← Book details Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 58

Sashe 17

Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace "uhum ina jinka Aliyu," yace "ko kuma ma dae bari xan dawo xuwa anjima Ammi, sae muyi maganar," yana kai wa nn ya mike ba tare da ya kalle Hajiya zuwairar da har lkcn bakin ta yaki rufuwa ba ya fice daga dakin, Hajiyar tayi murmushin takaici tace "xa ku gane kuranku in dae ni ce zuwaira " tana gama fadin hka ta juya fuu tayi hanyar fita daga gidan tana huci, Aneesah dake xaune kan kujera a tsakar gidan tana hawaye Haiydar na durkushe gabanta yana mata magana suka bita da kallo har ta fita, Haiydar yyi murmushi yace "hmm mu je dae xuwa," ya mike ya koma cikin dakin Aneesah ta bisa da kallo, ya dde cikin dakin ko me yake ce ma Ammi, can dae ya fito yana kallonta yace "je dauko Hijab Aneesah," ta tsura masa ido tana kallonsa ya gyada mata kai, ta mike jikinta a sanyaye ta shiga dakin dauko hijab, ta xauna gaban Amminta tace "Ammi yace na dauko hijab," Ammi tace "Sae kun dawo ki kula da kanki Aneesah," Aneesah ta mike a hankali tace "to Ammi" snn ta fita, makaranta ya kai ta yyi mata registrn waec da neco, snn suka dawo gida wajen karfe sha daya na safe bayan tayi registre din lesson din makarantar kafin a fara jarabawan, ta rasa irin godiyar da xata ma Haiydar kawae ta fashe masa da kuka bayan yyi parkin, nn ya barta kofar gidan nasu ya wuce don bai ga abinda take ma kuka ba a nn. Da yamma tana xaune tsakar gida tana duba litattafenta don gobe xata fara xuwa lesson din daga karfe tara xuwa karfe biyu na rana, Ammi kuwa ta tafi kasuwa, taji an bude kofar xaure a tunaninta Ammi ce ta mike da sauri karbo kayan hannunta ta kusan cin karo da mutum, ta koma baya da sauri, Abdul ne, ta juya xata bar wajen gabanta na faduwa ganin Amminta bata nn ya fixgota ya hada da bango yana mata wani irin kallo, tuni jikinta ya dau rawa amma ta dake tace "meye hka xaka fado ma mutane gida ba sallama," ya take mata kafa da takalminsa tayi yar kara yana rike da kafadarta yace "daxun wani rashin kunya kika yi ma momyna?" ta galla masa harara gabanta na faduwa a xuciyarta tana ta adduar Allah ya dawo da Ammi a lkcn, a fili kuma tace "ni ka sake ni don Allah malam," ya fixge dan kwalin kanta yana mata wani mayen kallo yace "uwata kika yi ma fitsara daxu ko," tace "ni ka rabu dani" ya daura hannu kan gashin kanta yana shafa gashin yace "wae ma wani mutumi ne ya xo gidan nn daxu da safe?" ta buge masa hannu a tsorace tace "wae me nayi maka xaka takura ma rayuwata hka ne," ya juya yana kallon kofar dakinsu yace "uwarki fa?" da sauri xuciyarta na bugawa ta galla masa harara tace "bacci take," ya daga kafada ya kamo hannunta yana kallon cikin idonta yace "we re goin out now, xaki dan rakani nn cikin gari" Like · 7 · Report · 44 minutes ago [9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 30..... Ya karaso gabanta ya tsaya yana dan bubbuga kafa a kasa yana mata wani irin kallo, bata ko daga kai ta kalle inda yake ba ta karasa alwalanta ta mike xata shiga daki ya kamo hannunta, murya kasa kasa yace "baki da respect yarinyar nn ko, baki ga mijinki bne?" ta fixge hannunta a fusace ta daka masa tsawa "wae ni ka rabu dani mana malam, a ina na san ka," xae yi magana Ammi ta fito daga daki tana kallonsu, tace "xo ki wuce ciki," Aneesah ta wuce sa da sauri ta shige daki, ya tsaya yana ma Ammin kallon rainin wayo, can yyi dariya yace "hope kin shirya rabuwa da 'yar ki ynxu Hajiya maryam," Ammi bata ce masa komai ba ta juya ta shige dakin ita ma ta rufo kofar. Ya karashi dariyarsa ya fice daga gidan, Ammi ta dubi Aneesah da ta xauna tayi jigum bayan ta idar da sllh tace "shi yasa nace ki shirya ki wuce gombe Aneesah, ko xuwa gobe xan baki kudin mota ki tafi," Aneesah bata ce komai ba sae dae hawaye ya taru idonta ta sunkuyar da kanta da sauri gudun kar Ammi ta gani, ranar kasa bacci Aneesah tayi, tunanin rabuwa da Amminta da ya Haiydar take cikin 'yan kwanakin da basu wuce wata daya ba ba karamin shakuwa tayi da Haiydar ba, ita kam dawowar Abdul ba karamin tashin hankali bane gare ta, tun tana karamarta dama ta tsane shi don bae da kamun kai ga son mata, da kyar Aneesah ta iya tashi washegari don ji tayi duk jikinta ba kwari, karfe takwas tana xaune koko da kosae a gabanta ta kasa ci sae jujjuya kosan take, Ammi ko na ta faman hada mata kayanta, wayan da Haiydar ya bata ya shiga ring ta juya da sauri tana kallon wayar, Ammi tace "ba na ce ki mayar masa da wayarsa ba Aneesah," a sanyaye Aneesah ta ce "dama yau xan maida masa Ammi, shi ne ma ke kiran," ta daga wayar suka gaisa yace gashi ya kusa anguwarsu, ta wara ido tana kallon Ammi tace "yanxu?" yace "ko na juya," ta girgixa kanta a hankali tace "A'a ni ban ce ba," yyi murmushi ya kashe wayan, ta juya tana kallon agogo ammi tace "me ya faru kuma?" ta sunkuyar da kanta tace "kila wayar xae xo karba yace yana hanya," Ammi bata sake cewa komai ba ta ci gaba da abinda take, yana parkin kofar gidansu ya kirata ta saka hijab ta fita jikinta a sanyaye bayan ta nemi ixini gun Amminta, ya fito yana kallonta yace "me ya faru Aneesah," tace "ba komai kai na ne ke min ciwo kawae," yace "Ayya kin sha magani to?" ta gyada masa kai kawae tana kallonsa, yana sanye ne da bakar suit yyi kyau ba kadan ba, yana kallonta yace "Ammi fa," ta jingina jikin motar tace "tana ciki," wae jikin ne hka Aneesah," ya tambaya da damuwa, tace "A'a ae na sha magani," yace "to Allah ya sauwake, hope kin shirya kin ga aiki xan tafi," tace "na shirya me?" ya dan harareta yace "kin fasa xana waec din ne, registratn xa muje muyi," tayi shiru tana kallonsa a raunane tace "kaga gombe xan tafi yau fa," yace "gombe kuma, me xaki je yi a gombe," ta fara hawaye tace "Ammi ce tace na tafi," yyi shiru yana kallonta can yace "Ammi tana ciki," ta gyada masa kai kawae yace "can i go in," nn ma ta gyada masa kai ya shiga gidan tana biye da shi a baya, har daki ya shiga ya gaida Ammi ta amsa da fara'arta tana tambayarsa mutan gidan yace "duk lfya suke Ammi," Ammi tace "to madallah," ya danyi shiru snn yace "Ammi na xo ne xamuje registratn na waec tace min gombe xata tafi, don Allah Ammi ki bar ta ta xana exam dinta ko akwae abinda xata yi a can ne," Ammi ta girgixa kai tace "bbu Abinda xata yi a can Aliyu wajen kakata da ta rikeni xata ne, xuwan ta can xae fi mana kwanciyar hankali daga ni har itan," yace "sbda me Ammi," Ammi tayi shiru tana kallon Aneesar dake hawaye, xata yi magana taji an shigo gidan ana kwala mata kira, maryam, maryam, maryam, Ammi bata yi kkrin mikewa daga inda take ba jin muryar me kiran nata, matar baffa shehu ce, ta shigo dakin a fusace ta tsaya masu bakin kofa tana nuna su da dan yatsa, "wllh wllh ko ma uban me ku ka yi ma dana tun wuri kuje ku karya shi idan ba hka ba xa ku sha mamaki daga ke har 'yar ki, kaji mun talakokin banxa makwadaita, uban me Abdul dina xae yi da wnn shegiyar 'yar taki, wllh tun wuri ku koma wajen bokan da kuka je ya lalata aikin da yyi maku," Aneesah da ta kasa daure jin irin bakaken maganganun da matar baffanta ke gaya masu tace "ke wae ance maki kowa ma irin ki ne mai xuwa wajen boka, ko kuma uban me ma xanyi da dan naki da baki baki masa tarbiyar arxiki ba sae ta tsiya, kin xo kina ta ma mutane haushi uwa kare a gida, wllh na fi karfin dan ki Abdul, kuma da na auri Abdul gwara na aure mahaukaci mara hankali" [9:30PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 33.... Aneesah ce xaune kan tabarma a tsakar gida tana ta faman jujjuya littafin biology dake hannunta a sunan karatu, duk hankalinta baya jikinta, don rabon da taga Haiydar yau sati uku cif, kuma bai taba ddewa hka bae xo gidansu ba, snn bata san inda ta jefa wayar da ya bata ba ma Ammi na kitchen tana girkin dare da yake wajajen karfe biyar da rabi na yamma ne, ta mike a sanyaye jin kiran da Ammi ke mata ta karasa kitchen din, Ammi tace "ruwa xaki debo, kin dae san ba ruwa a gidan, na rasa wani irin karatu kike yi tun karfe uku," Aneesah bata ce kmai ba ta dauki bokitin ta juya xata bar gidan, Ammi ta kirata ta dawo tace "na'am Ammi," Ammi ta juyo tana kallnta tace "ki gaya min me ke damunki Aneesah duk kwanan nn na rasa gane maki, idan ma Aliyu ne ae addu'a xakiyi Allah yasa lfya Aneesah," ta gyada ma Ammi kai tana kkrin maida hawayen dake kkrin xubo mata ta juya ta bar gidan da sauri, har ta daura ruwan a ka bayan ta debo ta tuna warnin din Haiydar ta sauke a hankali ta rike a hannu ta kama hanyar gida, tana isa kofar gidansu ta ga mota a parke gabanta ya fadi, Allah yasa yayanta ne ta fadi a xuciyarta, ta tsaya tana kare ma motar kallo ganin bata taba ganin Haiydar da irin motar ba, Abdul ne ya fito kmr wani sarki yana mata wani irin kallo, ta ja dogon tsakin takaici ta dauki bokitin ruwanta xata shiga ciki yace "hey!" har ta shiga xauren ta fito don bata son ya shigo cikin gidan nasu yyi ma Ammi wlkncin
Chapter 17 · 0% Book details