← Book details Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 58

Sashe 20

Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

pretty tace "lfya lau, ya su Ammi" Aneesah ta kalli Haydar tayi murmushi ta ce tana nn lfya, Haydar ya hada kudin gaba daya ya biya da na prettyn don ita ma ta gama siyayyanta snn suka fita ixuwa mota... Tare suka yi gidansu Aneesah da pretty, ta shiga ta gaida Ammi da yayanta, ita dae Aneesah bin ta kawae take da kallo, tana son yarinyar ssai, Ammi ta xuba masu abinci suka ci tare da ita, haydar kuwa yace ya koshi, sun jima suna hira daga bisanni yyi ma Ammi sallama yace xasu koma gida, Aneesah ta rakosu har bakin mota, ya fito mata da kayan shoppin din da yyi mata yana kallonta yace "no more gombe kina ji na," ita dae murmushi kawae tayi ta kauda kanta a xuciyarta tana cewa gombe kam dole naje sa, pretty ta shiga mota tana daga ma Aneesar hannu, haydar yace "yauwa baki bani Address din da na tambayeki ba Aneesah," tace "wae me xaka yi da Address din yayana," ya harareta yace "ina son nasan ko nasan anguwan ne," da kyar ta gaya masa Address din baffan nata, yyi mata sallama suka bar anguwar, ita kuma ta koma cikin gidan a sanyaye. Haydar yyi parkin dae dae kofar gidan Baffa yana kare ma gidan da anguwar kallo, sanye yake da suit baki har lkcn, ya kalli agogan hannunsa karfe biyar na yamma, ya karasa bakin gate din ya danna bell maigadi ya leko yana tambayar waye, a nutse Haiydar yace "nn ne gidan Alhaji shehu?" mai gadin yace "eh nn ne, akwae matsala ne, don baxa ka samu ganinsa ba ynxu bae jima da shigowa ba" Haydar yace "No ni wajen Abdul naxo ae yana ciki?" mai gadin yace "ko minti goma ba ayi da fitarsa ba sae dai in jiransa xaka yi a ciki," Haydar yace "eh ba matsala xan iya jiransa," mai gadin ya bude masa gate ya shiga gidan yana kare ma ko ina kallo yana murmushi har ya isa kofar shiga falon, ya tsaya ya danna bell, 'yar aiki ta taho da sauri ta bude kofar, yace "Alhaji shehu na ciki ko?" tace "eh amma hutawa yake yi," yace "kije kice masa ana nemansa urgently, a dan tsorace tace "A'a ni ba a bani ixinin hawa sama ba sae dae na kira maka kande, yace "to me kike jira," da sauri ta juya sae ga ta da kande, ya gaya ma kande abinda ya fada mata, ita ma a tsorace tace "aa ni iya ka ta kofar dakin Hajiya," cikin tsawa yace "eh kije kice da Hajiyar ana neman mijinta," ta dan koma baya tace "gskya baxan kuma hawa sama ba sae gobe don na gama duk ayyukana na yau," xae yi magana sae ga hajiya ta sauko, tana kallon yan aikin tace "me ya faru, wnn daga ina," kande ta durkusa da sauri tace "A'a ranki shi dde wnn bawan Allahn ne ke neman Alhaji wae," ta karaso cikin falon tace "akwae damuwa ne yaro?" Haydar yyi murmushi mai sauti yace "gun Alhaji shehu na xo," tace "in ji lfya" ya daga kafada yace "lfya lau, kan wani business ne," tayi murmushi tace "Ayyo xauna mana, bari na kirasa yana ciki," [9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 38...... Haiydar yyi murmushi ganin bata gane sa ba bayan ta bar falon xuwa kiran maigidan nata, bayan kmr minti biyar baffa ya sauko cikin bakar jallabiya, har lkcn Haiydar na tsaye a falon, ya karaso falon yana kallon Haiydar daga sama xuwa kasa yace "hw may i help yhu gentleman?" Haiydar ya gyara tsayuwa yana kallonsa da kyau yace "srry fa, hope am speakin 2 Alhaji Shehu," Baffa ya basa hannu yace "ehh ni ne, have a sit mana," Haiydar ya girgixa masa kai ya juya masa baya yace "ba xama ya kawo ni ba Alhaji Shehu, am barrister Aliyu muhammad," yana fadin hka ya juyo yana fuskantar baffan da dan fara'ar dake shimfide a fuskarsa ya bace da gudu, fuskarsa a daure yace "ehem hw may i help yhu? kana da matsala da ni ne?" Haydar ya girgixa kai a nutse yace "ko daya, i came on behalf of the late Alhaji mukhtar's family," baffa ya yo waje da tulelen idonsa a fusace yace "Alhaji mukhtar meye hadinka da mukhtar, da'alla malam fice min a gida, wnn ae xancen bnxa ne wae on behalf of Alhaji mukhtar, kasan alaka ta da mukhtar xaka xo kana gya min magana malam," Haiydar yyi murmushi mai sauti ya fito da takardar aljihunsa ya jefa ma baffan yace "gidaje biyar, motoci hudu, filaye hudu, 2 companies ba a maganar kudin da ya bari a acctn ma tukun, duk ka tattaro ka damka ma iyalansa nn da sati daya, if nt i will sue yhu, bnxa kawae jahili mara tunani masu cin haram" yana gama fadin hka ya juya yyi kofar fita, baffa ya bude baki yana kallonsa, dae dae bakin kofa Haydar ya juyo yana kallonsa yace "just a week," snn ya fice daga falon, baffa ya girgixa kai cikin tashin hankali ya shiga kwada ma matarsa kira, ta sauko da sauri tana tambayar lfya, me ya faru Alhaji, cikin in ina yace "wnn waye kika turo ni wajensa, kina da hankali kuwa, ni ni ya gaggaya wa magana hka ya fita, ta ina ya shigo gidan nn, yasan ko ni wanene ma kuwa" Hajia zuwaira ta rude tace "wllh ca nake business partner dinka ne Alhaji, mai yace maka?" baffa ya dinga kai komo a falon yana salati, "lallai sae nayi maganin tsinannun mutanen nn, nn ba da dde wa ba, ni xa su toxarta??" duk yanda Hajiya zuwaira ta so jin me bakon ya gaya ma mijin nata hkn bae yiwu ba don duk ya fita hayyacinsa, kira wnn a waya, kira wancan a waya, duk lauyoyinsa biyu sae da ya kirasu, daga karshe ya kira wani abokinsa Dpo, ita dae Hajiya duk inda yyi binsa take kawae a baya, gashi ya ki sauraranta, suna nan a wann hali Abdul ya shigo gidan a fusace, yana kiran abbansa, dad, dad, baffa ya juyo da jajayen idonsa yana kallonsa ba tare da ya amsa ba, "kana sane dae gobe ne daurin aurena da yarinyar nn ko?" Baffa yace "nonsense kasan tashin hankalin da nake ciki ynxu kuwa xaka min maganar auren wa inda suka sa ni cikin tashin hnkalin," cikin tsawa Abdul yace "ina ruwana da tashin hankalinka dad, ni kasan irin tashin hankalin da nake ciki, shit! dad wllh komai xae iya faruwa idan yarinyar nn bata xama matata gobe ba, idan ma kai baxa ka daura min auren ba sae na biya wani ya daura mana, wnn ae walakanci ne kke min dad" baffa ya xauna kan kujera ya dafe kansa yana girgixa kafa, Hajiya Zuwaira dae an sa ta a duhu ta rasa gane abinda ke faruwa, a nutse baffa ya shiga yi ma Abdul bayanin abinda Haydar ya xo yyi masa, Abdul yace "shit shine dad saurayin Aneesar ne, shine wanda nake gaya maka shekaranjiya, shine yyi min tijara daxu" Hajiya ta saki salati tana gwale ido tace "ban gane sa ba wllh Alhaji, ba ranar da naje gidan ba nima nace mka na ga wani a xaune a dakinsu, au shine ya xo yau, tab" abdul yyi tsaki yace "wnn duk ba matsalata bace dad, gobe nake son wnn mara kunyar yarinyar ta xama mata ta don na gwada mata hankali, period," yana kai wa nn ya haye sama yana huci. Baffa ya dafe kai yace "innalillahi wa inna ilai hi raji'un," Hajiya ta xube kan kujera tana kuka, baffa ya mike ya bar falon da sauri yana cewa "nasan abin da xanyi," Hajiya ta bisa da sauri ita ma. [9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 39..... Dai-dai bakin kofa Hajiya Zuwaira ta hadu da mai gidan nata yana kkrin fitowa daga dakinsa rike da makullin motarsa, da mamaki tana kallonsa tace "A'ah ina xuwa kuma Alhaji...." yyi saurin katseta ta hanyar daura yatsansa a baki yace "shhiii" alamar tayi shiru ta ja gefe ya fito daga dakin kmr mara gskya yana kallon kofar dakin Abdul, ya dan yi gyaran murya yace "guy kayi bacci ne!" duk da idon Abdul biyu bae tanka masa ba, baffa ya karasa har bakin kofar dakin ya tura kofar yana kallon cikin dakin, ya ga Abdul din xaune yana xugar taba, ga wine mai sanyi a gabansa, baffa yyi murmushi yace "ashe dae baka yi bacci ba, wae da fa fita xa muyi guy!" Abdul ya juyo da jajayen idonsa yana kallon uban nasa a walakance yace "mu fita muje ina?" baffa yace " No Alhaji kasim ne ya kira ni gidansa ba lafiya shine xan je ynxu," Abdul yyi tsaki yace "shine xan bi ka" baffa yyi murmushi mai sauti yace "mai da wukar Angon gobe, bari naje ynxun nn xan dawo muyi maganar yanda shirye shiryen bikin xae kasance gobe," Abdul yace "A'a ana daura auren a bani matata na tafi da ita kawae bbu wani bikin da xa ayi," " baffa yace "an gama guy, bari naje na dawo" snn yyi masa sallama ya fice Hajiya Zuwaira da hankalinta ya gama tashi jin mijin nata na xancen auren dan ta da Aneesah gobe, ta dinga binsa a baya har suka sauka kasa snn ta fashe da kuka ynxu Alhaji da gske aura masa shegiyar yarinyar nn xaka yi, yyi mata wani mugun kallo yace "da yake na ce maki mahaukaciya ce ta haifeni ba, ni shehu na hada zuri'a da tsinannun mutanen nan baki san ni bane Zuwaira, look ba lallai bne na dawo yau har sae na idda abinda na fita yi, kiyi min addu'a kawae kuma bana son Abdul ya gane ban kwana gida ba, be vry watchful," yana kai wa nn ya fice yana kiran driver a waya, ta bi shi da Allah ya kiyaye xuciyarta ya dan yi sanyi sanin mijin nata shaidanin gske ne. Kofar gidansu Aneesah drivern baffa yyi parkin dinsa, ya fito yana kallon agogo karfe goma da rabi na dare, yace ma drivern gashi nn fitowa ynxun nn snn ya shige gidan. Like · 9 · Report · 26 minutes ago [9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By
Chapter 20 · 0% Book details