Sashe 32
Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tace "ni da bako ne maman mubarack," tace yana ina shi kuma a ina kika san sa, ko wnn ne mai xuwa gun ki, dama baffanki ba gidansa ya kai ki ba, Aneesah tace "yana waje," matar tace "to ya shigo mana, Aneesah bana son ki kara ko da minti goma ne a anguwan nn kar yan iskan layin nn su gan ki mu shiga uku," ynxu dae maxa je ki ce bakon ya shigo," Aneesah ta fita gabanta na faduwa suka shigo tare da Mujaheed ya gaisheta ta amsa da fara'a snn ta fara masa bayanin abinda ake ciki ynxu, Mujaheed ya fara jero mata tambayoyinsa na gado taki amsa ko daya tace ita dae ba ruwanta kawae ya tafi da Aneesah kar su sake dawo wa anguwan, Aneesah na kuka Amina ta hadata da nikaf ta saka, ta rakosu har mota suka shiga, Mujaheed ya bata kudi mai yawa ta karba da kyar snn suka bar anguwar har lkcn Aneesah na kuka kmr ranta xae fita, cikn kuka tace "ina xaka kai ni yayana," bae tanka ta ba har suka isa gida ya shiga yyi parkn snn ya juyo yana kallonta a nutse ya fara magana "ki yarda dani Aneesah ba xan taba cutar ki ba, ki daukeni a matsayin yayanki da kuka fito ciki daya, idan ma baxa ki iya tsayawa tare da ni a gida daya ba ni xan bar maki gidan snn na maki alkawarin xan nemo maki amminki, Aneesah me yasa baki gaya min gskyan cewar baffan ku ne ya rike dukiyarku ya hana ku ba, wllh wllh ni Mujaheed sae na sa mutumin nn ya gane kuransa, xan sa ayi masa abunda har ya mutu baxae manta ba kuma baxae sake sha'awar cin abinda ba nasa ba, snn ko tsinkenku baxan bari a hannunsa ba" yana gama fadin hka ya fito ya bude mata mota ita ma ta fito a sanyaye, yana gaba tana binsa a baya har suka shiga cikin falon, ta xauna kan kujera duk jikinta a mace shi kuma ya haye sama. Ba a jima ba ya sauko yace "xan tafi masallaci, ke ma kije kiyi sallah," to kawae tace masa ya fita daga gidan, ita kuma ta hau sama ta shiga dakin da ya gwada mata daxu. Tana idar da sallah ta sake wanka, tayi kwanciyarta kan carpet din dakin abun duniya ya isheta. [12/8, 21:11] +234 803 751 8717: Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 64..... Karfe takwas Mujaheed ya shiga da motarsa gidansu Haiydar, ya nemi gu yyi parkin ya fito, ya daga ma mai gadin dake gaishesa ba kakkautawa hannu kawae ya shiga falon gidan da sallamarsa, Hajiyar na xaune tana cin tufar dake gabanta a kan dan table, pretty na kwance kan kujera tana kallo, tana ganin Mujaheed ta mike da sauri ta rungumesa tana cewa "yayana oyoyo," yyi dariya ya daga ta sama yace "kai garin yaya kika yi nauyi hka bbyna," ta galla masa harara tace "ni ba nauyin da nayi yaya, karfinka dae ne ya ragu kila," yyi dariya ya kamo hannunta suka karasa cikn falon ya gaida Hajiya dake ta murmushi tace "sannu da xuwa jaheed ya hanya," yace "lfya lau wllh mum, ashe abun da ya faru knn?" Hajiya tayi kwafa tace "ka bari kawae," yace "to mum tun farkon faruwan abun meyasa baki kirani ba ai ina Nigeria," Hajiyar ta tabe baki tace "to dan iskan ya sanar min kana Nigeria ne jaheed, ae ni Haydar da ba dan wani abu ba da sae nace musanya aka min a asibiti" Mujaheed yyi dariya yace "to ynxu ya ake ciki mum, amma lawyern da kika dauka bae iya aikinsa ba ina ga dae ko, ya xa ayi ya bari a kai sa har prison, haba don Allah," Hajiya ta bude baki tace "in ji wa yace maka bai iya aikin ba, shi umar din ne bae iya aiki ba, tab, ae wnda yake karewan ne babban dan iska kuma shi ya kai kanshi kurkuku" Mujaheed yace "ae Aliyu ban san irin shi ba, wae ma ina suka hadu da yarinyar tukunna Hajiya?" Hajiya tayi murmushin takaici tace "kaddara fa jaheed, rabon ayi, aiki na kawota take min a gidan nn, ashe wae soyayya Haiydar yake da tsinanniyar shegiyar bamu sani ba, wancan munafuka algungumar prettn na sane bata gaya min ba Mujaheed," Mujaheed ya juya da sauri yana kallon pretty, ta dan yi tsaki ta mike tsaye ta haye sama Mujaheed na kiranta ko waigowa bata yi ba, Hajiya tace "tsayawa xata yi aka ce maka" Mujaheed yace "ikon Allah da 'yar aiki kuma haydar ya buge da soyayya anya kuwa yana da hankali mum?" Hajya tace "ka bari kawae ashe ma har gidansu yana xuwa ban sani ba, dama su sumy na ce min suna xargin soyayya yake da ita sbda irin reactions dinsa a kanta, kiri kiri fa sae ya hanata mana girki muna ji muna gani wae ae mu ma mata ne," Mujaheed ya dinga dariya har da buga kafa, Hajiya ta girgixa kai tayi murmushin takaici tace "ka bari kawae Jaheed ae Haydar ya cuce ni a rayuwa," Mujaheed yace "to yanxu wa kuke tunanin ya dauke 'yar aikin, to wae ma ya gani jikin mere mai aiki yake so idan ba wautan Haydar ba" Hajiya tace "ka bari kawae Mujaheed, yau da xan ga tsinanniyar 'yar nn wllh wllh bbu abinda xae sa baxan kashe shegiya ba ko kuma na sa a kasheta, kai ba ita ba har wni nata xan iya kashewa wllh ace sbda ita dana da na haifa na galallawa a gidan yari, kuma ynxn ma bae baci ba don nasa ana ta min bincike har a gano ta, kaji fa kullum maganrsa idn naje gunsa baya wuce na hankalinsa ya kasa kwanciya don bae san halin da take ba ynxu, kaji tsiya jaheed" Mujaheed yace "anya ma ba asiri suka masa ba," Hajiya tace "wllh naje ance bbu abinda aka masa, tsabar iskanci ne da wlknci irin na Aliyu," Mujaheed yace "to ita yarinyar kyau gareta ne Hajiya," Hajiya ta hade rae tace "ni ka rabu dani idan baxa ka min tambayar arxiki ba Mujaheed, kyan banxa, uban me ake da kyan talaka matsiyaci," Mujaheed yyi dariya yace "Allah ya baki hkuri, ynxu wa kuke tunanin ya dauke yarinyar ko kuwa da gsken sharri aka masa," Hajiya ta tabe baki tace "oho dae ko sace ta aka yi da gsken ko ma karya ce ba ruwana ni dae dana ya fito," Mujaheed ya gyada kai yace "shknn mum, gobe xan je gunsa na samu wasu informations din kuma," Hajiya tace "ahaf Allah ya sa ya baka hadin kai tunda yace shi dabba ne," Mujaheed yace "ae ki bar ni da shi kawae mu, don uwarsa kar ya bani hadin kan," hajiya tace "to, amma ka bari jibi don ba lallai bne a bar ka ka gansa gobe, tunda jiya mun je kar kayi wahalan bnxa ga dankaran nisa gun," Mujaheed yace "sun ci ubansu, don me baxa a bar ni na gansa ba," Hajiya tace "a'a ni fa taurin kanku ke hada ni da ku, nace ka bari jibi," Mujaheed yace "to yyi ni xan koma mum," tace "lah ko ruwa baka sha ba bari sumy ta hado maka dinner ko baxa ka ci ba ka tafi dashi," yace "A'a nagode mum, sae wani lkcn dae, su sun fi karfin su sauko su gaida mutane 'yan rainin wayo ko," Hajiya ta mike da sauri tace "aa bafa su san ka xo ba Mujaheed, meenah ma bata nn," ya tabe baki yy kofar fita sae ga meenah ta shigo cikin matsatsun kaya da dogon heel, tana ganinsa ta gyara gashin dokin kanta ta bi ta gefensa xata wuce ya fixgota "don uwarki daga ina kike ynxu?" ta galla masa harara tace "kaji min mutum aikena kayi ne?" ya xabga mata mari yace ni kike gaya ma hka don ubanki, hajiya ta karaso a fusace tace "kaga mujaheed fitar min a gida tun kan raina ya bace wnn wace irin jaraba ce xaka marar min 'ya daga xuwanka," ta fixge hannunsa daga rikon da yyi ma meenar dake ta rusa ihu tace "Allah ya kiyaye," ta ja 'yarta suka haye sama tana ci gaba da masifa. Yyi tsakin taka[truncated by WhatsApp] [12/8, 21:11] +234 803 751 8717: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 65.... Washegari Aneesah ta tashi da asuba ta shiga bathroom tayi alwala ta fito tayi sallah, snn ta fara gyara daki duk da ba abinda ya samu dakin don ko ina fes, a xuciyarta tace "ko wancan mutumin ya dawo jiya, don bata ji shigowarsa ba da wuri tayi bacci, tana gamawa ta shiga wanka ta ga sabon toothbrush ta dauka ta wanke bakinta snn tayi wankan ta fito, bata yi karambanin taba kayan shafe shafe da turarruka da kayan kwalliyan dake cike gaban madubi ba, ta dae sane jikinta da dankwalin kayan da ta sa don ko towel ma bata taba ba, snn ta dauki wata jallabiya baka da ta gani linke a dakin a gefen gado ta xura, ta dauki Hijab ta saka. Har gari ya washe bata yi gigin bude kofar dakin ba, tayi jigum tana tunanin duniya aka kwankwasa kofar dakin, tayi shiru tana kallon kofar, yyi sallama da muryarsa mai sanyi nn ma bata amsa ba, sunanta ya shiga kira a hankali, ta mike tsaye ta isa bakin kofar ta jingina tace "ya akayi?" taji yace "to fa, Allah ya baki hkuri sallah dama nake son sanin ko kin yi," tace "dama da safe ake sallhn?" yyi 'yar dariya yace "nasani ko a kauye hka ake yi," tayi murmushi mara sauti tace "to ka kyauta ma kanka," yace "baxa ki bude kofar ba kanwata," tace "in maka me?" ya dan yi shiru snn yace "breakfst xaki hada mana," tayi shiru snn tace "to ka tafi xan fito," yace "ok kanwata tnx," bayan kmr minti biyar ta bude kofar a hankali don a tunaninta ya tafi, tana bude kofa suka yi ido hudu da shi yana jingine jikin bango sanye da jallabiya baka, yyi murmushi ya kashe mata ido a rude don bata yi xaton yana nn har lkcn ba ta juya da sauri xata shige dakin ashe ta jawo