu je Unguwa,cike da girmamawa Gwaggo ta amsa mata da toh.

Bayan sallan Juma'a,Hajiya zaune ita da Haisam saman Dining suna cin lunch,Haisam yasha shadda gizner Ash colour hannunsa sanye da wani hadaddan Diamond watch,kafarsa sanye cikin dakakkun takalma na zallar fata suma Ash,Hajjaju ma ansha atamfa babbar Holland kunnanta sanye da yan kunnan zinari harda sark'arsu da zobuna tayi d'aurin kallabi irin nasu na dattawa,kamshi ne kawae ke tashi daga jikinsu,

Bakinta d'auke da sallama ta shigo,gaba daya suka juya suna kallon entry d'in,tana hango su a Dining area ta nufi can,har ta isa idanunsu na a kanta,
"Tubarkallah,maa sha Allah,wannan kwalliya haka Fateema,kice saboda kinci gayu yasa yau ba ayi man irin sallamar da aka saba ba" Cike da jin kunya tasa tafin hannuwanta ta rufe fuska tana dariya,sanye take da riga da skirt na lace brown mai d'auke da kwalliyan fulawoyi Coffee brown,ta yafa gyale coffee yau Allah ya yi ta canza gyale, kafafunta na sanye da takalma masu tudu bak'ake hannunta ruke da yar k'aramar bak'ar jaka,yayin da wuyanta ke sanye da sarka mai kyau da yan kunnanta harda yan hannu,tayi kwalliya harda jan baki maroon,haka kitsonta an ida mata shi ta zubo shi ta gaba har ya wuce kirjinta,cikin kayanta ne na sallan bara tasa,ta Matuk'ar yin kyau,kalan lace din ya hau da fatar jikinta sosae,ganin tana ta tsayuwa Hajiya tace"Zo ki zauna kema kici abincin"cire tafukan tayi daga kan fuskan ta k'arasa wurin table d'in,dama saboda zumudin zasu fita unguwa ita da hajiya lokacin da gwaggo ta sanar da ita yasa ta kasa zama taci abinci,kujera taja ta zauna idonta akan haisam dake cin Abinci a nutse,Saude hajiya ta fara kwala ma kira don tazo tayi serving fatun,A hankali haisam ya cira kai ya kalli side d'in da take,suna had'a ido ta sakar mashi murmushi"Yaya handsome ina wuni"jinjina mata kai kawae yayi don akwae abinci a bakinshi,daga haka ya maido idanunshi kan Abincin,
Chapter 55 · 0% Book details