← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 91

Sashe 91

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Cikin ikon Allah yanzu cikinta yashiga wata tara harda ƙarin kwanki,  ganin yanda cikin nata yayi girma sosai ne yasa Oummu ɗaukota ta dawo da ita gabanta, nanfa Sooraj shima ya tattaro yadawo gidan Oummun dan kuwa baya taɓa iya bacci idan baiji ɗumin jikin Sunshine ɗinsa ba.
Awata ranan larabane naƙuda ya tashiwa Ziyada gadan gadan tun tana daurewa hardai Oummu tafahimta haka suka ɗauketa suka wuce da ita asibiti, SOORAJ kam gaba ɗaya yatashi hankalinsa idanunsa sunyi jajur kamar wanda zaiyi kuka,  matsanancin tausayinta yakeji.
30 minute kacal da shigar da ita labour room cikin sauƙaƙawa irin na Ubangiji ta haifo kyakkyawan ɗanta mai azabar kyau wanda kamanninsa da SOORAJ yayi over, har kamar an tsaga kara,  nan nurses suka kimtsa ta tare dayi mata alluran bacci don su naso tasamu hutu, kimtsa yaron sukayi inda suka fito dashi, ganin nurses din sunfito yasanya su Oummu sukayi kansu, ƙoƙarin miƙawa Oummu yaron wata nurse tasomayi da sauri SOORAJ yasa hannu ya amshi yaron, duban fuskar yaron yayi inda yahango matsanancin kamanninsa akan fuskar yaron, rungume yaron yayi acikin ƙirjinsa, take kuma saiga hawaye sun silalo daga cikin idanunsa.
Da SOORAJ da yaron duka Oummu ta haɗa ta rungume, itama ƙwalla ne yacika idanunta, cikin ranta takeyiwa Allah godiya, nan nurse ɗin tabasu izini inda suka shiga ɗakin hutun da aka kwantar da Ziyada,  ƙarasawa gaban gadon SOORAJ yayi tare da yin hugging ɗinta,   cikin yanayi irin na mayen baccin da take ciki tasaki murmushi, kiss yayi mata tare da kai bakinsa daidai saitin kunnenta ahankali yace "Thank you so much My Sunshine!."
Oummuce taƙaraso jikin gadon itama tare dayi mata sannu.
Haka Oummu tashiga ƙiran mutane tana sanar dasu batun haihuwar, koda Abba yaji tuni yasa akai masa booking flight don zuwa Abuja duba ɗan jikansa, bayan yasa ayi masa ordern zazzafan mota wanda zai bawa Ziyada amatsayin gift.  

Kulawa ta musamman Ziyada ke samu daga wajen kowa, yayinda Sooraj ya É—auki matsanancin soyayyar duniya ya É—aura akanta ita da yaronsa.
Haka ƴan uwa suka dinga zuwa suna duba Zieyaderhn Aunty Ounnaisa  da sauran ƴan uwa ma sunzo sun dubasa, haka Hajiya Mama tazo tayi kwanaki 5 sannan ta koma, ranan da aka cika kwana bakwai da haihuwa yaro ya amsa sunan. ABDALLAH wanda kuma babansa ne ya zaɓa masa sunan,  Sosai akasha shagalin suna anyi hidima sosai, inda SOORAJ ya gwadawa Ziyada matsayinta agaresa, don sosai ya kashe mata kudi ita da yaron ta.

***

After 7 month.

Shigowarsa ɗakin kenan, idanunsa ya zubawa Abdallah dake zaune atsakiyan gado yana wasa, murmushine ya bayyana akan fuskarsa, cikin matsanancin ƙaunar kyakkyawan ɗannasa daya zarta sa kyau ya ƙaraso jikin gadon, ɗaga yaron nasa sama yayi tare da rungumesa ya ɗaurasa akan shoulder ɗinsa, hugging ɗinsa tayi ta baya tare da ɓoye fuskarta abayansa, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da sanya hannunsa ya jawota ya zamana suna facing  juna. Sosai tayi masa kyau cikin shigarta na wata rigan net dake bayyana komai na jikinta,  sai kuma wani ɗan ƙaramin wandon jeans dake jikinta wanda iya karsa cinya, aje yaron yayi tare da sanya hannunsa yakamo waist ɗinta, cikin mayen soyayyarta dake jansa ya kashe mata idanunsa ɗaya tare da rungumeta.
Murmushi tayi itama tare da ɗan ɗaga ƙafafunta sama, bakinta ta ɗaura adaidai saitin kunnensa ahankali tace.
"I love you!."
Lumshe idanunsa yayi tare da ƙara hugging ɗinta, sosai yake shaƙan daddaɗan ƙamshin dake fita ajikinta.
Hannunsa yakai yana shafa hips É—inta ahankali, É—an É—ago fuskarta yayi cikin idanunta ya kalla, ahankali yace.
"I love you too  Sunshine."
Murmushi sukayi tare da haÉ—e bakinsu waje É—aya.
Zuƙatansu cike yake da matsanancin farinciki, inda soyayya ke ɗawainiya da zuƙatan kowannensu, haƙiƙa idan zuciyoyi suka haɗe waje guda, akan samu wata irin zazzafan ƙauna mai ban mamaki,  tazama HASKE acikin rayuwarsa, yayinda ita kuma yazame mata madubin dubawa.   Soyayya wata abace dake sanya zuciya nishaɗi, haka soyayya wata abace dake gusar da duk wata damuwa, haƙiƙa SOYAYYARSU acikin jininsu take.

(Alhamdulillah, dama ance laifin daɗi ƙarewa, anan nakawo ƙarshen labarin SOORAJ!!! ina roƙon Allah  Inda nayi kuskure da ya yafemin, inda kuma nayi daidai yasa mutane su amfana da hakan,  Allah yayafe mana zunubanmu baki ɗaya Ameen.   Saikunjini acikin sabon labarin dazan gabatar muku nan gaba,  godiya mai tarin yawa agareku masoyana, haƙiƙa kunnunamin ƙauna, kana kuma kun nunawa book ɗin SOORAJ tsantsar soyayya, nagode sosai, musamman masoyana na Wattpad bazan taɓa gajiya da gode muku ba, musamman yanda kuke min comments da kuma vote haƙiƙa inajin daɗin hakan, wannan nema yasa naji ƙarfin guiwa inda zan sake zuwa muku da sabon labari mai ratsa zuciya.
Kuyi haƙuri nasan wasu zasuce nayi ƙarshen cikin gaggawa, nima bahaka naso ba,  ina muku fatan farinciki  mai ɗorewa, sannan ina muku fatan alkhairi, Allah yasa ayi sallah lafiya, Allah Kuma ya nuna mana wata sallan dama wanda ke gaban gabanta Ameen, then karku manta da Happy Sallah na please😢 am waiting............ I LOVE YOU SO MUCH MY AMIABLE FANS🧡)

*Vote*
   *and*
*comment*

*30/July/2020*

             FATYMASARDAUNA
Chapter 91 · 0% Book details