← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 91

Sashe 61

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mas'oud ne ya buɗe murfin motar ya shigo, saidai ba inda Sooraj ke zaune yashiga ba ɓangaren driver ya shiga tare da yiwa motar key,    tunda ya sunkuyar da kansa ƙasa bai ɗagoba harkawo yanzu da suka kawo cikin katafaren gidannasa. Mas'oud na gama daidaita parking motar ya juyo da kallonsa ga Sooraj  baikai ga cewa Komai ba,  Sooraj ya buɗe murfin motar ya fita, sam bayako iya ganin gabansa da kyau hakan yasa yake ta gauraya hanya tamkar wanda ke cikin maye, kamar kububuwa haka ya wuce zuwa ɗakinsa dake sama, yana shiga yasoma kiciniyar cire babban rigan dake jikinsa, ƙarasawa gaban tangamemen glass mirror ɗin dake cikin ɗakin yayi, duban kansa da yayi acikin mirror ɗinne yasanyashi jin wani irin ɗaci amaƙoshinsa, cikin wani irin zafin nama haɗi da ƙunci, damuwa, da takaici yasanya hannunsa ya daki mirror'n, take mirror'n ya tarwatse, yayinda hannunsa kuwa yashiga zub da jini,  cikin wani irin tururin ɓacin rai dake damunsa yasanya hannunsa gaba ɗaya yayi watsi da gaba ɗaya kayan shafan dake jere reras agaban mirror'n, wani irin ƙara yasanya tare da soma buga kansa ajikin bango, daidai lokacin Mas'oud ya ƙaraso cikin ɗakin,  ganin abun da Sooraj ɗin ke aikatawa, sannan ga kuma hannunsa dake zubar da jini,  yasanya Mas'oud ƙarasowa cikin ɗakin da sauri, cikin tsananin tashin hankali yace.
"Sooraj ka......"

"Shut up Mas'oud!!!" Sooraj yafaɗa atsawace wanda har saida Mas'oud yaɗan tsorata, cikin tsananin ɓacin ran dake cinsa azuciya yace.
"Mekuka aikata kenan Mas'oud? Nace me kuka aikata!!" Kunsan abun da kukayi kuwa?"
Azafafe ya shaƙe wuyan rigar Mas'oud cikin wata irin murya me amo, wanda tunda Mas'oud ɗin yake baisan cewa Sooraj  na da'ita ba yace.
  "Why do you do this to me? mehakan da kukayi yake nufi? You already know my problem Mas'oud!  you know dat i am not a complete man, meyasa kuka zaɓi cutar da ita? bazan zauna da ita ba Mas'oud! bazan Zauna da ita ba!!"
Gaba É—aya cikin ficewar hayyaci SOORAJ ke faÉ—an maganganun.
Tsananin damuwa ne ya bayyana akan fuskar Mas'oud cikin son kwantarwa da Sooraj  hankali yace.
"Kadawo cikin hankalinka Sooraj, kai musulmi ne kasan ƙaddara kuma tana iya sauyawa ako da yaushe, sannan kyakkyawa takan iya zama mummuna,  mummuna kuma takan iya zama  kyakkyawa, dan Allah Sooraj kada ka aikata abun da zuciyarka ke shirya maka,  nasan matsalanka Sooraj nasani amma nasan bazaka taɓa tabbata ahaka ba, nayarda dacewa wannan auren rufin asirine agareka dan Allah RAJ ka tausashi zuciyarka, kadawo cikin nutsuwarka!"
Mas'oud ya faɗi haka idanunsa cike tab da  ƙwalla, tabbas ya hango tsananin damuwa da tashin hankali akan fuskar SOORAJ, amma basu da wani zaɓi, tunda Allah ya riga da yayi nasa.

Iska SOORAj ya fesar ta bakinsa tare da rumtse jajayen idanunsa, wani irin azababben ciwon kai yakeji, yayinda yakejin gaba ɗaya duniyar na juya masa,   ahankali ya taka tare da  ƙarasawa gaban bedsite ɗinsa, cikin zaƙuwa ya buɗe drawer'n  bedsite ɗin, wata kwalba ya ciro wanda cikinta ke ɗauke da magani,  cikin rufewar ido ya ɓalle  murfin kwalban tare da kafa bakin kwalban acikin nasa bakin,  arazane Mas'oud yayo kansa daniyar hanasa shan maganin, amma kafun yaƙaraso tuni Sooraj ya shanye maganin tas, cikin zafin nama Mas'oud ya ƙwace kwalban maganin daga hannun Sooraj cikin nuna damuwa yace.
"Please calm down RAJ, dan Allah ka nutsu kada kayiwa kanka illa!"

Kan gado ya faɗa tare da rumtse idanunsa, jiyake kamar zuciyarsa zata fashe, wasu baƙin abubuwane ke ziyartan tunaninsa,   akusa dashi Mas'oud ya zauna tare da sanya hannayensa ya rufe fuskarsa, sosai damuwar abokinnasa ke damunsa, musamman yau da yaga gaba ɗaya RAJ ɗin ya fita a hayyacinsa, sai yakeji inama da ba'a haɗa baki dashi wajen ɓoyewa SOORAJ auren ba.
Tarin da Sooraj É—in keyine yasanya Mas'oud juyowa ya kallesa, wani irin guda gudan jini dayaga yana fita abakin Sooraj É—inne yasanyashi zaro idanunsa cikin tsananin kaÉ—uwa yace.
"RAJ dan Allah kada kayiwa kanka illa!"
Wani farin handkerchief yasanya ya goge jinin dake  fita abakin sa, cikin ƙarfin hali ya sauƙo daga kan gadon,  toilet ya nufa yana shiga ya wanke bakinsa tare da watsawa fuskarsa ruwa, wani irin dishi dishi yake gani yayinda  jiri ke neman kadashi, adaddafe yafito daga toilet ɗin, zuwa lokacin  baya  ko iya ganin gabansa, hayyacinsa ne ke neman barin jikinsa, kan gadonsa ya faɗa, lokaci guda idanunsa suka rufe ruf..

Ganin haka yasanya Mas'oud lulluɓa masa blanket, wayarsa ya ciro ya dannawa Dr.Waleey  likitan Sooraj ɗin ƙira, bayanin komai yayi masa, nan Dr.Waleey yace gashinan zuwa, mintuna kaɗan saiga  Dr.Waleey  yaƙaraso gidan, duƙufa yayi sosai akan Sooraj ɗin wajen gano matsalarsa,  ganin cewa maganin da Sooraj ɗin yasha yana da illa sosai ne yasanyashi yi masa wata allura wanda zata sauƙaƙawa jikinsa wajen gusar da duk wata wahala,
  kallon Mas'oud Dr.Waleey yayi cikin kulawa yace.
" Wani abu ya ɓata masa rai ne?"
Ajiyar zuciya Mas'oud yayi tare da jinjina kansa alamar.
"Eh"

Cikin tausayawa Dr.Waleey yace.      
"Ciwonsa yayi worse yakamata kuna kiyaye ɓacin rai ko wani abu da zai na taɓa zuciyarsa, sannan yana da buƙatar kulawa ta musamman"
ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da cigaba da cewa.
"Ina tsananin tausayin Sooraj Mas'oud, saboda Allah ya haɗasa da ƙaddarori masu girma, saidai ina masa fatan samun sauƙi akoda yaushe"
Wasu magunguna ya ciro daga cikin jakarsa kana ya miƙawa Mas'oud, cikin kulawa yace. "Idan yatashi katabbatar yasha waƴannan magungunan zasu taimaka sosai!"
Kai Mas'oud ya jinjina tare da yiwa Dr.Waleey godiya daga haka sukayi sallama,  zama Mas'oud yayi akan wata lallausan kujera dake cikin ɗakin tare da kai dubansa ga Sooraj wanda ke kwance kamar gawa, wani irin hawayene suka cika idanun Mas'oud  har suka samu daman gangarowa, bayansa ya jingina  da jikin kujera tare da lumshe idanunsa.

Ahankali idanunta ke buɗewa harta gama waresu tas, tashi zaune tayi tare da kai dubanta ga  cannula'n dake ɗaure a tsintsiyar hannunta, bayanta ta jingina da jikin gadon da take kwance, ahankali hayaniyan jama'an da suka cika gidan ke ratsawa cikin kunnuwanta,    sake lumshe idanunta tayi yayinda wasu siraran hawaye suka samu daman gangarowa daga cikin idanunta,  hannunta takai ta dafe saitin zuciyarta dakeyi mata zafi,  daidai lokacin aka turo ƙofar ɗakin nata, da sauri tasanya bayan hannunta ta share hawayen nata,
  Oummu da Aunty Laylerh ne suka shigo cikin ɗakin, ganinta azaune yasanya murmushi  bayyana akan fuskarsu,
cike da kulawa Oummu tace "Sannu Zieyaderh kintashi ya jikin?"
Cikin sassanyar muryarta wacce ke ɗauke da zallan damuwa tace "Da sauƙi!"
Aunty Laylerh ne ta zauna akan gadon tare da ɗan taɓa jikin Zieyaderh'n cikin kulawa tace "Masha Allah zafin jikin ya sauƙa, yanzu me kikeji ajikin naki?"

Ita kanta bazata iya tantance me takejiba saboda ciwon ba ajikinta yake ba azuciyarta yake, rashin sanin abun da zatace yasanya kawai ta nuna kanta, cikin kulawa Aunty Laylerh tace "Sannu ko"
Duban Oummu tayi tare da cewa, takawowa Zieyaderh'n tea me kauri da abinci idan taci sai tasha magani,   hakan kuwa akayi Oummu da kanta ta haɗa mata tea da kuma pepper chicken,   Aunty Laylerh da kanta tasanya Zieyaderh agaba akan cewa lalle dole sai tasha tea din, duk da cewa batajin daɗin bakinta haka dole ta daure taɗansha tea ɗin kaɗan,  koda ta nuna ta ƙoshi Aunty Laylerh da kanta tashiga bata naman abaki, da ƙyar ta iya cin kaɗan ta kauda kanta gefe alaman ta ƙoshi, 

shigowar Aunty Muhibbat cikin ɗakinne yasanya Aunty Laylerh cewa takai Zieyaderh'n tasakeyin wanka daganan sai a shiryata tunda dai sunga jikinnata daɗan sauƙi,   wani irin ingantaccen ruwa wanda yaji haɗaɗɗen turaren wanka Aunty Muhibbat ta haɗa mata,  ahankali take takawa saboda gaba ɗaya jikinta ba ƙarfi, toilet ɗin ta shiga tare da zare rigar jikinta,  dayake ruwan nada ɗan ɗumi hakan yasa ta kwanta lif acikinsa, wani irin ajiyar zuciya ta sauƙe tana mejin wani sabon yanayi nashiga jikinta, cikin rashin kuzari haɗi da kasala  tayi wankan inda gaba ɗaya jikinta yasake gaurayewa da daddaɗan ƙamshi, alwalan sallan Azahar tayi kana fito daga cikin toilet ɗin,  cikin ɗan kuzarin daya rage mata yayi sallah  inda Oummu ta taturo Bilkh don ta gyarata.   Kasancewar bata wani jin daɗi yasanya Bilkh yi mata light meckup, hakan kuwa baƙaramin fito da kyawunta yayi ba, wani haɗaɗɗen lace wanda yaji ɗinkin doguwar riga fitted gown tasanya, sosai leshin ya amshi jikinta kasancewar lace ɗin nada kalan ja, hakan yasa Bilkh ta naɗa mata ƙaton white vail ajikinta mai adon jan duwatsu,  sosai tayi kyau, saidai ƴar rama kaɗan data bayyana ajikinta, yanayin yanda bilkh ta naɗa mata mayafinne yasanya yaɗan rufe rabin fuskarta kaɗan, Aunty Muhibbat ce tariƙota suka fice daga cikin ɗakin, kaitsaye ɗakin Oummu suka nufa,  Oummu ce ita kaɗai zaune akan gado, akusa da ƙafan Oummu Aunty Muhibbat ta ajiyeta kana ta juya ta fice daga cikin ɗakin,   cikin nutsuwa Oummu ta ɗago Zieyaderh kana ta kawota kusa da ita, cikin tsananin kulawa tace.
"Cikar mutumcin ko wacce ƴa mace shine aure, haka kuma duk wata ƴa mace tana sanin ƙima da darajar kanta ne aduk lokacin da tayi aure, kamar yanda kika sani yau anɗaura miki aure  saboda haka  kin tashi daga sunan budurwa kin zama matar aure" ɗan numfasawa Oummu tayi tare da kamo hannuwan Zieyaderh cike da tausayawa tace
"Kigafarceni Zieyaderh, haƙiƙa ban aikata haka daniyar son zuciya ba, nayi hakane saboda inganta rayuwarku ku duka biyun, nakumayi hakanne amatsayina na uwa mai son cigaban ƴaƴanta,  bansan yazakiji ba amma yazama dole na faɗa miki"  sake hannun Zieyaderh'n tayi tare da sanya hannu ta ɗan ɗage mayafin dake kan Zieyaderh'n,  hakan yasanya Zieyaderh taɗan ɗago ta kalleta, cikin kulawa Oummu tace.

"Anɗaura aurenki yau saidai kuma bada Almustapha aka ɗaura ba, kamar yanda kike tunani, nasan zakiji abun wani iri amma ƙaddara ta riga fata!"

Ɗago idanunta dake cike da mamaki tayi ta kalli Oummu,  hannunta Oummu tasake kamawa cikin son kwantar mata da hankali tace
"Ƙwarai bada Almustapha aka ɗaura miki aure ba, dan Allah Zieyaderh kiyi haƙuri ki karɓi wannan ƙaddaran!"
Chapter 61 · 0% Book details