← Book details Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 58

Sashe 14

Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta mike da kyar tana goge hawayen da ya ki tsaya mata ta shiga gidan kafin hajiya ta fara kwala mata kira tana nemanta. Har Aneesah ta bar gidan ranar bata ga Haiydar ba, da kyar ta isa gida ta tarda jikin Ammi yyi sauki don har ta gyara gidan tayi masu girki, wanka da Alwala kadae ta iya yi ta kwanta don kasa sallahn tayi ammi tace ta sa kaya su tafi Asibiti amma tace aa don sanin kanta ne kudi kadan ya rage a hannunsu ynxu kafin karshen wata a biya su, Ammi ta fita siyo mata magani a chemist suka shigo tare da yusuf ya dawo daga makaranta, ya xube jikinta yace "Antyna baki da lfya har ynxu," ta gyada masa kai da kyar, yace "to Anty idan na girma xan xama Doctor don na dinga baki magani idan baki da lfya ke da Ammina" Aneesah ta mike da sauri tace "A'a lawyer xaka xama yusuf don ka dinga kare ryt din mutane," ya mike tsaye da sauri yace "A'a na manta Anty soja xan xama don na kama baffa na dauresa nae ta dukansa na sa shi frog jump idan ya sake yi ma Ammi da ke ihu, kuma xan xama mai kudi na siya maku gida na dinga baku abinci kullum" Aneesah ta dinga dariya ta rungumosa tace "yauwa yusuf dina shi yasa nake son ka, Allah ya bar mu tare," Ammi ta dinga murmushi tana kallonsu, nn da nn Aneesah ta nemi xaxxabinta ta rasa, hka suka dinga hira yusuf na basu dariya da shirmensa har dare ya raba snn suka kwanta. Washegari Aneesah ta tashi da karfinta taji bbu wani sauran xaxxabi a tattare da ita, ta kama hanyar gidan aikinta bayan ta ajiye yusuf a sch, don ca yyi ita xata kai sa ranar baxae bi su jamia ba, hkn yasa ta fara ajiyesa bakin gate tayi peck dinsa tayi masa bye bye snn ta tafi gidan aikinta, har kusan rana bata ga Haiydar ba, da yake duk 'yan gidan sun tafi gantali daga ita sae pretty a gida tana tae mata hira, karfe hudu saura tana wanke wanke kafin 'yan gidan su dawo pretty na sama taji wani mugun xaxxabi na neman rufeta, ta dinga ganin jiri ga ciwon kai da ya sa ta kasa bude idonta, ta gama wanke wanken da kyar ta shiga garden ta xauna ta jingina jikin bango tana mayar da numfashi, a hka Haiydar ya xo ya sameta a garden din ya durkusa gabanta ba tare da ya bari sun hada ido ba yace "har ynxu jikin ne kanwata," bata ce masa komai ba kanta a sunkuye, xae yi magana motarsu Hajiya suka shigo gidan, ya mike da sauri ya shiga kitchen sae gashi ya fito da ruwa a glass ya fito da ledar magani ya balla ya durkusa gabanta yace "gashi ki sha kanwata hope kinci abinci," ba tace masa komai ba kuma bata karbi maganin ba, ya dinga rokanta yana lallabata ta sha maganin amma taki ko da dagowa ta kallesa sae hawayen da take tayi, ya mike yyi tsaki ta dalilin kiransa da yaji Hajiyarsa nayi a falo, bae sake shigowa garden din ba har karfe biyar saura, ganin baxa ta iya daurewa bne kuma yasa ta mike da kyar tana ganin jiri ta shiga falon tace ma Hajiya tayi hkuri xata tafi gida bata da lafiya, Hajiyar ta tsaya kallonta don duk wanda yaga yana yinta yasan bata da lfya, ta tabe baki xata yi magana pretty tace "momy ki bar ta ta wuce tun tuni take ta ma mutane amai kar taje ta sume mana a gida," Hajiyar tayi tsaki tace "to tashi sae ki gyara min daki snn ki tafi makira kawae," Haiydar ya mike yyi waje, ita ko ta shiga ta gyara dakin da kyar snn ta fito tayi masu sae da safe ta fita, sumy ta bita a baya, Haiydar na tsaye bakin gate yana jiranta, tana fitowa kuwa xae yi magana sae ga sumy, ya juya da sauri yana danna wayarsa kmr mai shirin kira, ita ko ta kama hanyar gida tana karanto addu'a a xuciyarta na Allah ya kai ta lfya ganin condition dinta, Haiydar ya galla ma sumy harara a fusace yace "uban me kike nema a nn," cikin ladabi kar ya maketa tace "kawata nake jira bata san gidan ba shi yasa na fito," yyi tsaki ya juya bae[truncated by WhatsApp] [9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 26..... Aneesah ta dauke idonta da sauri daga na sa ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta, cikin tsawa hajiya tace "rainin wayon naki ne ya tashi shegiya xaki yi ma mutane shiru ki samu gaba kina kallo da daddaya da daddaya don uwarki" ta girgixa kai a raunane tana hawaye tace "kuyi hkuri hajiya wllh kanina ne ya rasu," cikin halin ko in kula Hajiya tace "to ni na kashe shi da xaki ki xuwa min aiki," Aneesah tayi shiru tana hawayen takaici, Hajiyar ta tabe baki tace "to ki sani baxan biya ki kudi cikin wnn watan ba sae karshen sabon watan da xamu shiga, bace min da gani kar na ji maki ciwo a nn mayya kawae ba kaninki ba uwarki da ubanki ma su mutu ina ruwan wani," Aneesah ta mike tsaye a sanyaye hawaye na bin kuncinta xata bar falon, cikin gadara meenah tace "kuma ga kayan wanki na can ya taru ba kyan gani, dasu xa ki fara," sumy tace "nima wllh gasu can duk ki hada yau ki wanke mana ni har da takalma na, kuma ki cire ma mutane wnn hijabin jikin naki duk ya janyo ma mutane duhu a falo," Aneesah dae na tsaye tana hawaye tana kallon sumyn cike da takaici kuma bata cire hijab din ba, sumy ta mike a fusace ta fixge hijab din daga jikinta ta wurgar tana huci tace "don uwarki ina maki magana xaki yi min shiru......" ba shiri sumy tayi shiru ta wara ido baki bude tana kallon gashin kan Aneesahn da ya xubo har kusan bayanta ta dalilin fixge mata hijabin da tayi hade da dankwalin kanta, meenah ta mike da sauri da mamaki tace "lala attachment ne a kanki kina matsayin yar aiki ni nasa ke ki sa," a fusace ta damko gashin Aneesar a xatonta kari tayi kmr yanda su ma ke yi, "wllh sae kin cire gashin nn ynxun nn a nn idan ba hka ba har gashin kanki sae na aske yau, dama munafuka shi yasa baki son cire hijab idan kika......" wani wawan marin da aka dauketa da ne ya sa ta kasa karasawa ta fasa ihu a gigice ta sake gashin Aneesar tana kallon wanda ya mareta yayanta ta gani tsaye kanta yana huci, ya fixgota ya buga ta da bango snn ya damki nata karin gashin dake kanta yana huci ya makureta cikin tsawa yace "uban me ta maki kike neman birkita mata kwakwalwa nake son ki gaya min kar na hallakaki a nn," Hajiya ta mike tana salati a rude tace "me xan gani hka Aliyu, meye hadinka da 'yar aikin nn xaka kashe kanwarka kanta," ya wurgar da meenar a fusace, ya dawo kan Aneesah da ke durkushe a wajen tana rusa kuka, ya durkusa gabanta ya dago kanta a hankali yana kallonta cike da tausayi yace "kiyi hakuri fateema," Hajiyar ta yo waje da ido baki bude tana kallonsu a tsorace ta daura hannu a ka tace "Aliyu," pretty ta mike a hankali ita ma tana hawaye ta bar falon ta haye sama, sumy ta mike tsaye ta fashe da wani wawan dariya tana kallon uwartata tace "heheho me na gaya maki mummy ba kin ki yarda dani ba, ni dama nasan da wani abun a tsakaninsu wllh, kin taba ganin yaya ya hana 'yar aiki yi mana aiki a gidan nn, ko kin taba ganin ya ci girkin 'yan aiki, ko 'yar aiki ta taba shiga dakinsa da sunan gyara masa ko yi masa guga, yaya bashi da aiki ynxu sae na xuwa garden, ni dama nasan da wani abu a kasa amma kika ki yarda dani da meenah, yau dae gashi kin gane ma idonki, shiyasa ranan nn ma na fita da sauri ganin ko bin ta xae yi a bakin gate nayi masa karya kwata nake jira, ba haushi na ya dinga ji ba har washegari na hana sa bin sahibarsa, a bnxa aka ce maki yake rashin lafiya kwanan nn," ta sake fashewa da dariya tana tafa hannu tace "kasala don burst" Aliyu ya yo kanta cikin fushi ya buga ta da bango da karfi, nn da nn se ga jini da gudu kmr famfo, daga ita har Hajiya suka rude Hajiya ta dinga rusa ihu tayi kitchen da gudu tana cewa "kan wnn matsiyaciyar xaka kashe min 'ya, wllh wllh wllh sae na hallaka ta yau," sanin halin uwartasa yasa ya ja Aneesar dake ta kuka da sauri suka bar falon, yyi garage ya bude motarsa don makulli na aljihunsa ya saka ta cikin motar ya xaga da sauri ya shiga ya tada motar yana horn ba kakkautawa, sae ga Hajiyar da gudu ta fito rike da tabarya da wuka, cikin tsawa ta dinga cewa maigadin kar ya bude gate din, Aliyu dake jiran ya karasa bude gate din kawae ya fice ya daka masa tsawa yace "xan take ka da motar nn baka bude min gate ba malam," maigadi duk ya rude ya rasa umarnin wanda xae bi ganin Aliyu ya yo kansa da motar yasa cikin ihu a gigice ya dinga cewa xae bude har ya wangala gate din jikinsa na rawa Aliyu ya fice da gudu ya bar compound din, kmr xasu tashi sama. [9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 28..... Aneesah ta shiga daki ta fito da tabarma ta shimfida masa ya xauna, Ammi ta fito ta dauko kujera ta xauna tanai masa sannu da xuwa murmushi bayyane a fuskarta, ya gaisheta a ladabe yana tambayar ya gidan, tace masa lfya lau ya nasu gida, yyi mata gaisuwan rasuwar yusuf, tayi masa gdya sosai daga bisanni ya sake bata hakura a kan abinda ya faru snn yyi mata sallama yace xae wuce, tayi masa gdya tace Allah ya
Chapter 14 · 0% Book details