Sashe 26
Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ido tace "me?? Kmr ya naji," shatu tace "ca tayi Abulo ce ta fara tsokanarta ko ke kurma ce, don hka sae ki ja ma abulo kunne ta fita harkarta don Aneesah salaha ce ni nasan bbu ruwanta, kar watarana ta je tayi mata wnda ya fi wnn don nasan Abulo akwae aukin tsokana" kyauta ta saki shewan rashin mutunci tace "kan uban nn, ae yau wllh sae na rama ma 'ya ta," shatu ta cire tsumman dankwalin kanta ta daura kugu tace "kika taba min 'ya yau na nakada maki uban duka wllh wllh," [9:37PM, 12/21/2016] Khaleesat: [12/8, 21:11] +234 803 751 8717: Khaleesat Haiydar ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 51..... Aneesah tayi shiru tana sauraran shatu da ta sa ta gaba wae xata yi mata magana a cikin bukkarta, shatu tace "kina dae jina ko?" Aneesah tace "eh mama ina ji," shatu tayi kasa da murya tace "ae dae kinsan malam tanko na nn kauyen?" Aneesah ta girgixa kai tace "A'a ban san shi ba?" shatu ta harareta tace "shi uban garbeben ne baki sani ba?" Aneesah ta dan yarfe hannu tace "ina dae jin lbrinsa mama," shatu tace "yauwa, kin dae san duk kauyen nn bbu mai kudinsa ko, kuma shanayensa ma sun fi ashirin da biyar kin sani, snn da siminti aka gina masa gidansa dake kusa da kasuwan 'yan gwari, 'ya yansa maxa da mata suna can wnn kauyen dake gaba da namu suna karatu wae a firamari, kin dae san bae ma cika xama a kauye ba sae lkci lkci don a can birni yake aiki amma duk matansa uku suna nn kauyen," Aneesah dae kai kawae take gyada mata gabanta na faduwa, shatu tayi murmushi tace "yauwa Aneesah, shi fa, wllh jiya malam ya xo ya sameni wae yace son ki yake da aure, da kin san yanda matan kauyen nn ke rububinsa ko Aneesah," shatu tayi kwafa ta cija dan yatsa tace "kar ki bani kunya Aneesah, mu ba mara da kunya, kinga dae ina da 'ya ya mata amma ban maki bakin cikin auren tanko ba don nasan duk karuwa xamuyi ko ba komai, don hka nake sonki bani hadin kai, wllh dubu daya jiya ya ba malam da kaji biyu," Aneesah ta kasa cewa komai don tashin hankali, ta shiga uku wnn tsohon namamajon da taji karime ke cewa xa a hada ta da? Da kyar ta gyada kai ganin shatu jiran cewarta take tace "to mama naji duk abinda kike so shi nke so," shatu tayi murmushi har sae da jajayen hakoranta suka bayyana snn tace "yauwa lu'u lu'u 'yar Albarka shi yasa nake son ki, amma fa karki ki kula su garbebe da su hudu da mai shayi, duk abinda suka ba ki ki karba ae basu san da xancen ba, amma gskya wnn mudassirun ki rabu dashi don na tsanesa wllh, gashi ko kwandala baya baki na gani," Aneesah dae to kawae take ta ce mata kanta a kasa, tana kkrin mayar da hawayen dake neman xubo mata, shatu tace "yauwa Aneesah maxa tashi ki je ga can guntun kaxan jiya ki dauka ki ci ki yi min wanke wanke ki gyara min gida ki debo ruwa ki ajiye, ni ynxu xan je saro gyada ne, tunda su gantalallun yaran nn ban san inda suka yi ba, tana kaiwa nn ta saba bakin gyalenta ta fita daga bukkar tana cewa sae na dawo, kuka kam har da na tashin hankli Aneesah tayi shi ranar, ohh ko wani Hali Amminta ke ciki ma ynxu, ko ina yaya Haydar dinta gashi ana shirin mata aure da tsoho, da kyar ta iya yin duk aikin da shatu ta sa ta kafin ta dawo don duk jikinta yyi sanyi. Da yamma tana gantalin nemo itacen girki a kauyen suka hadu da mudassir da lado, lado na ganinta yace "gidan malam mati basa taba siyan itacen naira goma, sae dae su tsinta a daji," bata ko kallesu ba ta wuce su don dama basa shiri da lado tunda ya nuna yana sonta tayi shun dinsa, mudatheer ya bita yace "'yar birni ba gaisuwa," ta juya tana kallonsa taga lado yyi gaba abinsa, hkn yasa ta xauna karkashin wata bishiya mudassir ma ya xauna, yace "shatu ta dokeki ne halan," ta tabe baki bata ce masa komai ba tana harhada icenta, sae da ta gama snn ta juyo tana kallonsa tace "wae don ina son sanin gidanku shine xaka wani ce min it's of no use ko [12/8, 21:11] +234 803 751 8717: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 53..... Yau ma kmr kullum Aneesah ta fita neman itacen girkin yamma ta hadu da Mudatheer, ta karaso karkashin bishiyar da yake ta xauna tana kallonsa tace "to baka fa gaya min gidan wa kke ba a nn kauyen" ya dago yana kallonta yace "ina yini?" tayi dariya tace "au na manta ina yini?" bae ce komai ba sae murmushin da yyi, snn yace "gidansu sanusi da lado nake ai kin sansu?" tace "lah wa inan kaxaman masu xaman kashe wando sae ji da kan karya, ko gona bnga suna xuwa ba" mudatheer yyi dariya yace "xasu maki duka kuwa idan suka ji ki" ta hararesa tace "tunda 'yar su ce ni ba, wae in tambayeka meysa su garbebe ke jin tsoranka toh?" nn ma yyi dariya yace "sbda mun taba gwada karfi dasu na raunata su gaba daya, daga nn suka gane ni wanene, kuma na samu kwanciyar hankali daga lkcn a kauyen." Aneesah ta dinga dariya har da buga kafa, yyi murmushi yace "yau ma sae shatu ta biyo ki koh, wae ma meye hadinki da mugayen mutanen nn marasu hali?" Aneesah tayi shiru bata ce komai ba, can ta mike tace "ni xan je neman woods na girki bye bye," ya mike da sauri yace "to bara na rakaki inda xaki samu woods da yawa," tace "to muje," ya shiga gaba tana biye da shi a baya. Da daddaren ranan tana dandali tana sayar da gyada wata 'yar makwabciyarsu shafa ta xo da gudu kiranta, wae shatu tace ta maxa ta dawo gida ko bata sayar da gyadan duka ba, Aneesah tayi ma kawarta karime dake saida xobo sallama snn ta dauki bokitin gyadar ta ta bar dandalin don abokinta mudatheer ma bae xo ba, tana isa gida taga wata tsohuwar mota da ta gama shan wahalar duniya tana neman freedom a fake a kofar gida, ta bi ta gefen motar ta shiga gidan, shatu ta gani xaune kan 'yar kujera, kan tabarma kuwa wani tsoho ne dake ta washe baki, gaban Aneesah yyi mugun faduwa ta dake ta karaso dan tsakar gidan da sallamarta snn ta shige bukkarsu, shatu na wagale baki tace "sannu da dawowa lu'u lu'u, in kin ajiye bokin ki fito ga malam tanko ku gaisa," Aneesah tayi kmr bata ji ta ba ta sulale kasa a hankali cike da tausayin kanta taji kmr ta fasa ihu, shatu ce ta shigo dakin da kanta tana ganin Aneesah a wnn hali ta hade rai, tace "ke ni fa ban son iskanci da rainin hankali, kina ji ina kiranki xaki yi bnxa dani ga bawan Allah can ya xo tun daxu yana jiranki, an gaya maki yana xuwa gun 'yan mata ne da sunan xance, wllh sae dae su suje gidansa su same shi, don mun samu ya tuko santaleliyar motarsa har nn shine xaki masa walakanci, maxa shafa jan baki da hoda ki fito yana jiranki," Aneesah ta mike tsaye da kyar tana kkrin mayar da hawayen da ya cika idonta, shatu na kallonta tayi duk yanda ta ce mata, snn ta sa ta yafa wani dan guntun mayafi, xata fita shatu ta jawo ta da sauri, ta marairaice fuska kmr xata yi kuka tace "ki tausaya min Aneesah idan muka rasa wnn daman mun shiga uku hka xamu ta tsaya wa a talauce har mu mutu, don Allah ki ba sa hadin kai, duk me yace maki kiyi, kinga ko sati biyu baxa a yi ba xa a daura auren ku, idan ma baki son xama wnn kauyen ne sbda 'yan sa ido kawae sae ki koma kauyen dake gaba da wnn yana da gida a can aka ce wae, ki rufa min asiri kar ki sa a mana dariya don ixuwa ynxu lbri ya gama baxuwa wae malam tanko na birni xae aure Aneesah, kar ki bani kunya don Allah," tunda shatu ta fara xancen ta kan Aneesah a kasa yake tana kukan xuci, har shatu ta sallameta tace maxa taje yana jiranta, ta fita jikinta a sanyaye ashe har ya fita kofar gida yana jiranta, tana karaso wa kuwa ya washe hakora yana murmushi yace "yauwa 'yan mata sannu da fitowa," ita dae bata ce kmai ba ta tsaya kanta a kasa, yace "to mu shiga cikin mota muyi hiran mana amaryata," ta dago cike da tsana tana kallonsa tace "A'a nn ma ya isa," yace "haba amaryata ae yawa ne a gan mu tsaye kmr yara a nn, ke dae shiga kawae,"ya bude motar yana kallonta, Aneesah tayi murmushin takaice tace "ni fa baxan shiga wnn motar ba malam," ya tsaya kallonta na kusan minti biyar snn ya bude motarsa ya shige ya ja ta yyi gaba, ta tabe baki a xuciyarta tace Alhmdllh ta shiga gida abinta, shatu na tsaye a bukkarta sae kai komo take ta kasa xaune ta kasa tsaye, Aneesah na shigowa ta riko hannayenta da sauri har wani bari jikinta yake tace "har ya tafi, nawa ya baki," Aneesah ta dan koma baya tace "wae fa mama sae na shiga motar da kila ko fitila ma bbu, ni ko nace masa baxan shiga ba shine ya wuce," shatu ta xaro kwala kwalan idonta ta daura hannu a ka ta kwala ihu tace "shiknn ta ja mana, Na shiga uku ni shatu don ubanki koransa kika yi sbda kin isa?? Na banu na lalace," Aneesah ta tsorata sosae da yanayin da shatu ta shiga, ta dinga komawa baya, cikin tsawa shatu tace "xo nn don ubanki shegiya mugu," [12/8, 21:11] +234 803 751 8717: ~Aneesah~ By Khaleesah Haiydar 54..... Aneesah ta fasa ihu ta durkushe wajen ganin shatu ta yo kanta, duka kam ta sha shi ranar don shatu komawa tayi kmr wata