Sashe 16
Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kukan, ganin abun nata ba na hankali bne yasa daya daga makwabtansu maman yazid ta fara mata magana cikin fada "haba Aneesah so kike ki daga ma Amminki hankali ne ki sa ta cikin wani yanayi ita ma ko me, da wanne xata ji, mutuwar danta ko haukanki, ihu da birgimar taki ce xata dawo da yusuf ko me, don me baxa ki ji tausayin amminki ba ki rarrasheta ku rungumi kaddara, sae kace ba musulma ba, ynxu dae yusuf ya rasu addu'a kadae xakiyi masa ba ihu da birgima ba," a hankali Aneesah ta fara nutsuwa tana kuka a hankali, hka suka taru suka dinga mata nasiha da bata baki, daga karshe suka ce taje tayi alwala tayi sllh tayi ma kanninta addu'a" jiki ba kwari ta mike ta fita daga dakin xuwa yin alwalan, ranar daga ita har Amminta xaune suka kwana bayan kowa ya watse, ta kasa daina kuka yi take kmr ranta xae fita, ganin kukan da take yi ne ke sa Amminta kuka yasa ta daina kukan da kyar ta dawo gefen Amminta ta xauna tana kallonta, Ammin ta rungumota a hankali tace "ya isa hka Aneesah, addu'a xamui wa yusuf kinji, Allah yasa karshen wahalarsa knn," ta gyada ma amminta kai a hankali, a hka bacci ya kwasheta jikin amminta kusan asuba. Yau akayi sadakan bakwan yusuf amma har lkcn Aneesah ta kasa sa ma kanta nutsuwa ba karamin girgixa ta mutuwar kanin nata yyi ba, sae a lkcn ta gane ashe sign din mutuwar kaninnata ta dinga ji kwanakin baya take ta ciwo ita da Ammi, Ammi kam har ta gaji da lallashinta ta sa mata ido ganin abun nata bana karewa bane don komai na yusuf ta kwashe a gidan ko hkn xae sa Aneesar ta nutsu idan ta daina ganinsu amma duk a bnxa , duk da ita ma daurewa kawae take barin idan taga 'yar tata na kuka, ita ko Aneesah irin mutuwar da yusuf yyi ne kadae ke bata takaici. Bayan sati biyu da rasuwar yusuf Aneesah na xaune bakin kofar dakinsu Ammi kuwa na cikin daki tana masu linki ta kirata ganin tun da gari ya waye take xaune bakin kofar, Aneesah ta mike da sauri ta shiga dakin ta xauna tace "gani Ammi," Ammi ta harareta tace "kuka kike yi komai," ta girgixa kanta da sauri duk da kukan ta gama tace "A'a ni ba kuka nake yi ba Ammi," cikin lallami ammi ta fara magana "Haba Aneesah so kike ki janyo ma kanki wani ciwon ko, ya kike son nayi da rayuwata idan ke ma na rasa ki," ta fashe da kuka tace "na daina daga yau Ammina amma idan na xauna kullum nakan yi tunanin me yusuf yyi ma baffa da xae turo a kashe shi," cikin fada Ammi tace "wa yace maki baffa ne ya turo a kashe shi, ni fa bana son surutun bnxa, daga mota ta bugesa ta gudu kuma sae ya xamanto baffa ne yasa a xo a bugesa a gudu," tace "Ammi wlh shine, da gangan fa aka ce mai motar ya bugesa snn kuma ya take sa, Allah ya isan ma," Ammi tace "ni dae ki tausaya min ki daena sa ma kanki damuwa Aneesah in ma shi ya sa a kashesa din don kansa, ynxu abinda nke so dake gobe ki shirya ki tafi wajen aikinki kin ga yau sati biyu rabon ki da xuwa kuma bbu ddi hkn, sae kiyi mata bayanin abinda ya faru," Aneesah tayi shiru gabanta na faduwa jin an kira mata gun aikinta, can dae tace "to Ammi," washegari Aneesah ta shirya ta kama hanyar gidan aikinta gabanta na faduwa, jikinta a sanyaye ta shiga gidan bayan ta gaida mai gadin, ta karasa stairs din balcony ta hau ta tsaya bakin kofar falon xuciyarta na bugawa ta kasa shiga, da kyar tayi shahada tayi sallama ta shiga falon tana addua a xuciyarta da ya kasa daina bugawa, suna xaune gaba dayansu a falon hankalinsu kwance suna kallon tauraron dan adam, Haiydar na kwance kan kujera amma shi ba kallo yake ba idonsa a lumshe, duk suka juya suna kallonta ta karaso cikin falon a sanyaye ta durkusa tana gaida Hajiyar da ke ta girgixa kafa tana mata wani mugun kallo, ta sunkuyar da kanta da sauri ta rasa ta ina xata fara ma, cikin tsawa meenah tace "don uwarki ki fice mana gaban TV ko baki ga abinda muke yi bane wawiya kawae," ta ja gefe a hankali hawaye ya cika idonta ta juya tana kallon Haiydar da ya tsura mata ido. [9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 32..... Aneesah ta fixge hannunta tana masa wani mugun kallo gabanta na faduwa tace "ka fitar mana a gida kar na maka ihu malam, wnn ai iskanci ne da rashin tarbiya, xaka fado mata mutane gida kamar barawo," ya wara idonsa da mamaki yana kallonta, "ni kike ce ma barawo," ya tambayeta yana kallon cikin idonta, tayi tsaki ta juya xata bar wajen ya fixgota ya watsa mata mari, tare da hadeta da bango yana huci, "ke kinsan ko da wa kike magana don uwarki kuwa," cikin kuka tace "na sani mana, mugu, axalumi, mara tarbiya, masu cin dukiyar marayu....." wani gigitattcen marin ya sake wanke ta da a fusace yana huci, ya shake wuyarta yana kallonta da kyau xae yi magana, aka shigo gidan, Haiydar ne, ya tsaya daga bakin kofar xauren ya rungume hannayensa yana kallonsu, Aneesah dake ta faman kuka ta juya tana kallonsa tana ci gaba da rusa kukan, Almajirae ne suka shigo gidan rike da kayayyakin abinci tun daga kan, buhun shinkafa, cartons din taliya man gyada, da doya, Haiydar ya ja gefe ya basu hanya suka shigo gidan suka dire kayan abincin, ya ciro dubu uku ya mika masu hade dacewa tnk yhu, suka yi godiya suka fice daga gidan, Abdul da ke ta bin Aliyu da kallo ya yatsine fuska a walakance yana kallon Aneesah cikin tsawa yace "waye wnn kuma," bae rufe bakinsa ba Haiydar yace "Barrister Aliyu Muhammad, kai fa?" ya tambayesa yana masa wani irin kallo, Abdul yyi wani mugun murmushi ya sake Aneesar da har lkcn yana rike da ita yace "uban meye hadinki da wnn," xata yi magana Haiydar ya riga ta, "abinda ya hadata da kai shi ya hadata ni," Abdul yyi masa kallon tsab daga sama xuwa kasa snn ya fashe da wani wawan dariya yace "xamu gani," snn ya juya a fusace ya bar gidan, Aneesah ta sulale kasa a hankali ta hade kanta da gwiwa tana kuka, Haiydar ya karaso gabanta ya durkusa ya dago kanta yace "bana son kina kuka Aneesah, ki kwantar da hankalinki bbu wanda ya isa ya cutar min ke kinji kanwata" tayi shiru bata ce komai ba tana kallonsa, ya ciro hankici ya share mata fuskarta snn ya mike tsaye yace "Ammi fa," a hankali tace "ta tafi kasuwa," ya durkusa gabanta kuma a hankali yace "kinsan me Aneesah, ki daina tsayawa gida ke daya, duk inda Ammi xata kuje tare ," ta gyada masa kai ta dan yi murmushi tace "to yayana," ya dagota shi ma yana murmushin ya ja ta xuwa kan tabarman da take xaune da litattafenta, suka xauna ya jawo books din yana dubawa, binshi kawae take da kallo, ya dago kai suka hada ido ta rufe fuskarta da sauri tana 'yar dariya. Abdul ne xaune kan kujera yana kallon ubansa dake ta fama latse latsan laptop, baffa ya dago yana kallon Abdul din yace "ya aka yi guy?" Abdul ya tabe baki yace "ca nayi ina son cikin satin nn, ka daura min aure da Aneesah, da ita xan koma london, don aure nake so, kuma ina sonta," baffa ya mike a fusace yace "Aneesah, wacece Aneesah, uban me xaka yi da Aneesah, ba gwara ka kawo min baturiya ba kace na aura maka ita, Aneesar bnxa" Abdul ya mike ransa a bace yana nuna uban nasa da dan yatsa yace "kaga dad, Aneesah nace maka xan aura, kuma ita xan aura, wnn ai mgnr kawae kke min, ni fa xan xauna da ita ba kai xaka xauna min da ita ba," baffa ya sauke ajiyar xuciya ransa a jagule yana dan kame kame yace "look guy bae kai ga hka ba, kar ka damu xan aura maka Aneesah vry soon, amma ba ynxu ba sae nn da wata daya," Abdul ya buga table din gabansa, a fusace yace "y one month dad, da ita nke son komawa london nace maka, ko baka gane bne," baffa yace "cool down son, yau fa satinka biyu, kafin ka koma xan aura maka ita, kuma sati biyu xakuyi a nn kafin wata biyun hutunka ya cika, nafa san abinda nake yi," Abdul ya koma ya xauna yana murmushin mugunta yace "vry good dad." baffan ya kirkiro murmushi yyi pat din bayansa yace "gud son xan fita guy, sai na dawo," yana kai wa nn ya fice daga dakin da sauri. Abdul ya mike tsaye yana murmushin mugunta hade da cije lebe, can kuma ya fashe da dariya har da buga kafa snn ya fice daga dakin yana fi to. Hmm sistrs knn, ku dinga ma mutum uxuri plss, ku ka san abinda ya hanani post kwana biyu, rashin lfya ne, wani abun daban ne, duk baku yi tunanin hka ba, amma har na samu masu gaya min magana a whatsapp, wasu har da cewa xa suyi xuciya su daina karanta littafin khaleesah Haiydar, hmm ok oo, baku yi tunann ko ina da aure ba ko ina da yara da burden dinsu baxae bari nayi type ba wani lkcn, ni dae don mu nishadantu kuma don na fadakar nake yin wnn abun, amma Allah sarki makiyana sun fi masoyana yawa, duk da hka ina sonku gaba daya, Allah ya bar [truncated by WhatsApp] [9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 31..... Hajiya Zuwaira ta bude baki da mamaki tana kallon Aneesah, har ta gama fadin abinda ke ranta snn ta fice daga dakin har tana neman bangajeta, hajiyar ta rike haba da mamaki tace "ni 'yar nn ke gaya ma magana hka? Haiydar ya juya yana kallon Ammi dake xaune har lkcn bata bude baki ba yace "yauwa muna magana Ammi," Ammi