Sashe 44
Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kam, bbu wanda ya lura da halin da take ciki kowa da abinda yake cewa, banda Mujaheed dake murmushi kawae, ta bude idonta a hankali ta daura kan Mujaheed dake tsaye gefen gadon, shi din ma kallonta yake yi, suna hada ido ya dauke kansa da sauri, taji wani hawaye mai xafi na bin kuncinta ta girgixa kai tayi hanyar fita daga dakin da sauri, Mujaheed ya bi ta da kallo abun tausayi, Abdul dake kallonsu shima yaji wani iri, suna hada ido da Mujaheed, ya dauke kansa ya karasa kusa da gadon da Hydar yake kwance, ana surutu amma Hydar shiru sae ido da ya xuba masu, da dan damuwa Najeeb yace "A'a wae ya dae ku kira likita naga yaki magana," ganin Hydar yaki ce masu komai sae kallonsu da yake har lkcn yasa Abdul ya karaso kusa da gadon yana kallonsa yace "ya? Kana jin mu kuwa Hydar," Hydar ya sauke ajiyar xuciya yace "ina jinku," snn ya fara kkrin sauka daga kan gadon, Abdul ya rikesa yace "ina kuma xaka," ya dan yatsine fuska yace "4 hw lng nake nn kwance" Najeeb yace "u've been here 4 d past three dayz, sae yau da Aneesah ta xama mallakinka don gulma ka farfado har da ana shirin fita da kai egypt," Hydar yyi shiru yana kallonsa, a hankali cikin wani yanayi me kama da confusion yace "Aneesah" Najeeb yace "yes," Hydar ya dafe kansa na kusan minti biyar snn ya dago yana kallon Mujaheed, Mujaheed bae bari sun hada ido ba, Hydar ya fara kkrin mikewa tsaye ya koma da sauri ta dalilin wani jiri da ya gani, Abdul yace "ya dae," ya koma ya kwanta da ganinsa kasan bae da karfi a hankali yace "baxan iya tashi ba," Mujaheed yace "bari a kira doctor to," ya juya ya fita, Hydar na kallon Najeeb yace "ku gaya min gskya don Allah da gske ne abinda kuke gaya min," Najeeb yace "gskya ne Hydar Aneesah matarka ta sunna ce ynxu," Hydar ya girgixa kai cike da takaici yace "meyasa xakuyi hka, meyasa kuka yi ma Mujaheed hka, bani take so ba shi take so," faruuq yace "Aneesah na sonka dan uwa ka kwantar da hankalinka, hka Allah ya so," Aneesah na fita haraban asibiti taci karo da Hajiya, a rude Hajiya tace "meye kike kuka Aneesah me ya faru kuma" cikin kuka Aneesah tace "wae mumy da gske ya Hydar mijina ne ynxu," Hajiya ta rungumota tace "to meye abun kuka Aneesah ko ba kya son sa ne," cikin kuka ssae tace "ba sona yake ba mumy, don Allah ku taimakeni," da mamaki Hajiya tace "wa yace maki hka Aneesah, ae duk duniya a yanda na lura bbu wanda Hydar yake so bayan ubansa kmr ke," Hajiya ta ja ta suka isa gun mota takira driver ba a jima ba ya xo tace ya kai su gida, har suka isa gida Aneesah bata daina kuka ba, suna fitowa daga mota Aneesah ta tuna lst tym din da ta bar gidan, Hajiyar ta ja ta suka shiga ciki mutanen dake cikin gidan na ta tambayarta ko Aneesah ce amaryar, ta dae yi murmushi tayi masu sannu da gida suka wuce sama da Aneesah ta kai ta dakinta ta xaunar da ita kan gado, ynxu kam Aneesah ta daina kukan da take yi sae na xuciya, Hajiya ta dago kanta tana kallonta tace "kiyi hkuri Aneesah amma don me kika yi tunanin Hydar baya sonki, sbda ke fa ya shiga halin da yake ynxu, shi yace maki baya son ki" Aneesah ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, nn Hajiya ta dinga bata baki tana mata 'yan nasihohi ita dae bata ce komai ba sae hawayen da take, tana dakin hajiya ita kadae bayan sllhn isha tana jujjuya lafiyayyan abincin dake gabanta Wasu mata biyu suka shigo dakin, dayar tace "amaryarmu baki ci abincin bane," Aneesah ta sunkuyar da kanta tace "na ci," matar tace "to sako hijabinki ki fito ana jiranki a waje xaku wuce gida," bata yi musu ba ta sa Hajib ta bi su a baya, ta shiga motar da aka nuna mata, matar ma ta shiga snn driver ya ja motar suka bar gidan, dae dae kofar gidansu drivern ya tsaya suka fito ita da matar suka shiga gidansu, Ammi na xaune daki da wasu 'yan uwanta har uku da makwabta, Aneesah ta fada kan Amminta tana kuka ssae Ammi ta dagota tace "meye hka Aneesah," daya daga makwabtansu ta dagota ta fita da ita daga dakin ta shiga da ita gidanta, ranar Aneesah bata yi baccin kirki ba bayan matar tayi ta mata nasiha ssae game da xamantakewar aure, ita dae jinta kawae take amma ta kasa gaskata wae ynxu ita matar Hydar ce, washegari da safe matar tasa Aneesah ta shirya bayan ta aika yarinyarta ta karbo mata kaya a gida, da kyar ta daure tayi break din da matar ta hada mata, karfe goma saura suka shiga gida gun Ammi har lkcn da mutane cikin gidan nasu, Ammi ta kasa ce ma Aneesah komai sae matan dake dakin ne suka shiga bata baki da yi mata Nasiha, ashe abinda bata sani ba shine ranar xata bar gidansu ta tare gidan mijinta. 9 mins · Khaleesat Haiydar... [12/8, 21:13] +234 803 751 8717: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 115... Aneesah ta rasa me ke mata ddi a duniya, ita dae kawae jin abinda ake ce mata take amma bata fahmtar kmai, daga karshe aka dauki sadakinta dubu dari aka mika mata, daga baya xa a kai mta kayan daki dk da hjya tce su bari, ta fashe da kuka tana girgxa kai tana kalln kudin tce ni bana so abn ya ba mutann dake dakin dariya, wata mata tce naki ne wnn Aneesah, Aneesah ta girgixa kai tce na ba Ammina, matan dakin suka yi dariya snn wata tace Ammi dae xata rike maki, amma hakkin ki ne wnn," da kyar Aneesah tabi matar da suka xo jiya da wasu daga 'yan uwan abbanta guda uku suka fita daga gidan tana kuka ssae, duk daurewan Ammi sae da tayi hawaye, gani take kmr ta xalunce Aneesah ta yanke hukunci ita da yan uwanta ba tare da saninta ba, duk da tasan ya cancanci ta ba Hydar Aneesah, don yyi masu abinda 'yan uwansu na jini suka kasa masu a rayuwa, a yanda ta lura kmr Mujaheed take so ba Hydar ba, tausayin 'yar tata ya cikata. Karfe sha biyu suka isa gidansu Hydar, Aneesah ta fito daga mota a sanyaye wata na rike da hannunta suka shiga cikin gidan, mutane ne dayawa cikin falon, hkn yasa matar ta rungumota suka haura sama ta shiga da ita dakin Hajiya, Hajiya ta rungumeta cike da farin ciki ta xaunar da ita kan gado tanai masu sannu da xuwa, mutane nata shigowa ganin amaryar, wata daga kawar Hajiya tace "to Hajiya yaushe ne bikin," Hajiya tace "idan mijin nata yaji sauki ssae" duk suka dinga mata Allah sanya Alkhairi suna yaba kyan Aneesah da kunyarta don takurewa tayi guri daya, karfe biyar saura mutanen dake gidan suka fara raguwa, dakin ya rage daga Aneesah sae wasu mata biyu, aka turo kofan dakin pretty da Ameera suka shigo, Ameera ta sakar ma Aneesah murmushi, pretty kam bata ko kalleta ba ta karaso gabanta tace "sannu amaryarmu," snn ta ajiye farantin dake hannunta, tace "mu je Ameera," Ameera tace "mun gaishe da amaryarmu me kyau sae mun shigo anjima," suka juya suka bar dakin Aneesah ta bisu da kallo a sanyaye, hawayen da take son ji a idonta ma ta neme shi ta rasa, matan dake dakin suka ce ta sauka ta xuba abinci ta ci, bata yi masu musu ba ta xamo kasa daga kan gadon, duk da na daxu ma da aka kawo mata bata cinye ba. Bayan magrib Hajiya tasa ta shirya su kai ma Hydar abinci asibiti, ta shirya cikin wani material mae shegen kyau, ta sa Hajib dinta har kasa, bata yi wani make up ba, driver ya wuce da ita da kanwar Hajiya xuwa asibiti, a sanyaye gabanta na faduwa ta dinga bin matar da taji ake cema Anty farida xuwa ward din da Hydar yake, faridar ta riga ta shiga cikin dakin, ta shigo ita ma da sallamarta murya can kasa kasa, yana kwance amma idonsa biyu, ya rame ssae ba kadan ba, najeeb da wasu abokansa biyu na xaune cikin dakin, suna ganin Aneesah suka fara tsokanarta suna dariya, hkn yasa taji kmr ta fasa ihu ta saka masu kuka, hawaye ya cika idonta amma bata bari kowa ya lura ba,hydar kam dauke kansa yyi bayan ya gaida Anty farida dake ta dariya tana biye masu ta hanyr kare ma Aneesah, su ma bakinsu bae mutu ba su ka dai gama haukansu suka bar dakin suna dariya, Anty farida tace "da ku tsaya mana" sae a snn ta kalle Aneesah dake tsaye tace "A'a amaryarmu baki xauna ba," Aneesah ta kirkiro murmushi ta ja kujera ta xauna, Anty farida ta mike tsaye tace bari xan je siyo kati na dawo, tana fadin hka ta fice dakin ya rage daga Aneesah sae Hydar, ganin sun kai minti kusan biyar a hka yasa ta daure da kyar muryarta na rawa tace "ya jikin," sae da ya dan yi shiru snn taji yace "da sauki," ta daga kai tana kallonsa taga kallonta yake, ta sunkuyar da kanta da sauri tace "in xuba maka abincin?" ya girgixa mata kai yace "aa sae dae in ke xaki ci ki xuba," tayi shiru bata sake cewa komai ba, shima hka, kowa da tunanin da yake yi a xuciyarsa, a hankali taji yace "dan bani ruwan can," ta mike ta dauki ruwan ta bude ta dan dauraye kofin snn ta xuba masa ta karasa kusa da gadon tana mika masa, ganin bae karba ba yasa ta daga kai tana kallonsa ya sauke idonsa da sauri daga kallon da yake mata, ya mika hannu ta sakar masa ruwan ba tare da tasan bae rike ba, ruwan ya fada kansa yyi saurin daga kofin ta shiga goge masa ruwan a rude tana cewa wllh ban sani ba, ya kamo hannunta yana kallonta, wani iri taji daga saman kanta xuwa kasa,