← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 91

Sashe 67

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannunsa ya ɗaura adaidai tsakiyar  fatar bayanta dake shinning,  jin sauƙan hannu ajikinta yasanya ta sakin kwalban turaren humran dake hannunta, yayinda tayi saurin juyowa atsananin tsorace, hartakai ga  ƙirjinsu sun samu haɗewa waje guda, 
cikin mamakin ganinsa daf da ita ta ajiye idanunta akan faffaɗan chest ɗinsa, saboda  bazata iya juran kallon cikin fitinannun idanunsa ba.
Hannunsa dake kan naked skin ɗinta, ya sanya tare da ɗan jan bathrobe ɗin yayi sama,  inda yakawoshi harkan kafaɗunta, ahankali ya jawota gab dashi, cikin nutsuwa ya ɗaura hannayensa akan igiyoyin da zasu haɗe bathrobe ɗin su sanya ya kama jikinta, ahankali ya haɗo igiyan tare da sanya hannunsa yasoma ƙoƙarin ɗaure mata igiyoyin akan lafaffen cikinta, kokaɗan bai bari idanunsa sun sauƙa akan ƙirjinta dake aɗan buɗe ba, fuskarta kawai yake kallo,  yayinda ita kuma ta rufe kyawawan idanunta, wanda samansu ke ɗauke da zara zaran eye lashes, cikin son zame hannunsa daga jikinta, batare daya sani ba ƴan yatsunsa biyu suka gogi kan nipples ɗinta,  wani irin  yaaarrr  yaji ajikinsa, wanda koda wasa  baitaɓa jin kwatankwacin hakan ba.
Ita kuwa Zieyaderh rumtse idanunta tayi da ƙarfi,  tare dayin ƙasa da kanta, yayinda wani irin kunyaya rufeta.
Ahankali ya ɗauke hannunsa daga jikinta, tare da ɗan matsawa,  cikin takunsa mai ɗuke da nutsuwa ya nufi hanayar bathroom, tanajin rufewar ƙofar toilet ɗin tasaki wata  ƙatuwar ajiyar zuciya, tsikar jikintane  ke tashi, yayinda gefe guda kuwa taji wani irin sabon abu na baƙuntan gaba ɗaya gaɓɓan jikinta,  cikin jin kunyan abun daya faru, taƙarasa gaban ƙaton sif ɗinsa wanda aka jere mata kayanta daga ɗayan ɓangaren,  wata dark green ɗin doguwar riga mai faffaɗan  wuya ta zaro, cikin sauri sauri ta zura rigar ajinka.

Yanashiga cikin toilet ɗin yasoma ɓalle aninayen gaban rigarsa, cikin abunda aka aje a toilet ɗin musamman don ajiye kaya, ya ajiye rigarsa,  makunnin shower ya kunna tare da tsayawa ruwa na dukan murɗaɗɗiyar surar jikinsa, lumshe idanunsa yayi tare da sanya hannu ya dafe jikin  bango,  tunowa da yanda yaji ajikinsa ɗazun ne,  yasanyashi sake lumshe idanunsa,
tunowa da haka yasan yashi sake jin wani sabon abu ya tsarga masa tamkar awannan lokacin abun ya faru,  cikin yanayi nason ƙaryata kansa da abun dayakeji,  yaɗan soma jijjiga kansa, sam bayason zuciyarsa ta yaudaresa, tabbas yasan komai zaiji ayanzu to sharri da kuma yaudara ne irinta zuciya, koma mene bazai raɓa zama gaskiya ba.
Yajima sosai atsaye ruwa na dukan jikinsa, har saida idanunsa suka sanja kala daga farare zuwa launin ja, kafun ya kashe shower'n,
towel ɗin daya tsaya iyaka guiwarsa ya ɗaura, jikinsa na ɗigan ruwa haka ya murɗa handle ɗin ƙofar ya fito.
Jin motsin fitowarsa yasanya Zaieyaderh komawa kan gado da sauri ta kwanta,  tana me dafe saman mararta wanda takejinsa kamar akumbure, gaba ɗaya kwananan batajin daɗi ita kanta batasan meke damunta ba, takan daiji mararta na yawan murɗawa, yayinda takejin ƙasan marartata acike.

ƙarasawa gaban mirror' yayi aƙagauce ya shafa body lotion,tare da body spray ɗinsa mai daɗin ƙamshi, wani  blue crazy jeans tare da white t-shirt,
da kuma blue facing cap ya sanya, sosai yayi kyau ya fito acikakken handasome guy ɗinsa,   makullin motarsa ya ɗauka batare daya dubi inda take ba yasakai yafice daga cikin ɗakin.
Jin motsin  ficewar sa daga cikin ɗakin, yasanyata sake duƙunƙunewa waje ɗaya tare da lumshe idanunta,  ahankali sabon mood ɗin da ta samu kanta aciki ke ratsata,  yayinda yake ƙara shiga jikinta yana samun wajen zama, sannu ahankali ya mamaye gaba ɗaya jikinta, yayinda yasanya idanunta rufewa, tabbas ita awajenta hakan baƙon yanayi ne,  kuwa sam batasan da wani irin dan batasan da wani suna zata ƙirasa ba,   tunani ne  kala kala acikin rai da zuciyarta, haka tayita juyi har saida aka ƙira sallan magriba, tashi daga kwancen tayi, tare da wucewa bathroom ta ɗauro alwala.

Ahankali sautin cool music  ke tashi acikin  ƙawataccen club ɗin, daga gefe ƴan mata  da samari ne keta mu'amalansu awajen tamkar aƙasar turai,  yayinda kowa ke harkan gabansa.
Zaune yake akan wata haɗaɗɗiyar royal chair mai kyau, yayinda ya ɗaura ƙafafunsa bisa kan wani ɗan madaidaicin  table  ɗin dake gabansa. 
Bayansa yajingina da jikin kujeran, kana ya  lumshe idanunsa masu azabar kyau,  yakan zuwa club ne badon iskanci ba, haka kuma yakan zuwane badon wata manufa daban ba, yana zuwane saboda sometimes yakanji yanason abun dazaina ɗan ɗebe masa kewa, sannan kuma bakowani club yake zuwa ba, yana zuwa club ne, idan club ɗin ya amsa sunansa wajen haɗuwa,  idanunsa ya buɗe ahankali inda ya sauƙe su, akan wani guy dake zaune shi kaɗai yanata cikawa cikinsa wine,  kawar da kansa gefe yayi donshi sam kwata kwata ba'al adarsa bace shan wine ko alcohol, dubansa yakai kan screen ɗin wayarsa wacce ke  fitar da haske alama na  shigowar saƙo ko ƙira.
"Mas'oud." 
Shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar,  akasalance yayi picking call ɗin,
cikin unique voice É—insa yace. "Hello."

Ajiyar zuciya Mas'oud dake zaune cikin abokan business ɗinsu ya sauƙe, cikin gane alamun inda Sooraj ɗin ke zaune yace. 
"Club ko?."

Fuska Sooraj yaÉ—an ya mutsa cikin nuna halin ko in kula yace.
"Eh, akwai wani abu bayan hakanne?."

Cikin sanyi haÉ—i da kwantar da murya Mas'oud yace.
"RAJ yanzun fa bada bane yakamata kasani,  yanzu bakai kaɗai bane kamar da,  ka ajiye iyali, koda ace bakasonta yakamata ace kazauna da ita awannan lokacin, waima tsaya shin kama gwada abun da Dr. yace kayi?."

Wata ƴar murmushi Sooraj yayi cikin ƙosawa dajin maganganun Mas'oud ɗin yace.
"Kagama!."
Sarai Mas'oud yagane me Sooraj ɗin ke nufi, yasan hakan alamace dake nuna cewa Sooraj ɗin yagaji dajin maganansa, dama shi hakanan yake baka isa ƙiransa kuyi hira ba, magana ɗaya biyu sai ya kashe maka waya, aikuwa Mas'oud bai gama dawowa daga tunaninsa ba,  ƙit haka yaji Sooraj ya kashe wayar, sake gyara zamansa akan kujeran yayi tare da lumshe idanunsa, sosai tunaninsa yayi nisa izuwa gareta,  ajiyar zuciya ya sauƙe sakamakon tunowa da yanda yatsun hannunsa suka gogi kan nipple ɗinta,  murmushine ya bayyana akan fuskarsa, sam tunanin da yayi yanzu baisa yaji wani abuba, sannan kuma babu wata jijiya ajikinsa da tayi motsi, saɓanin tunaninsa na ɗazu da yaji wani irin abu ya ratsa har cikin tafin ƙafansa,
dama yasani idan harma yasaka rai to ya yaudari kansa, yasani sharrin zuciyane kawai, da ace yayarda yakumasa hakan aransa to tabbas da yasake yiwa zuciyarsa babban illa, saboda yarda da gaibu babban matsalane arayuwa.

Aƙalla sama da awa biyu Sooraj ya ɗauka zaune acikin club ɗin,  ƙarfe 12:15 am.
Ya baro cikin club ɗin,   cikin nutsuwa haka yake murza steering motar,  wani ɗan loka dake cikin motar ya buɗe, inda ya ciro kwalban maganinsa,  ɓalle murfin kwalban yayi, tare da watsa ƙwayoyin dake cikin kwalban abakinsa, haka ya haɗiyesu batare daya bi kansu da ruwa ba.
Kafun ma yaƙaraso gidannasu tuni 12:26 am.  Tayi cikin silently ya danna horn,  Maigadi wanda  idanunsa ke cike da magagin bacci ne ya wangale masa gate ɗin cikin hanzari,  cikin ƙaton parking lot ɗin gidannasu yayi parking motar,  kansa ya kifa ajikin steering motar aƙalla yaɗauki sama da mintuna 5 ahaka, kafun cikin salo da izza irin nasa ya buɗe murfin motar ya fito, kai tsaye cikin gidannasu ya nufa,  ko ina dake cikin falon ya ɗauki shiru ba abun dake tashi sai ƙaran AC.
LHar yakai bakin ƙofar da zata sadashi da part ɗinsa, muryar Oummu wacce ta ratsa cikin kunnuwansa, ita ta tilasta masa tsayawa.
Cikin kakkausar murya Oummu dake tsaye kan matattakalan falon ƙira sunansa.
"Sooraj!"
Cak ya tsaya cikin yanayi naɗan mamaki ya juyo,  makunnin ƙwan wutan falon Oummu ta kunna take haske ya gauraye ɗakin,   wani irin kallon tuhuma Oummu dake ƙarasowa garesa ta watsamai, ƙasa ya sadda kansa don sam bai tsammaci ganinta awannan lokacin ba.
"Daga ina kake?." Oummu ta tambayesa cikin ɓata fuska.

Sam bai wani iya ƙarya ba hakan yasa cikin muryarsa da ta ɗan sanja amo yace. "Club."
Kallonsa sosai Oummu tayi cikin ɓacin rai tace. 
"Hakan shine abun da kazaɓarwa rayuwarka ko? kabar yarinyar mutane cikin kaɗaici da kewa,  amma kai kasanya ƙafa katafi club, amatsayinka na wanda keda aure yakamata ace sai 12:30 am kake dawo gida?."

Shiru yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, cikin halin ƙosawa da tsayuwan yace.
"Am so sorry!."
Baki buɗe Oummu ke kallonsa, wato ma shiko ajikinsa, dan tsabar miskilanci irin nasa ita yake bawa haƙuri,  bama matarsa da ya aikata ba daidai agareta ba,  shiru Oummu tayi batare datace komai ba, saima zuba masa idanu da tayi, ganin haka yasanyashi murɗa handle din ƙofar da zata sadashi da part ɗinsa ya shige,
ajiyar zucia Oummu ta sauƙe, tare da girgiza kanta, afili tace. "Allah ya kyauta." juyawa tayi ta koma ɗakinta, don dama rashin jin motsin dawowarsa ne yahanata bacci.

Ahankali ya shigo cikin falon nasa wanda keta tashin ƙamshin turaren wuta, da'alama tunda yammaci aka sanya turaren amma kuma har zuwa yanzu ƙamshin nanan bai fice ba, handle ɗin ƙofar bedroom ɗin ya murɗa,  tare da tura ƙofar ciki kana yasa kansa acikin ɗakin, yana maida ƙofar ya sauƙe wata irin ajiyar zuciya, tare da ɗan juyowa ya sauƙe idanunsa akanta,  kwance take akan sallaya yayinda tayi matashin kai da hannunta, hijab ne ajikinta, kana cikin baccin nata da yayi nisa,  ta tattare gaba ɗaya doguwar rigan jikinta yayi sama, hakanne yayi sanadiyar bayyanan fararen ƙafafunta, wanda sukasha zanen jan lalle gwanin ban sha'awa.
Chapter 67 · 0% Book details