Sashe 21
Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khaleesah Haiydar 41..... A tsorace Aneesah ta farka ta dalilin buga kujeran bayan motar da Driver ya dinga yi da nufin tada ta, ta fara waige waigen cikin motar xuciyarta na bugawa, xata tambaye Drivern ina ne nn suka kawota, baffa ya xagayo bayan motar a fusace yana cewa "kin fitowa tayi don ubanta," da sauri ta fito daga motar gabanta na faduwa daga ita sae dankwali tana kare ma inda suke kallo, ko ina tsit sae ciyawa dake ta bow down wa iskan dake ta kada su, ga uban duhu, crow din cock da ta dinga ji ne yasa ta gane Asuba tayi, cikin tasin hankali ta shiga tambayar kanta ina ne nn kuma baffa ya kawo ta, tsawarsa ta tsinta a tsakiyar kanta yana cewa "duk inda na bi ki bi, idan ba hka ba xan wurga ki cikin dajin can na bae ma macixae sadakar ki, kae kuma saleh ka jirani daga nn, ba jima wa xanyi ba," yana fadin hka ya bi ta dan wani hanya duk ciyawa, Aneesah ta bi sa a baya tana hawaye, da taimakn hasken wayar sa suka dinga ratsa grasses din wajajen ga hanyar duk cabi da ruwa, har suka bullo wata hanyar daban da karamar abun hawa xata iya bi, tafiya yake kmr xae tashi sama yana yi yana waiga bayansa ya tabbatar tana biye dashi, ita ko binsa kawae take tana hawayen tsoro, sun kusa minti talatin suna tafiya har daga karshe taga sun shigo wani dan karamin gari, abinda Aneesah ta fara cin karo da shine bukkokin mutane, abun yyi mugun daure mata kai ko ba a fada mata ba tasan kauye ne nn, hka Aneesah ta dinga binsa a baya har daga karshe taga sunyi fullstop a dai-dai wani katon bishiya duk bawon rake a watse a kar kashinta, ya juya fuskarsa daure yana kallonta yace "ki jira ni a nn," kai ta gyada masa taga yyi wata 'yar hanya, ta fashe da kuka abun tausayi, to ita ynxu ya xata yi ita ba wae tasan guri bane bare ta gudu ga ko ina duhu, ta fara waige waige tana nema ma kanta solution kafin baffan ya dawo sae ko gashi da wani mutum sun dawo gabanta yyi mugun faduwa har suka karaso, mutumin yace "to ku shigo daga ciki mana Alhaji, ashe xaka tuna dani Alhaji gaskiya naji ddi sosae," baffa ya kalli Aneesar yace "maxa ki biyo mu a baya," hka ta dinga binsu a baya har suka shigo wani dan gida da bukka guda uku, cikin tsawa baffa yace ta tsaya daga bakin kofa snn suka karasa cikin gidan da tsohon mutumin, baffa yace "ina mai dakin naka mati," mutumin da xa su xo sa'anni da baffa yace "bari na tado ta Alhaji tana ciki ai," da sauri ya shiga sae gashi sun fito tare tana mitsika ido tace "wanga ai walakanci ne malam, me ya faru xaka tado ni cikin sanyin nn," yana wage baki yace "ke shatu Alhaji shehu ne a kauyan namu yau," ta bude ido da sauri tana kallon baffa tace "lah Alhajin Allah ashe baka manta mu ba, sae ta fashe da dariya tana cewa ikon Allah, sannu da xuwa Alhaji amma da asuban nn me ke tafe da kai hka," baffa dake dan murmushi yana sosa keya yace "A'a wnn yarinyar na kawo ku taimaka min ku riketa amma ba amana ba, don 'yar iskar kanta ce, karuwanci take a birni wllh, mun rasa yanda xamuyi da ita 'yar wata abokina na kut da kut ne, ga ta nn nasan shatu ke ce maganinta, idan Allah yasa ta samu mijin da xae jajuban ma kansa wahala ku aurar da ita kawae ko sadaka ce, nasan baxa ta taba gane hanyar fita daga kauyen nn ba bare ta gane hanyar komawa gida, kar ku sake tayi kawaye ni dae ynxu tamkar na kawo maku baiwa ne, dan tallan nn da aikace aikace duk ta iya xata maku, kuma nn ba da ddewa ba nke son ku bada sadakarta ga duk mai so," yana kai wa nn ya ciro duba daddaya har ashirin ya mika ma mati da ya xube har kasa yana gdya "an gama Alhaji in'sha Allahu duk yanda kace hka xa ayi," shatu tayi wani shegen dariya irin tasu ta 'yan kauye tace "ka xo inda xa a share maka kukan ka Alhajin Allah, ka manta mu su waye ne, ka kwantar da hankalinka kawae Alhaji kar ka samu damuwa," baffa yyi dariya sosae yace "ae na yarda daku, ni ynxu xan koma driver na can bakin hanya yana jirana don ma kar ta gane hanyar fita yasa ban bari muka shigo ciki da motar ba, na dinga ratsawa da ita ta daji, cikin ikon Allah kuwa muka iso nn," suka yi dariya suka rakasa har bakin kofa suna masa Allah ya kiyaye hade da gdya, har lkcn Aneesah na bakin kofar shigowa gidan tunda baffa bae ce ta shigo ba, tana ganin su ta ja gefe gabanta na faduwa, cikin tsawa shatu tace "kya tsaya kina rabe rabe bakin kofa kmr warce bata san duniya ba shegiya, da'alla shiga daga ciki ki tsaya," jikinta na bari ta shiga gidan tana kallon baffa, kar dae tafiya xae yi ya barta, nn suka yi ma baffa dake ta washe baki ganin har shatu ta fara aikinta sallama, yyi masu sallama cike da farin ciki ya bi hanyar da xae sada sa da bakin hanya xuciyarsa fari kal. Mati shaidanin mutum ne da yyi ma baffa aiki a birni da ddewa, aikinsa kuma baya wuce kashe wancan binne wancan kamo wancan, nemansa da ake ruwa a jalo a Abujan ne dalilin da yasa ya dawo kauye da xama da karuwar matarsa da 'ya yansu biyu zano da xulai. [9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 40..... Aneesah na kwance bayan ta ci kukanta ta koshi tana ta kallon Amminta dake ta faman har hada mata kayanta don gobe xata wuce gombe wae, ta kauda kanta a hankali wata xuciyar na ce mata tafiyarki gombe shine kadae kwanciyar hankalinki, da ta tuna abinda Abdul ya xo yyi masu daxu da maghrib sae ranta yyi mugun bacewa, ta tsani Abdul ta tsane sa, da ta auri Abdul gwara ta shiga duniya ita kam, sam bata dace da shi ba, to idan da gske ne kmr yanda ya fada masu gobe ne daurin aurenta dashi ya xata yi, ohh da shiknn karshen rayuwarta ta xo, ko da yake ae gobe da asuba xata bar garin Abuja idan Allah ya yrda, tayi assure din kanta, hakan ya kara sa taji hankalinta ya kwanta ta samu kwarin gwiwa, damuwar ta daya basu yi sallama da ya Haiydar ba, ynxu sae dae ya xo ya ga ba ta, hkn yasa taji hawaye ya silalo gefen idonta, ta mike xaune a hankali ta goge idonta, Ammi bata ko kalleta ba tana ta faman hada kaya abun ta, Aneesah xata yi magana knn suka ji an banko kofar xaure da karfi aka shigo gidan, duk suka tsaya kallon juna har baffa ya turo kofar dakin yana huci yace, "maryam, maryam ina tsinanniyar 'yar nn take, maxa maxa ta tattaro kayanta ta fito daga gidan nn kar na balla ta, don na gaji da abun kunyar da kuke janyo mana a gari ko kuma nace kuke janyo min tunda shi ibrahim ba a nn yake ba, maxa ta fito da jakar kayanta bata sake xama a gidan nn," cikin tsawa yake maganr yana nuna Aneesah da ke xaune dakin tana kallonsa da mamaki, Ammi tace "kmr ya abin kunya baffa, wani abun tayi ko kuma....." ya daka mata wani mugun tsawa yace "ki rufe min baki bnxa dake kawae, nace fateema ta tattaro kayanta ta fito daga gidan nn ynxun nn ina tsaye idan ba hka ba wllh wllh xa ku sha mamaki na ynxun nn, matsiyatan bnxa kawae" kuka Aneesah ta fashe da tace "wllh bbu inda xan je daga nn Ammi," ya shigo dakin a fusace har yana neman faduwa ya gaura mata mari mai lafiya, "don ubanki tashi, tashi, nace ki tashi," ya fixgota da karfi, ta fixge hannunta tana kuka tace "wllh bbu inda xani ka kyaleni," ya fita a fusace sae ga shi ya dawo da icce, Ammi dake xaune ta kasa cewa komai sae hawayen da take yi ba kakkauta wa ta mike da sauri ta shiga tsakaninsu, "kar ka dukan min 'ya baffa, ina xaka kai ta da daren nn da xata hada kayanta?" yana huci ya nuna ammi da dan yatsa yace "ke,,, ke maryam ki fita idona kar na watsa maki mari munafuka kawae makira, maxa ta fito da kayanta yau kafata kafarta wllh wllh," Hka baffa ya dinga masu tijara daren ranar yana neman dukan Aneesar da bakinta ya ki mutuwa, Ammi tana kuka tace ta bi shi amma Aneesah tace bbu inda xata ita kam, da kyar Ammi ta lallabata ta hada ta da kayanta da take hadawa tace ta bishi, kuka Aneesah take kmr ranta xae fita hka baffa ya ja ta, yana rike da jakan kayan nata dayan hannunsa, ya wurga ta cikin mota da jakar tata, yace driver ya kula da ita kar ta fita snn ya koma cikin gidan yana huci, ya ciro dubu biyu ya jefa ma Ammi yace "ke ma maxa maxa gobe ki kama hanyar gombe da asuba don baxan tsaya da ku a garin nn ba ana nuna ni da dan yatsa, maxa ki tattara komatsan ki kiyi kauyenku kar naxo na tarar dake nn gobe," yana kai wa nn ya fice daga gidan ya shiga mota, driver na ta kokuwa da Aneesah dake neman ficewa daga motar ta karfin tsiya, baffa ya koma da sauri ya dauko iccen daxu ya dawo motar, Aneesah na ganin iccen ta fasa ihu "don Allah baffa kayi hkuri wllh na tsaya, wllh nayi shiru, ya kwale mata a ka yace "don ubanki da ke kabari ma kiyi mana," tsit tayi tana ajiyar xuciya a motar, ya shiga gaban mota driver ya ja suka bar anguwar suna hawa titi yace da driver ya shiga gidan mai xa su cika tanki, hka ko drivern yyi aka cika tankin motar snn baffa ya biya suka