← Book details Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 58

Sashe 12

Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dinnin suna kallo a wayarsa, sumy tace "wae har ynxu 'yar aikin can bata gama guga bne a sama, gashi ina son na aiketa supermarket siyo min sabulu, don soap din wanka na ya kare, Hajiya tace "to ni ina nasani, wae Haiydar har ynxu bata gama gugan bne, xata mana farfesun kifi fa kafin ta tafi," yyi kmr bae ji su ba yana ta kallonsa da pretty, Meenah tayi tsaki ta mike tsaye tace "bari dae naje na duba, kila shegiyar taji sanyin A.c ma bacci ya dauketa a gun," Haiydar ya mike da sauri cikin tsawa yace "wat! Dakina xaki shiga, da ko kinga yanda ake cin uban mutum yau, don Allah je ki, na rantse da Allah idan ban sumar dake ba to sae na karya ki yau," Hajiya ta mike tace "ohh ni fateema na shiga uku, sae kace ba kanninka ba Aliyu meyasa kke hka, duk ka dauki karan tsana ka daura ma 'ya yan nn, meye a ciki don tace xata je dubo 'yar aiki, wnn wani irin rayuwace hka irin naka," ya daga kafada alamar bae damu da xancen nata ba yace "ai yaran ne basu da tarbiyar arxiki," sumy ta tabe baki tace "ni dae ko min dare wllh sae taje siyo min sabuluna, ba ma kaya ba in xata iya har dakin ma ta goge dole ta fito taje min market," meenah tace "nima wllh ko min dare kafin ta bar gidan nn sae ta min gugan kayana," Haiydar ya mike tsaye ya fara saukowa daga matakalan dinning din, gaba daya suka fasa ihu a tsorace suka yo bayan Hajiyarsu, ita ko ta mike tsaye da sauri tana cewa "kana ma Allah da annabinsa ka rabu da 'ya yana a gidan nn Aliyu, wllh wllh xan bata maka rai na Hada ka da Alhaji usman fa, wnn wace irin jaraba ce," ko kallon daga ita har 'ya yan nata bai yi ba ya haye sama, bayan kmr minti biyar sae gashi ya sakko Aneesah na biye da shi a bayansa, har lkcn Hajiya na tsaye, su meenah na rabe a bayanta sumy har da kuka, ya kalli Aneesah cikin tsawa yace "ke kama hanyar gidanku, kin gama aikinki 4 today," ta marairaice tana kallon Hajiyar da ta galla mata wani mugun harara, ya daka mata tsawa yace "nace ki fice ko bakya ji ne," a sanyaye ta fita daga gidan karfe hudu saura minti biyar," ya koma ya xauna, Hajiya tayi shiru tana kallonsa cikin lallami ta fara magana "Haba Aliyu so kke yarinyar nn ta raina mu ne, wnn ai bae yi ba, biyanta fa nake yi ka dinga hanata kuma tana ma yarana aiki, don su fa na kawota gidan," yace "sae randa suka canxa halinsu nima xan canxa," snn ya haye sama, meenah ta ja dogon tsaki tace "bnxa kawae dan wahala, in ina son dawowar wnn gantalallen mutumin gidan nn nayi ma Allah karya wllh," sumy tace "ke ko ni, wnn ai obstacle babba ne a gidan nn gare mu" Hajiya dae na tsaye tana kallonsu ta kasa cewa komai, pretty ta mike tayi tsaki tace "fitsararrun bnxa kawae, ai kune gantalallun," snn tayi hanyar stairs da gudu meenah ta bi ta har tana faduwa ta cafkota ta shiga xuba mata mari tana duka, pretty ta fasa ihu, sae ga Haiydar da sauri ya sakko, meenah ta juya da gudu xata bar wajen ya cafkota ya haye sama da ita Hajiya ta taho da gudu tana cewa "wllh ka sake min 'ya ta kasan abinda tayi mata ne," ko saurararta bae yi ba ya shige da ita dakinsa, ya kulle kofar da makulli, ranar shegen duka yyi mata da belt, su Hajiya da sumy aka tsaya bakin kofa suka dinga rusa kuka yaki bude kofar har sae da yyi mai isarsa snn ya cillota waje ya kulle kofarsa. Aneesah na komawa gida ranar Ammi ta tambayeta da mmaki me ya dawo da ita lkcn, tay mrmushi tace "nace mata bana jin ddi ne shine tace naje gida na huta, Ammi tace "Allah sarki, Allah ya kara masu budi, matar na da kirki," Aneesah tayi murmsuhi ta shige daki kawae a xuciyarta tana cewa lallai kam tana da kirki. Ko da Aneesah ta tafi aiki washegari bta ga Haydar ba, ta sha wahala ranr dn knta suka huce dk abnda yyi msu jiya daga su har uwarsu, ita de pretty bata ce kmai ba kallnsu kawae take, sun aiketa kasuwa ranr ya kai sau uku kuma a kafa, snn dk se da tyi masu guga da kwalemar dakunansu, krfe uku suka bar gidn bayan sn ci abncin rana, sumy ta kawaso mata takalmnta ta wanke na wankewa na gogewa kuma ta goge tce mata to, snn suka bar gidn gaba daya har da Hajiya amma banda pretty, sae bayan fitarsu pretty tayi mata magana ta kuma kawo mata maganinta na jiya da Haydar ya siyo mata tace yace ta bata, ta kuma kama mta sauran aikin da suka rage a gidan kafin 'yan uwanta su dawo. [9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 20..... Pretty ce ta shigo gidan, ta tsaya bakin kofar tana kallonsu ba tare da tace komai ba, Aneesah ta juya da sauri cikin tashin hankali xata bar wajen, sai maimaita nashiga uku take yi, Haiydar yyi saurin rikota, ta buge masa hannu tare da fashewa da kuka tace "ni ka rabu dani don Allah," ya ki sakinta sae ma xaunar da ita da yyi gabansa, ya juya yana kallon prettyn da har lkcn ke tsaye tana kallonsu yace "c'mon Zainab xo mu ci abinci," ta karaso falon ta ajiye jakarta kan kujera ta xauna kan carpet tace "washh yaya wllh na gaji dayawa akwae rana," ya mika mata spoon yace "to meyasa kika dawo da wuri," tace "kawae na gaji da xaman gidan ne," Haiydar ya juya yana kallon Aneesah da har lkcin yana rike da ita don kar ta tashi yace "kanwata kukan me kike kuma," tayi shiru bata ce komai ba sae faduwa da gabanta ya ke yi tana kallon prettyn a tsorace, pretty ta fara cin abincin ta tana ba yayan nata lbrin kawarta da taje wajenta, shi ko hankalinsa na kan Aneesah da ta ki sake wa, ya dubi pretty dake ta cin abincin ta yace "je ki sa key a kofa pretty," taje ta sa ta dawo, ganin Aneesah taki karban abincin da yake bata a baki yasa ya bata spoon ta ci da kanta, nn ma taki, pretty tace "kila bata son ta ci da kai ne yaya, ka xuba mata nata daban," yyi yanda pretty tace ya tura mata gabanta ya hade rae yace "oya maxa ki ci idan baki son nayi fushi," ta dago kai a hankali tana kallon pretty, prettyn ta sakar mata murmushi, ita ma ta dan yi murmushin snn ta fara cin abincin a hnkli, hka suka dinga cin abinci pretty na basu lbri har suka gama pretty ta kwashe kwanukan ta kai kitchen ta dawo suka ci gaba da hira, tun Aneesah na yi masu shiru har ita ma ta sake suna yi, pretty ta kalleta tace "yauwa wae me kike shafawa a lips dinki kullum sae na gansa pink" Aneesah tayi murmushi tace "ni bna sa komai," Haiydar yyi murmushi yace "ke ma kina son naki ya xama irin nata ne" pretty tayi dariya tace "eh yayana," yace "to xan ce ta tsam maki, ynxu dae je ki wanke plates din da muka ci abinci ki dawo" Aneesah ta ce "A'a xan wanke," ya riko hannunta yace "A'a bar ta ta wankesu, ke da baki da lfya magani xaki sha ynxu ma," pretty tace "bata da lfya ne," yace "eh" tace "Allah ya sauwake snn ta kwashi kwanukan tayi kitchen dasu ta wanke," ya lallabata ya bata magani tashi da kyar, snn tace masa xata je tayi masu gugan kayansu, ya harareta yace "baxa kiyi ba wllh," ganin yaki barin ta ta shi yasa ta hkura ta tsura masa ido kawae tana kallonsa ya hura mata idon yace "wnn kallo hka," ta boye fuskarta tana murmushi. Pretty ta dawo falon bayan ta gama wanke wanken tace "yayana na gama," yace "yauwa kanwata," ta xauna suka ci gaba da hirarsu kmr da can sun saba da Aneesah, budewar gate da suka ji yasa Aneesah ta mike tsaye da sauri, pretty ma ta tashi da sauri tayi hanyar kofa don lekawa taga ko waye, ta dawo da sauri tace "yaya mum ce da su meenah," Aneesah ta fixge hannunta daga rikon da yyi mata tace "na shiga uku don Allah ka sake ni," yace "baxa fa ki kara yin aiki gidan nn yau ba, gwara kawae ki tafi gida in hka ne," ta marairaice masa tace "lkcn tafiyata bae yi ba don Allah ka rabu dani guga xanje na masu," ya fixgota yyi hanyar stairs da ita tana masa magiyan ya kyaleta suna hawa sama ya bude bedroom dinsa ya jefata ciki yace "kar ki kuskura ki fito, gwara kawae kiyi bacci har lkcn tafiyar taki yyi," ya ciro makulli ya kulle dakin ta waje snn ya sauko downstairs, pretty ta ruga ta bude masu kofa Meenah ta ce "ina wnn shegiyar yarinyar taxo ta yi serve din mutane yunwa nke ji," Hajiya ma ta xauna tana tambayar haiydar har ya dawo, yace "ehh snn ya gaida ta, ta amsa tana cewa prettyna kin ci abinci, pretty tace "eh naci," a fusace hajiya tace " wae ina wnn gantalalliyar yarinyar take bata ji shigowrmu bne," Haydar yce "tana sama na sa ta guga ne," cikin gadara meenah tace "ni tayi min nawa gugan ne pretty?" pretty tace "na yaya take yi," meenah cikin bacin rae take "ba ni na fara sa ta ba xata bar min kayana don rainin wayo," Haydar yyi mata wani irin kallo yace "idan baki yi hnkli ba wllh yau sae na fasa mki kai "dare me" kuma ki gni," meenah ta hararesa tace "to kai naga ba dry cleaning kake kai kayanka ba idn ba gulma ba yaushe 'yan aiki suka fara maka guga," sumy ta tabe baki tace "shi dae na gani," ya mike cikin xafin nama ya yo kan meenar da ta fasa ihu a tsorace
Chapter 12 · 0% Book details