← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 91

Sashe 66

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itakuwa Zieyaderh tana shiga falon nasu aje basket ɗin tayi, inda ta zauna akan ɗaya daga cikin royal chairs ɗin da suka ƙawata tsakiyar falon,  kasancewar bata wani jin yunwa sosai hakan yasanya bataci abincin ba, idanunta ne suka sauƙa akan wani haɗaɗɗen hotonsa wanda ke saƙale ajikin bango, sosai hoton yayi kyau yayinda aka sirrantashi cikin wani glass mai tsada, ahankali tashiga takawa harta ƙarasa inda hoton yake,  idanunta ta tsurawa hoton tare da sakin wani murmushi,  ahoton sanye yake da army jeans black and black t shirt, yayinda yasanya wasu kyawawan combat shoe suma kalan baƙaƙe aƙafansa, yanayin tsayuwar da yayi acikin hoton, yasanya shi yin kyau sosai, murmushi taƙarayi tare da kai hannunta daidai saitin bakinsa, sosai murmushin dake ɗauke akan fuskarsa ta ƙara bayyana tsantsar kyawunsa.
"Kafi kyau idan kana murmush!."
Tafaɗi maganar acikin zuciyarta, sai dai abun da bata sani ba shine maganartata tafito fili,  ahankali tasanya hannunta ta shafo kan kyakkyawar fuskarsa,  aranta tace.
"Kai É—in na dabanne! babu wani É—a namiji dazai gwada maka komai, koba kyauba kana da abun da sauran maza basu dashi."
Lumshe kyawawan idanunta tayi tare da ɗan matsawa daga jikin hoton, juyowan da zatayi idanunta suka faɗa cikin nasa idanun, ƙirjinta ne taji yaɗan buga, cikin yanayi na ɗanjin kunya tayi ƙasa da kanta, shima ɗauke idanunsa daga kanta yayi tare da  raɓawa ta gefenta ya wuce, ƙasa ƙasa tabi sa da kallo harya fice daga cikin falon, sosai yayi kyau cikin ssbuwar shigar daya kuma sauyawa, lumshe idanunta tayi tare da komawa cikin falon ta zauna, luf tayi akan kujera tana mejin wani irin tsananin shauƙi na ratsa gaba ɗaya jikinta, wani irin abu takeji ajikinta wanda batasan dame zata ƙirasa ba, tanajin gaba ɗaya tsikar jikinta na mimmiƙewa, haka tayita juyi akan kujera daga ƙarshe bacci ya ɗauketa batare da ta shiryawa hakan ba.

Gyara zama Mas'oud yayi tare da duban Sooraj wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa, ɗago idanunsa yayi ya kalli Dr.Waleey, cikin yanayin dake nuna damuwa akan fuskarsa yace.
"Idan har kuma kun gazo gano matsalar RAJ, hakan nanufin kenan sihiri ne ko kuna shafan aljanu."

Murmushi Dr.Waleey yayi tare da girgiza kansa, cikin son kwantar musu da hankali yace.

"Sam ba asiri bane bakuma shafar aljanu bane kamar yanda kayi tunani, sau dayawa Allah kan jarrabi bawansa ta ɓangarori daban daban, wata jarrabawar abayyane take wata kuwa takan zuwa aɓoye, sannan acikin gaba ɗaya mutanen duniya babu wani wanda ya isa ya gujewa ƙaddararsa, me kyu ko akasinta, Ƙarfin ikon Allah ya wuce tunani, tayanda zai iya jarrabanka da komai,  haƙiƙa Allah na jarraban bawansa da jarabawa mafi girma, sau dayawa kuma idan Allah ya jarrabi bawa da jarrabawa mafi muni sai hankalin wasu daga cikin mutane ya gushe, har ta kaisu ga mantawa da ƙarfin ikon Allah, Idanunsu kan rufewa, sukan dage akan cewa asiri akaiwa mutum, bayan kuma babu wani wanda yayi masa asiri jarrabawace kawai daga Allah!."
ÆŠan numfasawa yayi tare da shafa sumar kansa, kallon Sooraj yayi da kyau, cikin tsananin tausayin Sooraj É—in da yakeji yaci gaba da cewa.

"Haƙiƙa kai ɗin maitawakkaline, sannan kuma kana da ƙarfin imanin riƙo da ƙaddara, tabbas jarabawar da Allah ya ɗaura maka mai matuƙar girmace, bakowani Namiji bane zai iya juran rufe sirrinshi tare da fawwalawa Allah Lamuransa kamar yanda kayi ba,  Baka da matsalan komai Sooraj, kuma kaima watarana Insha Allah zaka zama cikakken Namiji mai lafiya, watarana kai da kanka zakayi mamakin kanka, Insha Allahu bazaka taɓa tabbata ahaka ba!." Dr.Waleey yakai ƙarshen zancen cikin tausasa murya.

Ajiyar zuciya Mas'oud yayi cikin sanyi yace da Dr.Waleey
"Tayaya?"

Still murmushi Dr.Waleey yayi, zamansa ya gyara da kyau, tare da gyara zaman glass É—in dake idonsa.
"Tabbas zai iya zama cikakken namiji kuma lafiyarsa zata iya dawowa ako da yaushe,  zai iya samun sauƙi idan har ya kawar da duk wani tunani tahanyar sarrafa matarsa koda ko bayajin daɗi."
Shiru yayi kana yacigaba da cewa.
"Kusanci da mace zai iya daidaita komai, sannan yawan raɓan mace zai iya rage masa kaso 30 acikin 100 na matsalar dayake tattare da ita."
Sake kallon Sooraj da haryanzu kansa ke ƙasa yayi cikin lallami yace.
"Ka gwada jarrabawa Sooraj, domin lafiyarka abun buƙatace agareka, Namiji baya taɓa zama ingarma kuma jajirtacce, harsai yakasance yana iya biyawa matarsa buƙata, haƙiƙa nasan cewa kaiɗin gwarzone, saidai kuma irin wannan rashin lafiyan taka zata iya haifar da babban matsala arayuwarka, idan ka gwada za a dace insha Allah, matsalace da ka soma jinta ajikinka tun shekatu 8 da suka wuce, bada ita aka haifeka ba saboda haka zaka iya, watarana kuma zakayi mamaki."

Lumshe idanu Mas'oud yayi tare da buɗesu alokaci guda,  kallon Dr.Waleey yayi tare da basa hannu sukayi musabaha, cikin ɗan sukunin da ya samu acikin ransa najin cewa amininsa zai samu lafiya yace.
"Mungode sosai doctor!."

Nan sukayiwa Dr.Waleey sallama, shidai Sooraj ƙala baice daga bakinsa ba har suka bar cikin asibitin, hasalima wani irin abune yaji ya toshe masa maƙoshi. 
Tunda suka shiga mota babu wanda yace da É—an uwansa wani abu, agaban tangamemen gate É—in gidansu Sooraj É—in, Mas'oud yayi parking motar.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da kallon Sooraj wanda yajingina bayansa da jikin kujeran motar.

Cikin kulawa Mas'oud ya ƙira sunansa.
"RAJ!."
ÆŠago idanunsa wanda suka É—an soma sanja launi Sooraj yayi ya kallesa.

Idanu Mas'oud yaÉ—an lumshe cikin son samawa Sooraj É—in nutsuwa yace.
"Tabbas nayarda, kamar yanda Dr.Waleey yace idan ka jarraba zaka iya, please RAJ ka jarraba."

Murmushin dayafi kuka ciwo ne ya bayyana akan fuskar Sooraj, cikin cool voice ɗinsa yace. 

"Ƙaddara itace wacce tarigayi fata Mas'oud, kamar yanda Dr.Waleey ya faɗa hakane, ƙaddarata tana da girma sosai,  banso shigowarta cikin rayuwata ba Mas'oud, saboda nafi kowa sanin menene illata,  bazan amfaneta dakomai ba, sannan aurena yazama laluri agareta, aurena zai kashe mata ƙuruciyarta zai kuma kashe mata lokacinta, anayin aure ne don aji daɗi akuma raya sunna, bazan taɓa iya jiyar da ita wannan daɗin ba Mas'oud, saboda ina ɗauke da Nakasa." Ɗan tsagaitawa yayi da maganan, still murmushi yayi tare da lumshe idanunsa, cikin sanyin murya yace.

"Kasan yanda nakeji akanta kuwa Mas'oud?  Bansan daliliba amma kowani bugun zuciyata da tunaninta yake tafiya, Inajinta awani ɓangare na jikina, tayaya zan cutar da yarinya ƙarama kamarta? duk wata mace indai bata kasance marar lafiya ba tabbas nasan tana buƙatar Namiji akusa da ita, Ni nakasance saɓanin tunanin mutane, bazan amfaneta ba." Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ɗan cije laɓɓansa, yanzun kam sosai rauni ya bayyana akan kyakkyawar fuskarsa, tunda yake bai taɓajin ciwo da ɗacin rashin kasancewarsa lafiyayyen namiji ba sai yau, dama irin wannan ranan yaketa gudu, shiyasa ya keɓe rayuwarsa daga sha'anin mata, irin wannan raunin yake gujewa kansa shiyasa ya nesanta kansa da soyayya, gashi duk iyaka gudunsa ranar ta riskesa,  ɗago idanunsa yayi ya kalli Mas'oud wanda ƙwalla suka cika idanunsa tab, murmushin daya sanya hawayen dake cikin idanunsa gangarowa yayi tare da cewa.

"Zanyi abun daya dace Mas'oud!."

Yana kaiwa nan azancensa ya buɗe murfin motar ya fito, Da kallo Mas'oud ya bisa harya buɗe tangamemen gate ɗin gidannasu ya shige, hawayen dake cikin idanun Mas'oud ne suka samu daman gangarowa waje, wani irin tausayin abokinnasa yakeji, cikin sanyin jiki yaja motarsa yabar ƙofar gidan.

Tsaye take agaban dressing mirror, wani haɗaɗɗen humra wanda Hajiya Arabi ta bata, take shafawa ajikinta, gaba ɗaya ko ina dake cikin ɗakin ya cika da ƙamshin humra'n nata,
gaba ɗaya ta shagala da abun da takeyi, sanye take da bathrobe pink colour ajikinta, wanda ya tsaya iyaka cinyarta,   kunce igiyan bathrobe ɗin tayi tare da ɗan zamesa ya sauƙa zuwa kan ƙugunta,  humra tashiga shafawa akan ƙirjinta har zuwa kan kafaɗunta,  sam ta manta da cewa ma aɗakinsa take, gaba ɗaya ta saki jiki, daga gefe guda na zuciyarta kuwa, mamakin  ɗaukewan period ɗinta take, don yau kwata kwata kwanansa ɗaya amma ya ɗauke, baikuma taɓa yi mata haka ba,     ahankali ya murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ya shiga,  tsaye yayi ajikin ƙofar yana me ƙare mata kallo tundaga sama har ƙasa, santala santalan legs ɗinta dake ta shinning ya kalla, kana ya sauƙe idanunsa akan bayanta wanda ya matuƙar fidda shape ɗin gefe da gefen cikinta, yayinda fatar bayan nata ke shinning tana fidda wani irin ƙyalli, lumshe idanunsa yayi ahankali ya soma takowa zuwa gareta,  sam batasan da shigowarsa cikin ɗakin ba, gaba ɗaya hankalinta yayi nisa wajen rufe kwalban humran dake hannunta, taku ɗaya ne kacal ya rage atsakaninsu, tsayawa yayi, yayinda sosai ƙamshin da jikinta ke fitarwa yayi masa daɗi, ɗan lumshe idanunsa yayi, hannunsa dake rawa yakai kan fresh skin ɗin dake tsakiyar bayanta.

Azabure Pharouk yayi wurgi da laptop ɗin dake hannunsa, wani irin tuƙuƙin baƙinciki da ɓacin rai ne suka cika idanunsa har suke neman rufe ganinsa, jikinsa ne ya ɗauki rawa tamkar mazari, cikin ƙunan zuciya yafara sambatu lokaci guda kuma yasaki wata mahaukaciyar dariya mai cike da ƙeta,  abayyane yace. 
"Aure ko, hmmm lallai kuwa mu dukanmu zamu rasata,  aurenta da kayi bashike nuna cewa ka mallaketa ba SOORAJ! tabbas kashiryawa rashinta daga yau zuwa sauran ranaku masu zuwa."

(kuyi haƙuri two days bana baku updated da wuri, insha Allah yanzu zannayin ƙoƙarin baku update akai akai saboda inason nima na ƙare labarin soon!)

*Vote*
    *and*
*Comment*
 

      fatymasardauna

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

          *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

             *WATTPAD*
       @fatymasardauna
#Destiny.

*(Wannan fejin gabaki ɗayansa na sadaukar dashi agareki.My Aunty, AISHA ALI GARKUWA. Allah Yaƙara miki lafiya da nisan kwana, Ameen.)*
          

             *Chapter 47*
Chapter 66 · 0% Book details