Sashe 1
Aneesah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[9:29PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~ANEESAH~.... By Khaleesah~Haiydar *** 1..... A guje ta fado dakin ta xube kan Amminta dake linkin kaya tana sakawa cikin jaka, Ammi ta dago fuskarta a rude tana tambayarta "lfya? me yafaru?" tana mayar da numfashi a dan tsorace ta kasa ce ma Amminta komai, sae da Ammi ta maimaita mata tambayar a fusace snn ta fashe da dariya tace "wae Ammi yusuf ne xae dokeni, don mota ta take masa kwallonsa nayi dariya," Ammi ta haureta cikin fada ta fara magana "wae ke yaushe xakiyi hankali ne Aneesah, ba wanke-wanke na sa ki ba kika fita waje kina biye ma yusuf, shi yusuf din kike ma gudu idan ba wauta ba," ganin yanda Amminta ta fusata yasa ta mike tsaye da sauri ta marairaice murya tace "kiyi hkuri Ammi, amma idan na fita wllh dukana xae yi, kuka fa yake yi," Ammi xata yi magana sae gashi ya shigo dakin, da gudu tayi bayan Ammin tana cewa "wayyo ammi kin ganshi ko," Ammi ta dada mata duka snn tace "kai yusuf yayar taka xaka duka don ba ka da kunya," yyi ma Aneesar wani irin kallo yace "Allah ya taimake ki mutumin ya bani Naira ashirin na siya wani kwallon," Aneesah ta dinga dariya tana cewa "Naira ashirin" yace "eh mana" snn ya fito da sabbin dubu daya guda biyu, Aneesah ta xaro ido tana kallonsa, Ammi tace "kai yusuf wa ya baka wnn kudi hka," yace "mutum da ya fasa min ball da motarsa yace naje na siya sabo," Ammi ta juya tana kallon Aneesah, can tace "to kawo nn yusuf, anjima da kaina xanje kasuwa na siyo maka wani, amma kace masa ka gode ko?" yusuf yace "aa na manta, snn ya mika mata dubu biyun ya fice ya fice daga dakin," Ammi tace "oh Allah dae ya biya wnn mutumin, kmr yasan ynxu tunanin me xamu ci anjima nake Aneesah," Aneesah tayi murmushi tace "ki siyo kayan abinci kawae Ammi," ammi tace "hkn xanyi, bari na gama hada kayan nn sae na tafi kasuwa," Aneesah ta mike jikinta a sanyaye ta fita daga dakin taje yin wanke wanken dake tsakar gidan. [9:29PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ 3...... Yan uwansa na ganin hka suka fara shisshige masa suna nuna masa so, da yake shi Allah yyi sa mutum ne mai son xumunci kuma mara riko, ko kadan bai kullace su kan abinda suka yi masa ba ya ja su a jiki ya sama masu aiki don dama duk buga buga suke, ya kuma taimaka ma yan uwa da dama tun daga kan relatives har xuwa wa inda ma bai hada komai dasu ba. Ana hka suka hadu da Mahaifiyarsu Aneesah Maryam a bikin wani abokinsa, sunyi soyayyar gskya wanda ya kaisu ga aure duk da dangin ubanta basu so hkn ba don auren xumunci suka yi niyyar mata, amma da yake Allah yyi shine mijinta a hka su ka yi aurensu wanda bayan shekra daya Allah ya axurta su da samun Aneesah, daga ita ko basu sake haihuwa ba har sae bayan shekara takwas, don kaninta yusuf na da wata biyu mahaifin nasu ya rasu, ba karamin girgixa Ammi mutuwar mijin nata yyi ba, kuma duk da tsanar da danginsa ke mata don ko kadan basa sonta a hka ta gwammace ta xauna ta tarbiyantar da 'ya yanta a gidan ubansu don iyayenta talakawa ne sosae snn tun tana da shekara goma mahaifiyarta ta rasu matar uba ta sa ta gaba, hkn yasa kakarta na wajen uwarta ta maidota wajenta har Allah ya hadata da Alhaji Mukhtar suka yi aurensu, kuma tasan ko ta tunkari gidan mahaifinta ynxu baxae karbeta ba don duk abinda matarsa ta gaya masa shi yake bi, kuma matar bata so ta auri mai kudi ba tunda yayanta duk ba masu kudi suka aura ba, hkn yasa ta hkura ta xauna gidan mijinta da yaranta. Ko wata uku ba'ayi da rasuwan Alhaji Mukhtar ba yayansa da suke kira da Baffa shehu ya fitar dasu daga lafiyayyan mansion din da suke ciki wae xae sa yan haya ya dinga tara ma marayu kudinsu, duk da gidajen da mahaifin nasu ke da, Ammi bata yi masa musu ba ta harhada kayansu don a tunaninta dan madaidaicin gida xae basu su xauna, amma sae suka ga ya maidosu suleja ya basu daya daga cikin gidajen da Alhaji Mukhtar ya kyautar dasu ya bar ma mara su halin kama gida talakawa su xauna, ya kori occupant din ciki gaba daya wae ba kyauta kaninsa ya basu ba dama, a hka Ammi da yaranta suka xauna gidan cike da bakin ciki tunda basu da mai tsaya masu sae Allah, don cikin yan kwanakin nn da rasuwar mahaifinsu bbu abokinsa daya da ya sake lekosu, sun dae ci sa'a ya sa su private sch mai karamin kudi, ixuwa ynxu da Aneesah ke ss3 tana shirin xana waec da neco duk da sai term ya kusan karewa ma yake biyan kudin makarantar don sae suyi xaman sati shidda a gida basu je makaranta ba, kayan abinci kuwa idan ya ajiye masu buhun shinkafa da man gyada galon daya sae yyi kusan wata shidda bae waewayesu ba, ba karamin kkri Ammi ke yi ba don sbda future din 'ya yanta har wankau ta shiga yi, ta nn ne suka samu suke rufa ma kansu asiri. Bayan sati daya duk dan kayan abincin da Ammi ta siyo masu da kudin yusuf ya kare ta rasa yanda xata yi, don gidan da take wankau sun yi tafiya xuwa england tun wata daya da suka wuce, tayi jigum abun duniya ya isheta, gashi har kusan karfe goma basu karya ba jiya da daddare ma ba wani abincin kirki suka ci ba, don ita bata ma ci ba ta bar masu ganin bae da yawa ta sha ruwa kawae suka kwanta, Aneesah na xaune bakin kofa tana duba takardun makarantarta duk da yunwan take ji amma ko kadan bata nuna hkn ba tana ta karatu, yusuf ya shigo gidan don dama yana waje yana wasa da yara, ya fada jikin Ammi yace "ni Ammi yunwa nke ji," tayi shiru tana kallonsa, can ta kwalo ma Aneesah kira ta shigo ta nemi guri ta xauna tace "na'am Ammi," ammi tayi ajiyar xuciya tace "je wajen ladi mai kosae kice ta baki na dari xan kawo mata ko xuwa gobe ne," ta mike ta dauki hijab dinta ta fita daga gidan jikinta a sanyaye, tana isa ta tarda ladi na ta tuyan kosanta hankali kwance ga mutane cike wajen suna siyan kosae, ta dan ja gefe ta bari mutanen suka ragu snn ta bata sakon Amminta bayan ta gaisheta, ladi ta hade rai tace "ku ni fa ban ciki da cin bashin nn naku, kosan da idan an baku bashin ma ba biya kuke ba ynxu da xan xauna na lissafo bashin da kuka cin min wllh xae kai dubu daya, kullum gobe xa a kawo alhalin ba kawowan ake ba, to ni yau kullina bai da yawa bna bada bashi," ta ja tsaki ta ci gaba da tuyanta tana xage xage, a sanyaye Aneesah ta bar wajen ta koma gida ta xauna bakin kofa xata yi magana Ammi tace "shknn tunda bata ba ki ba," Aneesah ta dauke kanta kawae bata ce kmai ba, hka yusuf ya cika masu gida da kuka shi a bashi abinci yaci, Aneesah ta hade kanta da gwiwa ta shiga rera kuka a hankali a bakin kofar, ko Ammi ma bata san abinda take ba. [9:29PM, 12/21/2016] Khaleesat: ~Aneesah~ 2..... Aneesah na shirin islamiyya karfe hudu saura Ammi ta shigo gidan, ta karbi ledojin dake hannunta da sauri tanai mata sannu da xuwa ta fito mata da kujera waje snn ta debo mata ruwa a randa ta kawo mata, ta xauna gabanta tana tambayarta ya hanya, Ammi ta ajiye kofin ruwan dake hannunta bayan ta shanye ruwan tace "maxa ki tashi ki kama hanyar makaranta lkci na wucewa, ina yusuf?" tace "nace ya jirani yace shi su khabir xae bi," ta mike ta dauko goggen Hijab dinta da Nikaf ta saka snn tace "to Ammi sae na dawo," Ammi tayi mata Allah ya kiyaye ta fice daga gidan. Karfe bakwae saura su ka shigo gidan ita da kaninta, Ammi na share tsakar gida su ka yi mata sannu da gida suka shiga daki, tana gama cire uniform ta fito karbar sharan ammi tace "su yi sallah, ga abincinsu a kitchen," yusuf na ganin shinkafa da miyace ya dinga tsalle yana murna yau xa su ci shinkafa, Aneesah ta galla masa harara tace "yau ka saba cin shinkafa ne? wawa kawae," ya daga hannu xae kai mata kulli ta goce da sauri tare da kwala ma Ammi kira ganin wani kullin xae kai mata, Ammi ta shigo dakin da sauri ta raba ma kowa nasa tana masu fada snn ta nemi guri ta xauna tana kallon 'ya yan nata. Aneesah yarinya ce da bata wuce shekara 17 ba, sun taso cikin wahala da talauci tun bayan rasuwan mahaifinsu Alhaji Mukhtar, Alhaji Mukhtar shararren mai kudi ne a garin Abuja, Allah yyi masa rasuwa shekara takawas da suka wuce a hatsarin mota da yyi a hanyar sa ta dawowa Abuja daga kano bayan ya kai ma 'yan uwa da relatives ziyarar sallah, tun bayan rasuwarsa suka fara fuskantar kalubalen rayuwa duk da dukiyar da ya bari mai dumbin yawa don a lkcn ma gidajen da ya bari sun kai 6 bayan motoci da filaye, kiri kiri yayansa Alhaji shehu ya karbe komai nasa da sunan xae ajiye har sae yaransa sun mallaki hankalin kansu, Alhaji Mukhtar shine auta a gun mahaifinsu malam sule, da mahaifiyarsu saudat, su uku kadae Allah ya basu duk maxa, shehu, ibrahim da shi Mukhtar, tun yana primary Allah yyi ma mahaifiyarsu rasuwa, yana gab da gama secondary mahaifinsa ma ya rasu, tun daga lkcin komai ya tsaya masa don duk yayyinsa sun dauki karan tsana sun daura masa tun iyayensu na da rae bare ynxu da suka koma ga Allah, duk suka juya masa baya ga 'yan uwa ba xumunci, ya sha wahala sosae a rayuwa don da kyar da taimakon sana'ar da yake yi na wankin mota cikin ikon Allah ya kammala karatunsa ya sami