Sashe 15
Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
saka da alkhairi snn ya fita daga gidan yana kallon Aneesah. Sae da ya fita snn a hankali tace ma Ammi bari ta rakasa Ammi tace mata to, ta mike ta bi bayansa, yana jingine jikin motar yana jiranta, ta karaso gefensa ta tsaya a sanyaye tace "nagode yaya Haiydar," yyi murmushinsa mai kyau yace "nima ngd fateema," ita ma murmushin tayi ta boye fuskarta, yace "Aneesah an rufe registration din waec din ne?" a hankali tace "nima ban sani ba," yace "ok find out frm yhur sch mates," tayi shiru bata ce komai ba, yace "Aneesah naxo gidanku ko ruwa baki bani ba, gashi dama yunwa nke ji, kin san bnyi break ba," ta xaro ido tace "lah ae ban san xaka sha ba, bari na debo maka," yyi dariya yace "wasa nake maki," ya bude motar ya fito da ledar Hijabs din ya mika mata tace "na me," yace "naki mana," ta marairaice tace "A'a ni dae wnn ya isheni wllh," ya harareta yace "ki karba wucewa xanyi," a hankali tasa hannu ta dan risina ta karba snn tayi masa gdya, yyi murmushi yace "welcm Aneesah, i wil be goin now," ta gyada masa kai ya bude motar ya shiga ta daga masa hannu snn ta juya ta shiga gida, shi ko yyi reverse ya bar anguwar, hanyar gidansa yyi, don yasan Hajiya na can kila ta tara masa mutane ana jirasa don ma ya kashe wayoyinsa. Aneesah na shiga ta nuna ma Amminta hijjaban, Ammi tace "shine xaki karbo Aneesah ni fa ba ruwana," Aneesah tace "wllh Ammi nace ya bar shi yaki," a hankali ta shiga fito da su tana dudduba, tana fito da na ukun knn bandir din dari biyar biyar ya fado, ta koma baya da sauri tana kallon Amminta, ammi tace "wnn kuma daga ina?" Aneesah tayi shiru tana kallon kudin snn ta dago tana kallon Amminta a hankali tace "shi ya saka Ammi," Ammi ta kasa cewa kmai sae kallon Aneesar da take yi, can dae ta mike ta shige daki kawae, Aneesah ta bi ta ta fashe da kuka tace "wllh Ammi ban san ya saka ba," Ammi ta girgixa kai tace "to ki ajiye masa kudinsa kar ki taba," Aneesah tace "to" snn ta ajiye hijabs din da kudin cikin jakar kayanta. Washegari da yamma ta je dibo ruwa a borehole tana dawo wa xata shiga gida taji an mata horn, ta juya da sauri tana kallon motar da mamaki, Haiydar ne, ya bude motar ya fito ya wara mata ido yace "me hannunki yake da xaki daura ruwa a kai Aneesah," tayi murmushi tana kallonsa bata ce komai ba ya karaso gabanta ya sauke mata bokitin ruwan ya ajiye kasa yana mata wani irin kallo, ta boye fuskarta da tafin hannunta tana 'yar dariya tace "xafi hannun xae min shi yasa na daura a kai," ya harareta yace "to karki sake," tace "uhum," snn ta dauki bokitin ruwan a hannu yace "bari na taya ki mana," ta ce "A'a ina xuwa," ta shiga gidan, bayan kmr minti biyar ta fito rike da leda tana kallonsa tace "jiya kayi mantuwa cikin ledar da ka ban," ya galla mata harara yace "Ammi na ba bake ba, ni ina ruwana dake," ta marairaice fuska tana kallonsa tace "dn Allah ka bari ka amshi kayanka ni dae," ya hade rai yace "ba fa na son hka Aneesah," tayi shiru tana kallon kasa, yace "ya maganar da na maki jiya na waec kin tambaya?" ta wara ido tace "na manta," yyi mata wani irin kallo yace "you re nt cerious," ya ciro wayarsa daya ya mika mata yace "idan kin tambaya kya kirani ki gaya min nmbrna na ciki xaki ga anyi save da barrister," ta xaro ido tace "A'a ni bana so wllh ka tafi da kayanka watarana idan kaxo xan gaya maka idan na tambaya," ya ajiye mata kan wani dutse yace "idan na tafi ki barshi a wajen, ki gaida min da Ammi," yana kai wa nn ya shige motarsa ya juya ya bar anguwar, tayi kmr xata yi kuka har ta daina ganin motar snn ta dauki wayar ta shiga gida dashi. Da daddare tana wanke wanke a tsakar gida Ammi na daki taji kamr motsin mutum a xaure, ta dan tsorata ta mike da sauri tana jiran taga wa xae shigo taga bbu kowa, a ranta tace to ko dae ya Haiydar ne, hkn yasa ta karasa da sauri don tunaninsa take lkcn, ta shiga xauren tana dan waige waige cikin duhu bata ga alamar kowa ba ta dan leka waje ta dae ga motar a parke amma ba na Haiydar bne, kuma ba a kusa da gidansu akayi parkin din ba, ta danyi tsaki ta juya xata koma cikin gidan taji ta ci karo da mutum ta tsorata sosae xata fasa ihu ya fixgota ya rufe mata baki a hankali yace "menayi maki xaki fasa min ihu," a tsorace ta koma baya tace "ya Abdul," ya wara mata ido cikin duhun yace "waww kin xama 'yan mata bbyn nn," ta turasa da karfi a fusace xata bar xauren ya fixgota yace "yaushe na fara wasa dake?" [9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 27..... Sun yi nisa sosai, kawae tafiya yake ba tare da ya san inda xa shi ba, Aneesah ko bbu abin da take sae aikin kuka, ganin kawae tafiya yake bai da alamar tsayawa yasa cikin muryar kuka tace "ni ka sauke ni a nn na wuce gidanmu," sae a snn yyi parkin gefen titi, ya juyo yana kallonta, ta rufe fuskarta tana ci gaba da kuka, ya kamo hannunta yace "ya isa hkan Aneesah kiyi hkuri, bana son kina kuka, nn" bata ce masa komai ba amma ta kasa daina hawaye, ya ciro handkerchief ya goge mata fuskarta yana kallon gashinta da duk da talaucinsu ba a haramta mashi gyara ba, don sae kyalli yake ga tsantsi snn baki wuluk, ta cire hannunsa daga kan gashin nata da ya dafa a hankali tace "hijabina," ya gyada mata kai kawae, snn ya ja motar suka bar wajen, sun danyi tafiya mai nisa snn taga yyi park yace "fito ki xabi wanda ki ke so," ta kasa cewa komai tana kallonsa, ya gyada mata kai ta fito a sanyaye daga motar suka fara tafiya a hankali taga duk ido ya dawo kansu barin ita, da sauri ta fixge hannunta tace "ni baxan iya ba, ban da dankwali," ya komar da ita motar snn shi yaje xabo mata Hijab din, bayan kmr minti goma ya dawo da katon ledar boutique a hannunsa ya shiga motar yana kallonta ta sunkuyar da kai, yyi murmushi ya bude mata ledar yace "gashi ki xabi wanda xaki sa," a hankali ta jawo wani milk colour taga yana da tsayi hkn yasa ta saka shi kawae, tana kallonsa ya gyada mata kai yyi murmushi snn ya tada motar suka bar wajen, sae da suka hau kan titi snn a hankali yace "ina ne gidanku?" ba tare da ta kallesa ba tace "ka ajiye ni a nn, sae na wuce," ya girgixa mata kai yace "baxa ki fita daga motar nn yau ba knn," ganin da gaske yake yasa ta gaya masa anguwarsu kawae in yaso sae ta karasa gida da kafa, "aneesah," ta ji ya kirata ta juya tana kallonsa, idonsa na gaban titi yace "me ya sami yusuf?" nn da nn taji hawaye ya ciko mata ta girgixa kai da kyar tace "mota ce ta bugesa suna dawowa daga sch," yace "mota kuma, to ina mai motar," ta goge hawayen idonta tace "bae tsaya ba, kuma withness sun ce da gangan ya buge sa bayan ya bugesa kuma ya taka sa ya gudu," yyi parkin da sauri yana kallonta, ta sunkuyar da kanta tana ci gaba da xubda hawaye, yace "baffanku ya samu lbri," tace "eh amma bae xo ba har ynxu wae matarsa tace ya tafi lagos, kawae baffa ibrahim ne ya xo shima shekaranjiya yace gangancinmu ne ya kashe yusuf," Aliyu ya gyada kai bae ce komai ba ya ja motar suka bar wajen, har suka isa anguwar bai sake ce mata komai ba, sae da yyi da gske da ita snn ta nuna masa gidansu don ca tayi ya ajiyeta xata karasa da kafa, tace masa tana xuwa snn ta shiga cikin gidan, Ammi na share tsakar gidan don ita har lkcn bata koma aiki ba sun bata hutun wata daya ne, ta mike tsaye tana kallon Aneesar da mamaki tace "me ya faru Aneesah," Aneesah ta kirkiro murmushi don bata son daga ma Amminta hankali, suka shiga dakin snn tace "Ammi tun safe baki gama aikin ba ashe," Ammi tace "ki gaya min Aneesah me ya faru ga idanuwanki duk sun kumbura kice min bkm," Aneesah ta sunkuyar da kai gudun kar ta fara hawaye kuma, a hankali cikin nutsuwa tayi ma Amminta bayanin abinda ya faru, ammi tayi shiru tana kallnta da tausayi snn tace "shi kuma me ya biyo ki yi Aneesah," ta goge hawayen idonta tace "nima ban sani ba," Yana waje Ammi, Ammi tace "to shknn kice ya shigo," ta mike a sanyaye ta fita gidan tayi hanyar motarsa, tace "Ammina tace ka shigo," yyi murmushi ya fito daga motar ya rufe snn ya bi bayanta suka shiga gidan a tare. [9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 25..... Aneesah ta fara kkrin mikewa xaune, makwabciyarsu maman salim tayi saurin kamata tanai mata sannu, da kyar take bin dakin da kallo tana kkrin tunano abinda ya faru don kanta yyi mata nauyi sosae, a hankali komai ya dawo mata, murya can ciki ta kama hannun matar dake gabanta tana kkrin mikewa tsaye tace "ina yusuf," matar ta komar da ita ta xaunar tace "Haba Aneesah so kike ki daga ma Amminki hankali ne yusuf addu'a xakiyi masa kawae " Aneesah na jin hka ta fasa mata ihu a gigice tana girgixa ta tace "don Allah ku gaya min me ya sami yusuf dina," duk matan dakin suka yo kanta suna lallashi amma kamar ana sake tunxurata don ihu ta dinga masu tana kuka cikin daren har makwabta da yan unguwa sun fara shigowa, Ammi dae har lkcn tana xaune kan darduma tana nata