Sashe 42
Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
girgixa masa kai, hawayen da ta ga idonsa ya dada rikita ta, ya juya yyi hanyar motarsa, ta sulale wajen cikin tashin hankali, da kyar ta iya cewa "na shiga uku," tana kallo har Hydar ya bar anguwar, ta fashe da wani sabon kukan da ta sanin abun da tayi, da kyar ta iya mike tayi hanyar shiga gida tana ganin jiri, bata bari Ammi ta lura da kukan da take ba, tana shiga daki kwanciya kawae tayi, ranar tayi kukan da ta sanin abun da tayi da daddare, bacci ya kaurace mata duk taji bbu abinda ke mata dadi a duniyar, taji ta tsani kanta, sae kusan karfe uku ta samu bacci, da safe Ammi ta lura da yanda idonta ya kumbura tayi tayi da ita me ya sameta taki gaya ma Ammi tace kanta ne ke ciwo kawae, karfe sha daya su ummi da Momynta suka xo gidansu, Aneesah tayi farin cikin ganinsu ssae kuma tayi mamakin yanda akayi suka san gidansu, Ammi ta tare su da kyau don Aneesah ta bata lbrinsu, har Ammi na shirin xasu je gidan nasu xuwa nxt wk sae kuma ga su sun xo, momy na ta hira da Ammi bayan ta mata jajan Abinda ya faru, duk wnn hiran da ake Aneesah dakewa take kawae don xaxxabi take ji na neman rufeta, duk she is nt herself ta rasa abinda ke mata ddi a duniyar, kar ummi tace ta shareta yasa ta shiga tambayarta Mudatheer da mutanen da ta saba da xamanta gidansu, ummi tace "yana kano ae tun lst wkk," Aneesah ta dauko takarda da pen tace ummi ta rubuta mata Nmbrsa, sae kusan sha biyu Ammi da Aneesah suka rakasu bakin motarsu xasu koma gida, Ammi tace masu suna nn xuwa suma. Bayan tafiyar su ummi da kmr minti ashirin Faruuq ya shigo gidan, Aneesah ta kirkiro fara'a tana gaishesa ya amsa yana murmushi, tace "sae ynxu ya faruuq," yace "wllh kuwa ya shiga ya gaida Ammi a daki," Aneesah ta xauna ta rafka tagumi tayi jigum a tsakar gidan abun duniya ya isheta, tuna abinda ya faru jiya yasa hawaye ya shiga bin kuncinta, bata masu halacci ba, ta butulce masu, ta cuce kanta, kuka ssae take amma mara sauti, ta ga mutum durkushe gefenta yana kallonta, ta mike tsaye da sauri tana goge hawayenta tace "ya faruuq," ya girgixa mata kai yace "me ya faru Aneesah," tana goge fuskarta tace "bbu komai," ya harareta yace "karya kike yi, bana ce ki daukeni matsayin yayanki ba Aneesah, meye damuwarki ki gaya min, kar ki boye min ni yayanki ne kinji" wasu sababbin hawayen na bin kuncinta tace "bbu komai ya faruuq," yace "to bari naje na kira Ammi sae ki gaya mata ita," ta girgixa masa kai da sauri tace "A'a don Allah kayi hkuri," yace "to gaya min me ya sa ki kuka, tunda na shigo na lura kina cikin damuwa kanwata," tana goge fuskarta a sanyaye ta kasa cewa komai, yace "ki yarda dani Aneesah, ki gaya min damuwarki don Allah," a hankali tace "xan gaya maka to," ya shiga dakin da Ammi ta gyara masa don dakuna uku ne a gidan dama, ta bi sa a baya ta xauna kan kujera tana kallonsa yace "ina jinki kanwata," a sanyaye tace "lbrin mutane biyu xan baka yayana, sae ka gaya min wanda yafi cancanta a cikinsu ya xama mamallakin warce ke cikin lbrin nawa," ya hade rae yace "lbri nace maki nake son ji, matsalarki nace ki gaya min na sama maki solution kanwata," tace "ka fara saurarana yaya, wllh xaka ji damuwata idan na gama baka lbrin," yace "to ina jinki," a nutse ta shiga basa lbrin kanta ba tare da ta bari ya gane ba, tun daga farko har ixuwa lkcn da ta fara aiki gidansu Hydar, da irin taimakon da yyi mata, tun daga nn ya gane lbrinta take basa, ya dae yi shiru yana sauraranta, bbu abinda ta boye ma faruuq har xuwanta kauye da haduwarta da Mudatheer, snn Mujaheed, Faruuq ya tsura mata ido yana sauraran lbrin nata har ixuwa abinda ya faru jiya da daddare, bbu part din da ta boye masa, ta fashe da kuka tana kallon faruuq da ya lumshe idonsa ya kasa cewa komai, a hankali taji yace "Hydar ya cancanci xama mamallakin ki Aneesah," [12/8, 21:13] +234 803 751 8717: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 110.... A hankali Aneesah ta sulalo daga kan kujeran da take hawaye na bin kuncinta, Faruuq ya tsura mata ido snn yace "me yasa kika ce xaki biyasu abinda suka maki Aneesah, kinga alamar xaki iya biyan abinda suka maki, barin Hydar da ya xauna prison na watanni," kuka ssae take tana girgixa kai tace "ban san lkcn da nace masu hka ba ya Faruuq," faruuq yace "to ki kirasu ki basu hakuri," a sanyaye tace "ban da nmbrsu," yyi shiru yana kallonta snn yace "ki bani address dinsu duka, kafin na tafi yau xanje na samesu," ta gyada masa kai tana kallonsa, a takarda ta rubuta masa address dinsu gaba daya, snn ya mike yace "to ki share hawayenki kanwata kar ki daga ma Ammi hankali, sae na dawo" yana kai wa nn ya fice ta bi sa da kallo hawaye mai xafi na bin kuncinta, ta mike da kyar tana gyara fuskarta ta fita daga dakin xata je yin wanke wanke, throughout ranar Ammi ta kasa gane kan Aneesah duk ita ma ta daga hankalinta, ita dae Aneesah jiran dawowar ya faruuq kawae take, da yamma tana share tsakar gida taji an bude kofar gidan ta mike da sauri a tunaninta Faruuq ne, pretty ce ta shigo gidan kmr mahaukaciya wasu mata na biye da ita a baya, gaban Aneesah yyi mugun faduwa, pretty ta karaso kusa da ita da sauri ta rikota ta fashe da kuka tace "me kika yi ma yayana Aneesah, ki gaya min me kika yi ma yayana," ta sulale kasa ta daura hannu a ka tana kuka mai ban tausayi tace "don Allah ki gaya min me kika yi masa," Hajiyar Mujaheed ta karaso cikin gidan ita ma a rude tana kallon Aneesah tace "ke ce Aneesah ko," Aneesah ta kasa cewa komai don tashin hankali, a hankali ta sami kanta da sulale kasa ta fasa wani ihu a tsorace, hajiyar ta durkushe gabanta a rude ta rikota tace "don Allah ki rufa mana asiri," don a tunaninta suma Aneesah xata yi, Ammi da bata gidan ta shigo dai dai lkcn, ta karaso a dan tsorace tace "me ya faru," pretty na kuka ssae tace "don Allah mama ki bar ta ta bi mu asibiti, kar yayana ya mutu ita yake ta kira," daya daga cikin matan da suka shigo gidan ta dago Aneesah tayi waje da ita, Hajiya na biye da su da sauri, duk da ganinsu kasan suna cikin tashin hankali, Aneesah komawa tayi kmr statue duk ta kasa wani kwakkwaran tunani da kwakwalwarta, ta xama kmr wata mutum mutumi, hawayenta ma tamkar sun kafe take ga, Amai ta shiga kwararawa cikin motar ba gaira ba dalili, don har lkcn ita bata gama fahimtan abinda ke faruwa ba, matan suka riketa a rude wata na xuba mata ruwa, sae a snn maganganun pretty suka dinga dawo mata, daga nn kuma bata sake sanin abun da ya faru ba, don sulalewa jikin matar da ke rike da ita tayi sumammiya.duk suka rude a motar wasu har da kuka, pretty nata kam ba a magana, suna isa asibitin ita ma aka shiga da ita da sauri. Ko da ta bude idonta pretty ta gani xaune gefenta tana kuka, pretty ta kamo hannunta cikin kuka tace "don Allah kar ki sake rufe idonki Aneesah ki tausayama yayana," wata nurse ta shigo ta janye pretty daga kusa da Aneesah da ta xuba mata ido kmr wata mara hankali, nurse din tasa duk matan dake dakin suka fita, Aneesah dae binsu kawae take da kallo, nurse din ta fita ta ja kofar, bacci mai nauyi ya dauketa daga nn. [12/8, 21:13] +234 803 751 8717: Khaleesat Haiydar ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 111..... A hankali Aneesah ta bude idonta ta shiga kare ma inda take kallo, daga karshe ta sauke idonta kan drip din dake hannunta, ta fara kkrin mikewa xaune, taji muryan mutum a gefenta, ta juya da sauri taga Abdul ne, yace "ya jikin kanwata" tayi shiru tana kallonsa, ya mike ya fita ya shigo da nurse ta cire mata drip snn tace a bata tea ta sha, Abdul ya fita ya shigo tare da mum din Mujaheed ta karaso kusa da Aneesah tace "sannu kinji Aneesah," Aneesah dae bata ce komai ba sae kallonta da take, ta hada mata tea ta shiga bata da kanta, kadan Aneesah ta sha ta kauda mata kai Hajiyar tace "ki sha mana Aneesah," Aneesah ta girgixa mata kai a karo na farko muryarta a shake tace "ya Hydar fa," Hajiyar tace "ki daure ki sha sae na kai ki gunsa bacci yake," da kyar ta shiga kurban tean har tayi rabi tace ta koshi, wata nurse ta shigo da magunguna mum din Mujaheed ta karba tace "xa mu iya dan fita da ita nurse," Nurse din tace "idan har bata ganin jiri xaku iya fita da ita amma kar kuyi nisa," Hajiya tace "A'a bama waje xamu ba, ward din dake sama xamu," nurse din tace "ok," tana kallon Aneesah tace "hope bbu inda ke maki ciwo ynxu," Aneesah ta gyada mata kai nurse din ta fita, Abdul yace "mum ku bar Hydar ya huta kar a tada shi," hajiya tace "aa baxa mu tashe sa ba dama, da ya ma aka samu yyi baccin," hajiyar ta taimaka ma Aneesah ta mike tsaye ta bata takalmi ta sa, snn suka fita daga dakin, dakin da Hajiyar ke kwance ta fara kai ta, hajiya duk ta rame ta xama wani iri ita ma a daxun ciwonta ya tashi bayan an aiko mata da rasuwar sumy a can india, snn ga Hydar da aka rasa me ya samesa lkci daya, don lkcn bai ma san da mutuwar kanwartasa ba bare ace shine, Aneesah ta shigo dakin a sanyaye tana kallon hajiyar da ta mike xaune da sauri ganinta, ita ma ruwan ake