Sashe 4
Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta kwasa kayan da sabulae da omon da ta watsar mata ta fita daga falon ta shiga neman garden da kyar ta samo sbda girman gidan, ta ga bokitae da manyan robobin wanki a wajen ta tara famfo ba tare da bata lkci ba ta fara wankin, ba ita ta gama wankin nn ba sae kusan karfe daya, don kayan mugun yawa ne dasu, abun mamaki ma wasu bata ga alaman an sa su ba, ta juya bayan ta gama shanyan kayan tana kallon kudaden da ta dinga gani a wandunayensu da english wear tana ajiyewa gefe daya, ta kirga gaba daya kudin taga dubu biyar da dari biyar ce, tayi murmushi, rayuwa knn, ta dauki kudin da sauran sabulansu da omo sae jik, ta shiga cikin gidan, ta kusan cin karo da prettyn da ta ci kwalliya ta hade cikin riga da wando english wear ta sa spec da dan guntun mayafi xata fita, tayi ma Aneesahn wani irin kallon raina, ta bi gefenta xata fita Aneesah tace "ga wnn cikin kayanku na gani," ta juya tana kallon kudin da Aneesah ke mika mata ta mata wani irin kallo tana yatsine fuska tace "uwar me xan maki da shi, don me baxa ki xuba su cikin waste bin ba," tayi tsaki ta fice daga gidan. Aneesah ta bi ta da kallo da mamaki, ta yi hanyar dinning ta ajiye masu kudinsu a nn. Ta rasa me kuma xata yi gashi prettyn bata nuna mata ko ina na gidan ba, a hankali ta hau sama ta tsaya daga corridr din ta shiga sallama a hankali tana kare ma jerin dakunan kallo, ta kai minti biyar tsaye a wajen snn aka bude kofar da ke kallonta, hajiya ce ta fito cikin tsawa tace "wat! Kina da hankali kuwa, an ce maki 'yan aiki na hayo wa nn," a dan tsorace Aneesah tace "A'a hajiya na gama wankin ne ban san kuma me xanyi ba," cikin tsawa hajiyar tace "ko ma meye baki ga bell daga kasa da xaki danna ba" ta juya a sanyaye xata sauka, hajiyar tace "ko karamin kwakwalwarki bae baki cewa girkin rana xaki daura ba ynxu," Like · 4 · Report · 49 minutes ago [9:29PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 7...... A wahale Aneesah ta dawo gida ranar daga aiki don yini tayi tana aiki kmr machine, Ammi dake tsakar gida a xaune tana shirin alwala don maghrib tayi ta mike tsaye da sauri tana kallonta tace "duk hankalina ya tashi Aneesa ina ta tunanin inda kika shiga, ba karfe biyar da rabi tace xaki dinga barin gidan ba, ya akayi kika kai har maghriba, ko takowa kika yi da kafa," Aneesah ta kirkiro murmushin dole tace " ban sami mota bane Ammi, amma tun karfe biyar da rabi na bar gidan," Ammi tace "Ayya, naga ma na manta ban baki kudin mota ba, sun baki can ne," Aneesah ta gyada kai kawae duk da ko naira ba a bata ba, kuma dama bata sa rai ba, ammi tace "ta maki mutunci Allah ya biyata, gobe sae na baki kudi idan xaki tafi, daxu mamarsu jamila ta ba ma yusuf dari biyar," Aneesah tace "Allah sarki, mun gode Allah ya saka da khairan," "to ya kika ga aikin Aneesah, ba wahala dae ko, kar fa ki cuceni ki cuce kanki, ki gaya min gskya bata tsauwala maki dae koh?" Ammi ta tambayeta damuwa bayyane a fuskarta, Aneesah tayi murmushin dole don duk jikinta ma ciwo suke mata sbda tsabar aiki tace "Nace maki Ammi matar na da kirki idan ka iya xama da ita, aiki kuma ba wahala Ammi " ammi tace "to shiknn Aneesah, Allah ya taimaka, yyi maki albarka," Aneesa tace "Ameen Ammina," snn ta mike ta shige cikin daki ta cire kayan jikinta. Washegari da sassafe Aneesah ta bar gida don ta isa gurin aikinta da wuri, duk da hka sae da Hajiyar ta dinga mata masifa kmr xata rufeta da duka wae tun daxu su sumy da pretty ke jiranta ta xo ta hada masu breakfst, tana yi su sumyn na taya ta har da ce mata matsiyaciya 'yar talakawa , Aneesah ta shiga kitchen a sanyaye hawaye na bin kuncinta tana tunanin hali irin na mutanen gidan karfe bakwae da minti arbain fa ta shigo gidan suke mata tijara hka, cikin minti talatin ta gama hada masu break din ta jera kan dinnin, suka ci suka yi kat, ta dawo ta kwashi kwanukan snn ta ci gaba da aikace aikacen gidan, da rana ta hada masu lafiyayyar jollof din taliya da kaxa sae coconout drink bisa ga umarninsu, snn ta fita driver ya kaita kasuwa siyo masu ice fish da kayan ciki, don farfesun su xata yi masu da yamma kafin ta tafi, ranar ma dae ba ita ta bar gidan ba sae karfe shidda. Hka Aneesah ta dinga wahala a gidan walakancin yau daban ta gobe daban, kullum cikin kuka take a gidan don har marinta Hajiyar nayi, ga wani muguwar tsana da babbar 'yarta meenah ke mata duk tabi ta sa mata ido a gidan da tayi mistake daya ta dinga yayyafa mata masifa knn tana xagi, ita dae Aneesa sae dae ta sunkuyar da kai don sun hanata hada ido da su, ko kuma ta durkusa, duk irin abubuwan da take fuskanta a gidan kin gaya ma Amminta tayi, kullum cikin pretend take duk da irin muguwar raman da tayi, fatanta ita dae kawae tayi wata biyu tana aiki ta tara kudin waec dinta tayi gaba, amma da ta karbi kudi karshen wata matsalar gida ke karar dashi don wani lkcn ma sae su kwana hka basu ci komai ba, sae dae Ammi ta tura yusuf makwabta yaci abinci, hkn yasa ta ji ta fara hkura da karatun ma kawae, indae ta hka xasu dinga samun abinda xasu kai baki, kuma duk da irin walakancin da taga akeyi da abinci a gidan da take aiki ko sau daya bata taba debowa tace xata kawo gida ba, don itama wani lkcin da yunwa take yini a gidan sae ta dawo gida xata ci tunda ba bata suka yi ba ita kuma bata daukan abinda ba a bata ba, da hajiyar ce ma ta lura da hka duk da walakanci da gadaranta ta kan tambayeta ita ta ci abincin idan sun ci sun yi kat da 'ya yanta, sae tace mata aa don ko dan dana masu abinci bata yi idan ta gama girka masu, hkn yasa Hajiyar ta ware mata wani plate daban wae idan ta xuba ma kowa har maigadi da karen dake bayan gidan ita ma sae ta xuba nata, Aneesah tayi mata godiya ta mike ta bar wajen. Ran da Aneesah ta cika wata biyu da sati daya a gidan tana kitchen tana wanke wanke Hajiyar ta kwado mata kira "Aneesah," idan tana kwala mata kira sae ka rantse kace ita ta rada mata sunan, Aneesah ta taho da sauri ta durkushe gabanta tace "Na'am Hajiya," Hajiyar ta galla mata harara tace "da kina jina mahaukaciya kika yi min bnxa," Aneesah ta girgixa kai tace "kiyi hkuri Hajiya na bude famfo ne shiyasa banji ba," hajiyar ta daka mata tsawa "da yake kunnenki na ciwo ne ko 'yar walakanci," Aneesah tayi shiru bata ce komai ba, hajiyar tace "tashi ki ban waje raina ya daina baci shegiya kawae, anjima kya ji abinda xan gaya maki idan xuciyata ta huce," Aneesah ta mike a sanyaye ta bar wajen hawaye cike idonta, tana barin wajen meenah tace "wllh na tsani yarinyar nn mum, bata fa yi kama da 'yar aiki ba, ni ban ma yarda da ita ba kila wllh aikota gidan nn akayi ko kuma plan aka yi da ita, ji ta fa kyakkyawa gata fara, ni ban ga alamar ta taba aiki ba ma," sumy tace "ke dae bari kawae, kinga fa jiya da nake ta kallonta na kalli naga bbu abinda xaki nuna mata sae hasken bleachn," meenah ta mike a fusace tace "kika ce me, to ke din an ce maki kyau gare ki, wllh 'yar aikin nn tafi ki kyau sau dubu." [9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 11...... Wani gigitattcen mari Hajiya ta kai mata tana ball da ita a fusace, "don uwarki ke dabbar wace gari ce, baki da hankali ne xaki bata masa jiki hka da drink muguwa kawai," shi ko Haiydar mikewa yyi da sauri ya bar wajen ya haye sama, kuka ta dinga yi tana ba hajiyar hakuri tana cewa bata sani ba, amma hkn bae sa matar nn ta kyaleta ba, don marinta ta dinga yi son ranta, har ta gaji snn cikin tsawa tace "bace ki ban waje mahaukaciya kawae," da kyar Aneesah ta bar falon tana ganin jiri, a daddafe ta shiga kitchen ta jingina jikin fridge ta dinga kuka a hankali, ganin tsayuwar baxae mata ba yasa ta bude kofa ta shiga garden ta xauna ta hade kanta da gwiwa tana ci gaba da kukan takaici, wnn wace irin bakar rayuwace ita kam, ta kai minti kusan sha biyar a wajen tana ta aikin kuka, taji an dafa kafadarta a hankali, ta dago a tsorace taga wanene, xuciyarta ya kusan shigewa cikinta ganin ko waye, ya xauna gefenta yana kallonta ta matsa a tsorace tare da kkrin mikewa ta bar wajen ya rikota, a gigice ta tura hannunsa tace "nashiga uku, malam ka rufa min asiri don Allah don annabi ina rokanka," ya ki sakinta a hankali yace "to xauna kiji abinda xan ce," ta shiga waige waige a tsorace tace "kayi hkuri nace don Allah," ya wara mata manyan idanunsa yace "sae kin fara saurarata," ta sulale kasa gefensa don yaki sakinta har lkcin, hawaye na bin kuncinta tace "bka ma Allah knn" ya girgixa mata kai a hankali yace "ina yi masa," snn ya ciro handkercheif ya dafe kanta da hannunsa ya shiga goge mata hawayen fuskarta ta kauda fuskar da sauri xata mike tsaye, yyi saurin matsowa kusa da ita ya sakale hannunsa a wuyanta ya ci gaba da goge mata fuskar, ta tsorata sosai don tunda take ba a taba mata hka ba, ta fara kkrin kwace kanta tana cewa "nashiga uku meye hka malam," muryar Hajiya suka