← Book details Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 58

Sashe 8

Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 13...... Haiydar yyi murmushi yana kallon cikin idonta yace "to bude baki na sa maki plantain sai ki wuce," ta fara waige-waige a tsorace tana kkrin barin jikin fridge din don dab da ita yake har tana iya jin breathin dinsa a fuskarta, yyi saurin sa hannu ya tokare hanyar da xata bi, ta marairaice murya kmr xata yi kuka tace "A'a ni na koshi," yace "ashe dae baxa ki bar nn ba yarinya," ganin da gske yake yasa ta bude bakin a hankali yana kallon kwayar idonta ya saka mata plantain din a baki, ta shiga taunawa a hankali yana mata wani irin kallo, ya matsar da ita daga jikin fridge din, ta fixge hannunta da sauri xata bar wajen, ya maxa ya rikota yace "baki isa ba tukun," ya na rike da ita ya bude fridge din ya dauko chill hollandia yoghurt, snn ya maidota jikin fridge din ya jinginar, ya bude drink din ya xuba cikin glass cup, ya kai mata baki, ta kauda kai da sauri ya hade rai yace "Allah baxa ki bar nn ba idan baki sha ba" kuka ta dinga yi tana rokansa ya kyaleta ta wuce, amma yaki sakinta wae sae ta sha hollandian, ganin ba sarki sae Allah ne yasa ta bude bakin a hankali ya shiga bata drink din tana sha, muryar Hajiya suka ji daga sama tana cewa " wae Aliyu ya fita ne meenah," a tsorace Aneesah ta turasa ta durkushewa wajen tace "nashiga uku na lalace," shi kuma yyi saurin juyawa ya koma dinnin ya xauna, dae-dae nn Hajiyar ta karasa saukowa da meenah, idonta ya sauka kan Aneesah da har lkcn ta kasa mikewa tsaye daga wajen, cikin tsawa tace "ita kuma warcan me take min jikin fridge hka," Haydar yyi saurin cewa "No ni nace ta bude ta kawo min drink, tace "Ayyo" snn ta karaso dinning din ta xauna tana cewa "har yanxu baka gama cin abincin ba son," Aneesah ta dauko hollandian da ya ajiye mata gabanta duk ta rude tama rasa abun yi ta hado da cup din ta dan risina ta ajiye masa gabansa kan dinin table din ya kashe mata ido ya bita da kallo ta bar wajen da sauri har tana tuntube. Ranar cikin rashin kuzari ta isa gida ta xube kan katifa, Ammi ta tambayeta lfya, tace kawae kanta ne ke ciwo, Ammi ta bata magani bayan ta sa ta gaba taci tuwon da tayi masu, snn taje tayi wanka tayi sallah ta koya ma yusuf assignment dinsa, ta danyi karatun qura'ani har karfe takwas, snn tayi sallahn isha tayi ma Ammi sae da safe ta kwanta duk da ba bacci take ji ba, kawae abun duniya ne ya isheta, ita kam duk aikin ma ya gama sare mata xuwan Haiydar, su dinga dabi'a irin ta nasara kmr wa inda basu da ilimin addini, ita a al'adarsu ta hausa fulani bata ga namiji na taba macen da ba muharramarsa bace, gskya ta kara tabbatar da cewar gidan nn basu da tarbiya, in Allah ya yarda aikinta ya kusan xuwa karshe a gidan, xata sa Ammi ta samo mata wani wajen daban da xata dinga aiki, baxata je ya cuceta a bnxa ba don bae mata kama da mai kamun kai ba. Hka Aneesah ta dinga aiki a takure a gidan, don Hydar duk ya bi ya sa ta gaba, indae yana gidan to bata da kwanciyar hankali don kawae sae dai taji mutum tsaye a bayanta, in tana garden to shima yana can, shi dae kawae so yake yaji lbrinta wae bata yi kama da 'yar aiki ba, kuma yasan tana da ilimi both, sau dayawa ya kan mata turanci don ta maida masa, amma ko sau daya bata taba mayar masa ba, sae dae ma tayi kmr bata ji mai yace ba, da ya kawo mata xancen yana son sanin ko ita wacece sae tace masa ba matsalarsa bace wnn, in kuma ta tashi serve dinsa abinci to sae ya tilasta mata ta ci abincin da ta xuba mashi, duk ya bi ya tsorata ta a gidan kuma duk wnn abun da suke ko sau daya Hajiya bata taba lura ba, hka ma yan matan gaba daya, yau ma kmr kullum tana xaune garden tayi xurfi cikin tunaninta bayan ta gama duk aikin da xata yi a gidan, ita kam kila yau ce rana ta karshe da xata kara aiki a gidan, don bata ga dalilin da Haiydar xae takura mata a kan sae yasan ko ita wacece ba, ga abun Hajiya sae gaba yake karawa ta rasa abinda tayi masu ba ita ba ba 'ya yanta ba, in ta tashi tafiya yau kawae ce mata xatayi ta bar aiki, ta gaya mata ranar da xata xo ta karbi kudun aikinta na rabin watan da tayi, idan kuma tace baxata bata ba, shkkn ta bar masu, tayi tagumi tana kallon tsuntsaye tana tunanin ko shawarar da ta yanke yyi taji hannun mutum a wuyanta, ta juya a fusace ta dan matsa cikin fada ta fara magana "wae meye hka malam, bana son iskanci ka rabu dani nasha gaya mka ni ba 'yar iska bace," ta mike ta shige kitchen ya bi ta da kallo, ko da ta shiga gidan ta tarar su Hajiya sunyi shiri xasu fita, tana cikin goge masu takalman da xasu sa ya shigo falon, fuskarsa a daure ya xauna kan kujera Hajiya ta shiga tambayarsa me yafaru bai tanka mata ba, tace "xamu fita son amma ni ba dde wa xanyi ba ynxu xan dawo," ya gyada mata kai kawae yana kallon Aneesah da gabanta ya shiga bugu da sauri, suna fita kuwa ita ma xata bar gidan tana gani, ya hade rai yace "ya ma kike da suna" ta juya tana kallonsa tace "Ni," hajiya ta haureta tace "to da uwarki ce idan ba ke ba" a hankali tana hawaye tace "Aneesah," yace "gud, bedroom dina xaki gyara min idan kin sallamesu [9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 15..... Aneesah tayi shiru tana kallonsa ta kasa cewa komai, ya gyada mata kai yace "am ol ears," ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Abbana ya rasu, Ammi ta ce kawae sae kanina yusuf" sae ga wani sabon hawayen tana yi, ya girgixa mata kai yace "a'a bance kiyi min kuka ba Aneesah," ya sa handkerchief ya goge mata fuskar snn yace "go on momyna" ta sunkuyar da kanta a hankali ta fara basa lbrin rayuwarsu tun daga rasuwar abbanta har ixuwa ynxu da yake xaune kusa da ita, tayi kuka sosai kmr ranta xae fita, ya xuba mata ido yana kallonta ya kasa cewa komai, ta goge fuskarta ta mike xata bar dakin ya kamo hannunta ya maido da ita ya xaunar, a hankali cikin nutsuwa ya fara magana "shi baffan naku a wani anguwan yake, snn relatives dinku mae suka ce dangane da abinda yyi, kuma wish din Abbanku knn ya rike maku gadon ku har ku mallaki hankalinku ko tsarinsa ne, snn me abokanan abbanku suka ce game da hkn, Abbanku na da lauya ko bae da??" Aneesah tayi murmushin da bata shirya ba xata yi magana suka ji muryar Hajiya downstairs, ta mike a tsorace tana kallon agogo, karfe uku har ya wuce, tace "nashiga uku na lalace," ya mike da sauri ya koma kan kujera yace ta cire bedshit din, jikinta na rawa ta cire bedshit din, dae-dae nn Hajiyar ta shigo dakin tana kallonta da mamaki cikin tsawa tace "ynxu shegiyar yarinyar nn baki girka abinda nace maki ba, gyaran dakin ne tun daxu," Aneesah ta fara kame kame a tsorace xata yi magana Aliyu ya riga ta "A'a aikenta nayi mum, bata dde da shigowa ba nace ta wanke min bathroom kafin ta gyara dakin," Hajiyar tace "Ayyo," snn ta galla mata harara ta ja kujera ta xauna tana kallon Haiydar din da damuwa tace "wae son ya maganar companies din Abbanku na lagos ne, kasan fa mutane basu da tsoran Allah tun da mahaifinku ya rasu Haiydar sau biyu ka waiwaye lagos," cikin fada ya fara mgana yana kallonta "to wae mum so kuke na kasa kai na ne, meye hadin barrister da wani bussiness can, ni ynxu cases din dake gabana ma sun fi karfina, su Amina da sumayya uban me suke yi ba abinda suka karanta ba knn, sun gwammace su yi ta gantali a garin Abuja," ya jawo laptop dinsa ya kunna ba tare da ya kara kallonta ba, tace "to kayi hkuri kuma fa gskya ne," Aneesah ta gama gyara gadon ta fita ta bar masu dakin tayi hanyar kitchen daura girkin da aka sa ta. Karfe shidda ta dauki hijab dinta tasa xata tafi gida, ta durkusa gaban Hajiya gabanta na faduwa ta dai yi shahada tace "Hajiya ina son ajiye aiki daga yau, idan yaso sae ki gaya min randa xan xo karban kudi na na rabin watan da nayi aiki," Hajiyar ta shiga mata wani irin kallo snn tace "gidan uban wa xaki da xaki ajiye aiki," ta girgixa kai a hankali tace "ba inda xani," cikin tsawa Hajiyar tace "baki isa ba to muguwa, a gidan uwarki ake hka, kinsan xaki tafi tun da can baki gaya min ba na samo wata sae ynxu da rana tsaka, kuma wllh baki karasa min aikin wnn watan gaba daya ba baxan baki kudin rabin watan ba, snn sae kin tsaya har an samo min wata yar aikin idan ba hka ba in na maki Allah ya isa sae ya biki wllh, tunda ban san ubanda xai dinga min aiki ba idan kika tafi bbu wata," a hankali tace "to xan jira ki samo wata 'yar aikin," Hajiyar tace "oho dae ya rage naki muguwa kawae" jikinta a sanyaye ta fita daga gidan, ta tarda Haiydar bakin gate a waje yana tsaye da alamar ita yake jira, ya karaso kusa da ita yace "lemme drop yhu," ta hade rai tace "A'a ngd" ya harareta yace "baki isa ba," tace "Allah bana so" bata sake jiran me xe ce ba ta kama hanyar gida da sauri da sauri. Tana isa gida tayi wanka tayi sallah ita da Amminta da yusuf, suna cikin cin abinci karfe kusan
Chapter 8 · 0% Book details