← Book details Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 58

Sashe 3

Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya sani. Washegari laraba tun da sassafe Ammi ta fita xuwa gun wata hajiya xulfa da suke mutunci da, ta yi mata jagoran sama ma Aneesah inda xata dinga yin aiki don tana hulda da masu kudin cikin gari sosae kuma tana yawan kai masu 'yan aiki, karfe shidda na yamma Ammi ta dawo gidan a gajiye, Aneesah ta fito mata da kujera snn ta kawo mata ruwan sha a kofi, bayan ta sha take tambayar jikin yusuf Aneesah tace da sauki sosai don har ya fita wasa, sae da ta bar Ammi ta huta snn murya can kasa tace "Ammi ya hanya," Ammi tace "lfya lau, na samu inda xaki dinga aikin da kyar Aneesah, amma sae dae matar bata da mutunci ko kadan, bana tunanin xaki iya Aneesah barin ma ke da baki da hkuri, snn irin aikin da ta lissafo gskya bana jin xaki iya su sun maki yawa Aneesah, ki hkura kawae idan Allah yasa wataran Hajiya xulfa ta sake samun wani wurin aikin sae ki fara," Aneesah tace "haba Ammi ni wllh koma meye ni xan iya aikin nn, don Allah ki barni na fara kawae Ammi, nayi maki alkawarin baxan baki kunya ba kinji Ammina, " Ammi tayi shiru tana kallonta, can tace "shknn to Allah ya kai mu gobe," Aneesah tace "Ameen," cike da murna da jin ddi don ita so kawae take ta xana jarabawarta wnn shekaran da yardar Allah. Karfe goma da rabi Aneesah da Amminta suka isa kantamemen gidan da xata fara aiki a cikin garin Abuja, jikin Aneesah yyi sanyi sosai ganin gidan bana wasa bne don gidan ya hadu iyakar hadewa ga anguwar ma kadai abun kallone, maigadi da uniform din soja a jikinsa ya bude masu gate fuskarsa a tsuke yace "ku ne bakin da Hajiya tace xa su xo," Ammi tace "eh mune," ya nuna masu daga kusa da wani flower yace "to ku tsaya can tace ku jira ta a nn," Ammi tace "to snn suka dawo gefen shukan suka tsaya, Aneesah ta dinga masa wani irin kallo cike da jin haushin yanda yake masu maganar," yaje ya ba yaran gidan sako suce ma Hajiya masu aikin sun xo snn ya dawo bakin gate ya tsaya, Aneesah sun fi awa daya a tsaye wajen ga rana bbu hajiya bbu lbrinta, har sun firda ran fitowarta Ammi tace "muje kawae Aneesah," sae ga ta ta fito cikin shiga ta alfarma sanye da glass sae kamshi take a girme xata girme ma Ammi sosae ba kadan ba, ta dinga taku kmr baxata taka kasa ba ta iso kusa dasu tana masu wani irin kallon raini cikin isa da gadara tace "ina 'yar aikin," Ammi ta kasa cewa komai, sae Aneesah ce tace "gani," matar ta bude baki da dan mamaki tace, "wnn kwailar wani aiki xata iya hka, na yi xaton wata babba balagaggiya xaki kawo min malama," Aneesah ta dake tace "bbu abinda bana yi Hajiya, tun daga kan shara, wanke wanke, goge goge, girke girke, da duk aikin da kika sani Hajiya," Hajiyar ta tabe baki tace "yyi, duk wata dubu goma sha biyu nace xan dinga badawa kuma idan washing machine ya wanke ma babies dina kaya yau to gobe ita xata wanke masu, snn tun karfe bakwae xata xo aiki ta bar min gidana karfe shidda na yamma, ina fatan ku ba fulanin daji bne kun fahimce ni," Ammi tayi murmushi tace "mun fahimce ki Hajiya mun gode, amma karfe shiddan da kika ce Hajiya yyi dare don gidanmu da nisa sosai, ki rage kudin aikin in yaso sae ta dinga barin nn ko xuwa karfe biyar ne," hajiyar tayi masu wani kallo ta tabe baki tace "karfe biyar da rabi xata dinga barin nn period, idan hkn yyi maku to ta fara aiki daga dis vry moment, idan kuma bai maku ba ku ja tsumman rayuwarku ku fice min daga gida don ni bna kai wa wnn lkcn ina surutu da yan aiki talakawa irin ku," tana kaiwa nn ta juya ta shiga takunta cikin isa har ta hau balcony ta shige falo... [9:29PM, 12/21/2016] Khaleesat: 8...... Sumy ta mike da mamaki tana kallon yayarta Meenah don ita tsakani da Allah tayi maganarta ba wae don su yi fada ba, pretty tace "sumy ke kika fara neman tsokan gskya meye xaki hadata da wata banxa can kuma ma 'yar aiki, wae ta fita kyau" Meenah tace "ki kyaleni da 'yar walakanci kawae na faffasa mata baki ynxun nn....." ganin abun nasu na son ya xama fada sosai don sumy har ta fara kkrin cakumo yayartata tana cewa "to ki fasa min bakin kiga idan ban cire maki hkora ba ynxun nn nima," yasa Hajiya ta shige tsakaninsu da sauri tana basu hkuri, "haba bbies dina meye abun fada a nn iyye, kema sumy baki kyauta ba don me xaki ce wata tsinanniya can ta fi yayarki kyau idan ba tsokana ba," ta juyo tana kallon meenar tace "manta da ita meenah xolayarki take kinji, kuma ku kwantar da hankalinki indae mayyar 'yar nn ce wllh watan nn na kai wa karshe xan sallameta, ita wacece da xata dinga gasar kyau da daughters dina, ku kyaleni da shegiyar kawae kuje kuyi shirin birthday din da xaku kar lkci ya wuce," a hka ta lallaba 'ya yan nata suka hkura suka haye sama pretty na cewa "Allah ma yasa ba yau bne karshen xuwa partynmu" sumy tayi dariya tace "kuma fa hka ne wllh," hajiya tayi jigum tana tunani bayan tafiyar 'ya yan nata, ita kanta kyan Aneesah mamaki yake bata wani lkcn, yarinya hka sae kace aljana don kyau, anya ba plan aka yi mata da yarinyar nn ba kmr yanda su pretty suka ce ba, amma ta kusa kawo karshen komai idan Allah ya yarda wnn watan ne watanta na karshe a gidan taje can ta samu wani gidan tayi masu aikin ita kam ta yafe duk da ta san yarinyar ta iya aiki sosai uwa uba ga iya girki da tsafta, ta tabe baki a xuciyarta tace na sa a kawo mani wata balagaggiyar mummuna hankalina a kwance na 'ya yana a kwance, ta sake kwado ma Aneesahn dake tsaye a kitchen ta gama dukka aikinta na ranar amma tana tsoran tunkarata tace xata wuce, ta fito da sauri har tana tuntube ta durkushe gabanta tace "gani Hajiya," Hajiyar ta tabe baki tana hararta kmr xata makureta don tsana tace "idan kin ga dama gobe ki taho da Asuba don xaki hada ma son dina da xae dawo daga holland goben girki lafiyayyu, xakiyi masa fried rice da plantain kadan, sae farfesun kayan ciki da kaxa, snn ki hada masa cream salad, sae kuma kiyi masa cous-cous da miyar kwae, snn finally ki hada masa ginger drink mai kyau, daughters dina kuma kiyi masu jollof din taliya da naman rago da dan farfesun fish don sun fi son shi, ina fatan dae yhu re nt daft duk kin fahimce ni," Aneesah tace "nafahimta Hajiya," Hajiyar tace "tashi ki bani waje to, idan kinga dama karki xo da wuri ki ga rashin mutunci," Aneesah ta mike a sanyaye tayi mata sae da safe ta bar gidan [9:29PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By khaleesah Haiydar 7.... Ammi ta girgixa kai a hankali tace "baxa ki iya ba Aneesah muje kawae," Aneesah ta xame hannunta a hankali daga rikon da Amminta tayi mata tace "xan iya Ammi, ki tafi gida kawae sae na dawo," bata jira abinda Ammi xata ce ba tayi saurin barin wajen ta bi kofar da Hajiyar ta bi ta shige cikin gidan tana karanto Addu'o'i cikin xuciyarta, ta ga kanta a wani makeken falon gske mai cike da kayan alatu da kayan more rayuwa " ya salam! Aljannar duniya knn," ta dinga bin falon da kallo a hankali gabanta na faduwa sae kace ba Nigeria ba, wnn wani irin aiki suke yi hka, gskya wasu kam sun more duniya, ta rasa inda xata bi don falon ba kowa sae karar Ac da wani ni'imantattcen kamshi dake tashi, ta kai minti kusan goma a tsaye tana naxarin komai na falon duk da wasu tana ganinsu falon baffanta, taji ana taka matakalan bene a hankali ana saukowa ta tsura ma stairs din ido tana jiran taga ko Hajiyar ce ke sauko wa, wata kakkyawar yarinya da baxa ta wuce ta ba ce ta sauko tana sanye da kayan bacci, yarinyar ta mitsike ido tana kallonta da mamaki, Aneesah ta kauda kanta, yarinyar cikin gadara tace "who re yhu," Aneesah tayi shiru bata ce mata komai ba sae wani irin kallo ma da take ma yarinya, yarinyar ta juya da sauri ta koma sama, sae ga ta ta dawo da momynta, Hajiyar tace "ohh House Maid dinmu ce pretty," Hajiya ta karaso kasa a walakance tace "bbyna xata xaga dake ko ina na gidan ta nuna maki duk aikin da xaki dinga yi, sae ki fara daga ynxu," ta kira prettyn tace "sauko bby ki nuna mata House chores din gaba daya," yarinyar ta sauko tana yatsine fuska tace "momy ni kayana xata fara wanke min kafin ta fara komai, don ni ynxu na daina gane wankin washin machine din nn, shi kuma iliya baya wanke min da kyau gugan ma na Hauka yake min," Hajiya tace "to maxa ki fito mata da kayayyakin taje bakin tap a kusa da garden ta wanke, ki hado mata da na sumy don naga kmr tana da kayan wanki ita ma," prettyn tace "na meenah fa," Hajiyar tace "A'a kinsan halinta tana iya cewa bata samu ba, kwaso mata naku dae kawae," prettyn ta juya da sauri ta haye sama, Aneesah dae binsu da kallo kawae take. Hajiya ma ta juya ta haye sama, bayan kmr minti goma sae ga prettyn da tulin kayan wanki ta watsa mata su a gabanta, Aneesah ta dinga bin kayan da kallo, cikin gadara prettyn tace "kuma yarinya ki tabbatar kin wanke mana kayanmu da kyau, suna bushewa kuma ki goge mana su, snn karki kuskura ki hada min fararen kayana da wasu kayan don idan suka dafe wllh sae kin siya min sabo," ta juya tana tana karkade jiki ta haye sama. Aneesah tace "hmm, ikon Allah," ta girgixa kai
Chapter 3 · 0% Book details