← Book details Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 58

Sashe 2

Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

aiki a House of Assembly Abuja. [9:29PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ 4..... Sallamar wata makwabciyarsu ne ya sanya Aneesah ta dago tana goge fuskarta, ta karaso cikin gidan Aneesah ta gaida ta ta amsa tana tambayrta ya karatu, ta shiga dakin ta gaida Ammi snn ta ajiye kwano tace "gashi a ba yusuf ya kara Ammi, bbu yawa," Ammi tayi mata godiya tana tambayrta danta umar, tace "yana can waje suna wasa" snn ta fice. Ammi ta jawo kwanon ta bude taga dumamen tuwo ne, tasan kila yusuf yace mata yana jin yunwa ne shine ta kawo abincin don matar tana da kirki sosae duk da su ma manage suke don sae mijinta ya fita yyi shoe maker snn suke samun abinda xasu ci suma , ta kira Aneesan su xo su ci, bakin ciki da takaici yasa taji ta daina jin yunwan ma kwata kwata tace bata ci, da kyar Ammi ta lallabata ta ci dn tasan halinta. Karfe sha biyu saura Ammi ta fito da dinkekken atamfarta da kakarta ta aiko mata da wani sllh, Aneesah ta tambayeta inda xata da shi ganin tayi shirin fita ne, Ammi tace "xan je kasuwa ne na sayar Aneesah kafin su Hajiya salamatu su dawo," Aneesah tace "haba Ammi ke knn kullum sayar da xani don Allah don annabi," Ammi tace "to meye amfaninsu Aneesah," ki kula da yusuf kafin na dawo don daga can xan siyo abinda ya sauwaka na abinci," bata jira cewar Aneesahn ba ta fita daga gidan. Tana tsaye bakin kofar dakinsu bayan ta gama shirin boko, yusuf yace "Anty mu wuce kar su Jamila da khabir su ruga mu yau ma," Aneesah ta jawo sa tace "kasan me yusuf, maxa ka bisu ni ina nn xuwa kaji," bae yi mata musu ba ya fice daga gidan, Ammi tace "to ke me kike jira Aneesah," Aneesah ta shigo cikin dakin ta xauna tana kallon Amminta tace "kudin waec nd Neco Ammi, kuma ance kar mu xo yau idan har mun san xa muyi kuma bamu kawo kudi ba," Ammi ta tsura mata ido tana kallonta tace "to yaushe ma ya bada kudin makarantar da har xa'a tunkaresa da wani kudin waec, amma dae ki shirya kije ki samesa ki gaya masa ynxu kila Allah ya daura ki a kansa Aneesah" Aneesah ta hade rai, can ta tabe baki tace "bbu inda xanje Ammi, gwara kar na sake xuwa makarantar ma kwata kwata," Ammi ta galla mata harara tace "to ki xauna," Aneesahn tace "to wnn mutum ne Ammi, ko fa naje ba bani xae yi ba sae dae ya walakanta ni ma, ba gwara kawae kar naje ba," Ammi tace "ko ma de mae xaki ce, yayan babanki ne, baffanki ne dn hka ki iya bakin ki, kuma ki tashi ki shirya ki tafi kafin ya fita," ta mike jikinta a mace ta tube uniform dinta, ta dauki wani material dinta ashe da maroon ta saka, duk da talaucinsu in ta fita baka taba cewa tana cikin wahala don kullum fes xaka ganta. Ammi ta bata kudin motar tace ta barshi kawae xata taka, dole ta tilasta ta ta amshi kudin dn can cikin gari xata da nisa sosai. Aneesah na isa gidan baffan nata ta danna kararrawa daga waje mai gadi ya leko ta gaishe shi ya bude mata gate din ta shigo, ta tambayesa ko kawunta na ciki yace eh, da kyar gabanta na faduwa ta shiga gidan da sallamarta ta gaida 'yan aikin dake ta harkar gabansu a gidan, snn ta karasa cikin falon ta xauna kasan tiles tana jiran fitowar baffan nata. Like · Report · 4 minutes ago [9:29PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ 5...... Aneesah ta kusan minti ashirin xaune a falon kafin baffan nata ya fito cikin shiga ta shadda green colour sae walkiya yake, ga kamshin turare ya baxa ko ina, yana ganinta ko ya hade rai cikin daga murya yace "dama kece ki ke nemana wae?" ta sunkuyar da kai tace "eh nice ina kwana baffa," ya amsa a dakile snn yace "lfya da sassafen nn hka," tace "A'a dama kudin waec da Neco ne aka fara karba a schl, shine naxo na gya mka don sun ce kar mu xo yau ma," sae da ya saurareta ta kai aya snn ya daka mata wani mugun tsawa yace "don uwarki ca nayi maki ina da kudi ynxu da har xaki xo da sassafe karban kudin waec da Neco, kin bani ajiya ne ko uwar taki da ta aiko ki ta bani," ta girgixa kai tace "naga dae Baffa ba mu da wanda xamu tambaya bayan kai, kuma in ma hka ne ni fa ba kudinka nace ka bani ba, daga cikin kudin mahaifina xaka bani naje na biya abinda xan biya, kace sae mun mallake hankalin kanmu Baffa to ni dae na mallaki hankalina, a raba mana gadon mu kawae ka huta da tambayarka kudi ko makamancinsa da muke yi" tun da ta fara magana ya bude baki kmr soko cike da mamaki yana kallonta, tana gama fadin abinda xata fadi ya daka mata tsawa yace "ohho dama rashin kunya uwar taki ta turo ki kiyi min fateema, ni kike gaya ma wa innan maganganun don baki da kunya" ya saka salati yana jijjiga kansa yana kallon ceilin, ta dan tabe bki tace "ni fa ba rashin kunya nayi mka ba baffa" "to wllh wllh kinji rantsuwar musulmi ko, daga yau xuwa makarantarki ta kare, don aurar dake xayi don ubanki, kuma daga yau ko tsinke na ya daina shiga hannunku, shi uban naki da yake da rai uban me ya tsinana ma mutane sae uban rowa duk dukiyar da Allah ya basa, don uwarki duk hidimar da na ke maku har ixuwa yau da kudina nace maku ina maku, ai ki bar ma maganar gado don ko dubu dari bae rage cikin accnt din ubanki ba, duk kun cinyesu," ta mike tana yi masa wani irin kallo snn tace " lbri ma knn, shi kuma wnn gidan da kke ciki da sauran gidajensa da motocinsa fa ba a mayi maganar filaye ba, idan ma kace mun cinye kudin acc, ae wa innan suna nn baffa," ya kwasheta da wani gigitattcen mari yana huci "ni kke gaya ma wnn maganar," dae dae nn matarsa hajiya zuwaira ta fito da sauri, tace "me ya faru Alhaji, me ya kawo wnn kuma da sassafen nn," cikin in ina don ransa yyi mugun baci ya shiga yi mata bayani, Aneesah dae na tsaye dafe da kuncinta tana kallonsu, matar tasa bata bari ya kai aya ba tayi cikin kitchen da sauri tana cewa "ka kyaleni da shegiyar Alhaji," Aneesah na jin hka ta fice daga gidan da gudu don tasan matar bata da mutunci, bata manta randa ta biyo ta da yaji ba, yau kuma bata jira ganin me xata je daukowa ba ta yi ta kanta, tana barin anguwan ta dinga kuka a hanya tana bakin cikin wnn rayuwa irin tasu, da kyar ta isa gida don har wani jiri take ji dn yunwa dama koko kadae tasha da safe. Ammi ta mike da sauri tana kallonta tace "ya akayi kika dde Aneesah, me ya sa ki kuka," ta girgixa mata kai tace "ban samu ganinsa da wuri ba ne Ammi," sae da ta nutsu snn tayi ma Amminta bayanin duk yanda suka yi da baffan nata, Ammi ta dinga mata fada kmr xata mareta wae tayi ma baffanta fitsara ita dai shiru tayi bata ce komai ba har Ammi ta gaji tayi shiru, sae a nn ta shiga bata hkuri tana kuka, Ammi ta goge hawayen fuskarta don ita ma kukan take tace "kinga kin ma kanki Aneesah, ynxu xaman gidan kika fi so," Aneesah tace "dama Ammi ni banga alamar xae biya min ba fa," Ammi tace "to shknn Aneesah," Aneesah tayi shiru kmr mai naxari snn tace "Ammi kinsan mene," Ammi ta girgixa mata kai tace "me", ta dan kwantar da murya tace "don Allah Ammi ki sama min inda xan dinga aiki ana biyana sae na tara kudin waec din ta hka, tunda naga sae nn da wata uku xa a xana waec din," Ammi ta galla mata harara tace "kina da hankali kuwa Aneesah," ta yi narai narai da ido tace "kiyi hkuri Ammi, amma hkn shine kadae mafitar mu" Ammi tace "baxae yiwu ba, sae dae kijira har wani shekaran sae ki xana abinki idan Allah ya hore mana," Aneesah ta fashe da kuka tace "haba Ammi, to meye a ciki don nayi aiki, mu fa ynxu bamu da gata sae na Allah, don Allah ki bar koma wani tunani kike yi Ammi kin manta ko wacece Aneesah ne Ammi, wllh xan tsare kaina baxan taba baki kunya ba, ki tausaya min ki bari na tara kudin jarabawa na don Allah Ammi," tana magana ne tana kuka, Ammin ma kuka take, ta rasa abinda xata ce ma 'yar tata, can dae tace "shknn Aneesah ki bari nayi tunani da kyau kar mu janyo ma kanmu xagi a gari," Aneesah tace "to shknn Ammi," snn ta mike a sanyaye ta bar dakin taje debo ruwa a waje don ba ruwa a gidan. Like · 3 · Report · 1 hour ago [9:29PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ 6...... Bayan kwana biyu Aneesah na xaune gaban Ammi dake rungume da yusuf baya jin ddi tana basa ruwan tea, Aneesah ta kirata a hnkli tana kallonta, Ammi ta dago tace "meyafaru Aneesah," Aneesah ta sunkuyar da kai murya a raunane ta fara magana "Ammi har ynxu baki sake cewa komai kan maganar da muka yi dake ba, kince xaki yi tunani, don Allah Ammi ki bar ni na fara aiki, hkn xae taimaka mana sosai, gashi ynxu ko kudin da xa mu kai yusuf asibiti bbu" Ammi tayi shiru bata ce komai ba tana ta lallaba yusuf ya sha ruwan tean, hkn yasa Aneesah ta fara hawaye, Ammi ta dago kai tana kallonta, "meye na kuka Aneesah," Aneesa ta girgixa kai cikin kuka tace "to kin ki cewa komai Ammi," Ammi ta sauke ajiyar xuciya ta gyada mata kai tace "naji Aneesah," bata sake cewa komai ba daga nn, Aneesah ma tayi shiru tana tunanin wani irin rayuwace wnn da kowa kansa
Chapter 2 · 0% Book details