← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 91

Sashe 45

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manta biology text book  ɗinta da tayi, yasanya ta taho cikin sauri don komawa ta ɗauka, sam bata kulaba saiji tayi sunyi karo da juna,  wanda hakan yajawo zubewan documents ɗin dake  hannunsa.  Da sauri taja da baya ƙirjinta na bugu da ƙarfi, idanunsu ne suka faɗa cikin na juna, hakan yasanya taji tamkar an jona mata shocking,      kallonta yayi sannan ya kalli ƙasa inda documents ɗinsa suka zube,  da sauri ta durƙusa ƙasa hannunta har rawa yake wajen harhaɗa documents ɗin waje ɗaya.    Agogon hannunsa ya kalla yaga 7:30 kuma sai ya biya ta office kafun ya wuce airport, gashi duk gani yake kamar bata sauri wajen tattara documents ɗin.  Itakuwa bakomai ke cinta ba face tsoro hakan yasa gaba ɗaya bata sauri, ƙamshin mayen turarensa dake zautar da ita ne, ya daki hancinta sosai, hakan yasa ta ɗan ɗago da kanta, daidai lokacin shi kuma ya ɗan ranƙwafo don tattare documents ɗin, kanta ne ya bugi haɓanshi wanda hakan yasashi rumtse ido, ahankali yace "Auchhhh!!"  dan ya ɗanji zafi sosai.
Sakin documents ɗin tayi tare da sanya hannuwanta ta rufe bakinta, wani sabon tsoro ne  yasake kamata, baki na rawa tace "Kayi haƙuri Wallahi bansaniba ne!!"

Baikulata ba haka yasanya hannu ya shiga tattara papers ɗinsa da suka watse.  ganin haka yasa itama tashiga tayasa tattarewa,  gaba ɗaya ƙamshinsa ya jefata acikin wani irin yanayi, jin kanta take cikin wani  baƙon yanayi, har wani iska ne ke shiga jikinta.   Idanunta ne yakai kan wani papers da iska ke shirin kaɗasa wani wajen, da sauri takai hannunta zata kamo paper'n,  shima hannunsa yakai batare da yayi zato ba yaji hannunsa ya sauƙa akan nata, atare sukaji wani shock da sauri yajanye hannunsa daga kan nata tare da ɗaukan paper'n ya miƙe tsaye, baijira komai ba ya nufi wajen motarsa wanda tuni dama driver na jiransa, yana shiga gidan baya driver yayiwa motar key suka fice daga cikin gidan.   Saida taji alamun fitansu sannan ta iya miƙewa tsaye daga tsugunnen da take,  batare da ta saniba wani murmushi ya bayyana akan fuskarta take kuma saiga hawaye sun ziraro daga cikin idanunta, Wallahi ko za akasheta bazata iya fassara abun da takeji dangane dashi ba, tausayi ne? rauni ne? Ita duk takasa ganewa, tasan koma menene tabbas abun da takeji akanshi na musammanne,  idanunsa kaɗai da ta kalla ya sanya taji wani iri ajikinta, tabbas da zata samu mai bata amsar abun da takeji dangane dashi da taso hakan fiye da komai, watarana idan tagansa sai taji kamar tasanya masa kuka, watarana kuwa jitake kamar taje da gudu ta shige jikinsa tayi kuka sosai, wataƙila hakan zai ɗan sama mata salaman abun dake ranta.    Sam tama manta da cewa text book zata ɗauko sai kawai ta koma tashiga mota.
Luf tayi ajikin kujeran motar,  ƙamshinsa da har yanzu takejinsa acikin hancinta shiyayi fatali da duk wata nutsuwarta, sam tarasa me yasa takejin ƙamshin nasa har yanzu duk da cewa baya tare da ita,  hannunta takai tashafi fuskarta, sai alokacin ta gano daga inda ƙamshin ke fitowa, sake kai hannunta kan hancinta tayi tare da shunshunawa, tabbas hannunta da ya taɓa ne ke ƙamshin, wani irin sanyi taji acikin zuciyarta, ɗaura hannun tayi akan fuskarta tare da lumshe idanu, ahaka har suka iso cikin school ɗin.  Yau kam tayi late duk da cewa bahaka tasoba, don sunada biology, kuma shine first period, bakuma taso tayi missing lecture ɗin biology ko kaɗan,     ai kuwa tana zuwa bakin class ta iske malami aciki, da ƙyar ya barta tashiga cikin ajin, tana zama akan chair ta sauƙe ajiyar zuciya, hannu Nasmah tasanya ta ƙasa ta muntsineta akan cinyarta,   ƙasa ƙasa tayi dariya tare da rumtse ido alaman taji zafin muntsinin, hakan da tayi kuma sai ya tuna mata da MR.HELPER ɗinta, yanayin yanda ya rumtse idanunsa da kuma yanda yace "Auchhh!!" Baƙaramin kyau yanayin yayi masa ba, musamman yanda pink lips ɗinsa suka motsa abun saiya ɗauki hankalinta, sai ayanzu moment ɗin kedawowa cikin brain ɗinta da kyau, wani murmushi tasake tare da lumshe idanunta.
"Kenan shima yanajin zafi idan abu yasameshi?" A zuciyarta ta tambayi kanta, wani murmushin ta sakeyi alokacin da ta tuna da kyawun idanunsa, a iya tsawon rayuwarta itakam bataga irinsa ba, bata kuma tunanin zata taɓa ganin wani irinsa.    Ataƙaice dai  har biology teacher'n yafita, bata tsinci komai daga cikin darasin daya koyar ba,  gaba ɗaya hankali da tunaninta yau akan Mr.Helper yake. 
Su Shukra da kansu yau sun fuskanci cewa tana cikin farinciki, don koda aka fita break zagewa tayi tayita zuba musu surutu. 

7:59 AM

Gyara zama yayi tare da ɗaura sit belt ajikinsa, bayansa ya jingina ajikin luntsumemiyar kujeran dake cikin jirgin, 8:00 daidai jirginnasu ya ɗaga zuwa sararin samaniya,  tafin hannunsa yakai ya rufe fuskarsa, ko hakan zaisa yaɗan rage stress ɗin dayake ciki, ahankali yaji wani baƙon ƙamshi na ratsa cikin hancinsa yana me cakuɗa da numfashinsa, mamakine yakamasa don sam baisan daga ina ƙamshin ke fitowa ba, ɗan waigawa bayansa yayi,  dayake  ɓangaren business class ne kowa sha'aninsa kawai yake, babu kowa kuma akusa dashi dasai yace na kusa dashine ke ƙamshin.  Sake shunshuna hannunsa yayi, sai alokacin ya tabbatar da cewa tabbas hannunsa ne ke ƙamshin, bawani turarene me ƙarfi ba, irin dai turaren nanne da idan mutum yasa saima ka matso kusa dashi kafun kajiyo ƙamshin.   "Itace!" yafaɗa in a silent voice ɗinsa, sake kai hannun kan hancinsa yayi tare da ɗan taɓe lips ɗinsa.   Azuciyarsa yace.
"Su ƙamshi manya"   Jarida ya ɗauka yashiga karantawa tare da watsar da duk wani tunani dake ransa.

Hadari ne sosai ya haɗu agarin kasancewar anacikin yanayi na damuna,  3:30 pm, fitowarsu sallan La'asar kenan.
Tana idar da sallan ta fito daga cikin masallacin, sosai take matuƙar son yanayi irin wannan,  ahankali sanyin iska ke busa ko ina, hijab ɗinta iska keneman yayewa, da sauri tasanya hannuwanta ta kameshi ƙam ajikinta.  Yanayin na fusgarta hakan yasa kai tsaye ta nufi wajen da garden ɗin makarantar yake.
Ƴan tsirarun ɗalibai ne awajen, kowa harkan gabansa kawai yake. Gefe da garden ɗin wasu kujeru ne masu kyaun gaske da aka tanada don zama,  tana zama aka soma yayyafi hakan yasa tatashi da sauri don komawa cikin makaranta.    Idanunta ne suka sauƙa akanshi, tsaye yake ya sanya duka hannuwansa acikin aljihun wandonsa, idanunsa ƙyam akanta fuskarsa ɗauke da beautiful smile,   cike da mamakin ganinsa tasaki murmushi tare da sanya hannu ta kare kanta, kasancewar zuwa lokacin ruwa ya fara sauƙa kaɗan kaɗan.   ganin haka yasanyashi takowa yazo gab da ita, cikin sexy voice ɗinsa yace.
"Kina tsoron ruwa ne?"
Murmushi tayi wanda har saida ya bayyana white teeth ɗinta, kanta ta kaɗa masa alamar "Eh" ruwane ya ɓarke me ƙarfin gaske hakan yasa lokaci guda ta ruɗe, shikansa ƙarfin ruwan yabasa mamaki, hannunta ya kama zuwa wani ɗan rumfa dake wajen, duk da shigarsu rumfar iya kawunansu kawai ruwan zai tare amma banda gangar jikinsu.   Cikin yanayi na tsoro ta naɗe hannayenta akan ƙirjinta,  kallonsa tayi da fuskarta dake jiƙe da ruwa.  Murmushi yayi mata tare da ɗage mata giransa ɗaya, itama murmushin tayi masa tare da sake takure kanta waje ɗaya, don bawai sun tsirane daga ruwanba,  har yanzu yana dukan jikinsu, tuni uniform ɗinta yajiƙe sunbi jikinta sun lafe, shikansa Pharouk gaba ɗaya ya jiƙe duk da cewa akwai denim Jacket ajikinsa hakan bai hanashi jiƙewa ba.   bakinta har rawa yake saboda sanyi. 
"Zieyaderh!" yaƙira sunanta akasalance.

Ɗago fuskarta tayi ta kalleshi,  idanunsa ya sauƙe akan beautyful lips ɗinta wanda suka jiƙe suke kuma ɗigar da ruwa,  wani irin tashi yaji tsikar jikinsa yayi, take lissafin kansa suka shiga kuncewa, wani irin saliva dake maƙale a maƙoshinsa ya haɗiya, sam bata ɗauke idanunta akansa ba, yanayin sanyin da take ji yasanyata lumshe idanunta tare da ɗan buɗewa alokaci guda, hakan da tayi baƙaramin kyau yaƙarawa face ɗinta ba, take yaji wani irin different feelings na sauƙa ajikinsa, ji yake kamar yajawota jikinsa ya bata professional kissing, amma mene sunansa idan yayi hakan?  jingina bayansa yayi da jikin bango tare da lumshe idanunsa, bugun zuciyarsa ƙaruwa take, wani irin maganaɗisun sha'awarta ne ke fusgarsa,  lokaci guda mood ɗinsa ya sauya.  Cikin zaƙuwa da tsayuwan Zieyaderh ta juyo ta kalleshi acikin yanayinta na shagwaɓa tace "Am tired!!"  Ahankali ya buɗe idanunsa wanda sukai ja ya sauƙesu akanta, wani irin yarrr taji ajikinta sakamakon kallon cikin idanunsa da tayi,  batasan irin wannan yanayin ba hakan yasa ahankali tace  "Are you okay?"

Akasalance yayi murmushin daya bayyana dimples É—insa.
"Yes am okay!" yafaɗa yana me ƙare mata kallo,  murmushi tayi masa sannan ta juya tacigaba da kallon ruwa sam ta manta bata maida hannuwanta ƙirjinta ta kare baiyanar dasukayi ba, don saboda yanayin sanyin da ake ciki yasanya tsikar jikinta mimmiƙewa, hakan yasa nipples ɗinta ma suka miƙe tsaye, har idan kayi  mata kallon tsab zaka iya ganinsu.   Sauƙan idanunsa akan ƙirjinta baƙaramin gigita masa tunani yayi ba, take yaji tunaninsa ya tsaya cak, da sauri ya ɗauke idanunsa daga kanta tare da sanya baki ya cije laɓɓansa. (Nasan team RAJ, zasuce inama da ita da Sooraj ne😝)    Wani irin tsawa da aka buga ne ya matuƙar firgitata har batasan sanda ta dawo baya da sauri ba, sambata kula ba ta faɗa jikinsa, ƙamƙame jikinta tayi ƙaƙam tare da rumtse idanunta.   "Innalillahi" kawai take ambata acikin zuciyarta don ta tsorata,  ashe ba ita kaɗaice ke ambatan hakan ba harda Pharouk don alokacin da bayanta ya mannu da ƙirjinsa baƙaramin ruɗewa yayi ba, har numfashinsa saida yashiga seizing na ƴan wasu minutes.    Hanneyansa dake rawa yaɗaura akan shoulder ɗinta, hakanne ya bata damar dawowa cikin hankalinta, da sauri ta matsa gefe, cikin wani irin kunya ta jawo hijab ɗinta ta rufe fuskarta.  "Me na aikata haka?" ta tambayi kanta cike da nadama.
Chapter 45 · 0% Book details