← Book details Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 91

Sashe 49

Sooraj Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Chab amma kuwa Garba kayi banzan hali, yanzun barinta zakayi ta koma, oh wato kaidai ba ka gaji da jin zagin da mutane ke mana agarinnan ba, karka manta fa duk  akan ɓatanta sunanmu ya ɓaci,  to babu inda zataje tananan tadawo kenan!" Inna Ma'u ta faɗa amasifance, don sam bata tsammaci haka ba.

"Haba Ma'u meyasa ne bazaki sanja ba, dan Allah Kibar yarinyarnan tayi tafiyarta, tafara karatu acan birni, tsayar mata da karatunta bashida wani amfani"  Malam Garba yafaɗi haka cikin ɗan lallashi saboda yasan halin kayansa sarai ba mutumci.

Cike da kumfar baki Inna Ma'u tace "Dole kace haka mana saboda ƴar kace, ai dama ninasan banice na haifeta ba, kuma zaman birni kam wannan algungumar ƴar taka ta gama yinshi....." Bata gama rufe bakinta ba taji sauƙar wani abu me ɗan nauyi akan cinyarta,   idanu ta zaro lokaci guda tare da haɗiye maganan dake bakinta, take yanayin fuskarta ya sauya daga ɓacin rai zuwa murmushi. "To Alhamdulillah, irin wanga farare bugun can babban birni, Hajiyan Birni Allah ya ƙara arziki!" Inna Ma'u tafaɗa bakinta har kunne,   kuɗine masu yawa Oummu ta aje mata don rufe bakinta, ai kuwa lokaci guda sai ga bakinnata ya rufu .    cike da nishaɗi tace.
"To yanzu sai yaushe zaku kuma dawowa?"    yanayin yanda tayi maganan tana me ƙoƙarin cusa kuɗin cikin lalitantane yabasu daria amma sai suka gimtse, ɗauke da ɗan murmushi Oummu tace.
"Nan bada jimawa ba Insha Allah, Nangaba kaÉ—an kema nasan zaki kaimana ziyara!"

"Sosaima kuwa, kice  ziyarori ma ba iyaka ziyara kaɗai ba, don fa basau ɗaya zanzo ba!!" Inna Ma'u tafaɗa cikin jin daɗi, dama ita abun duniya shine kanta.

Har wajen mota suka rakasu,  bayan motar  Oummu ta buɗe wanda ke shaƙe da kaya, Kamalu driver tasanya ya shiga ciro kayan yana kaiwa cikin gidansu Zieyaderh, kayan abincine kala kala da kuma wata leda dake ɗauke da kayan sawa, atamfofi da shadda irin na maza, godiya kam ba irin wanda baban Zieyaderh baiyi mata ba, duk da yanuna mata cewa kayan sunyi yawa, amma saitace masa ba komai,  koda ta bashi kuɗi ƙin amsa yayi babu yanda batayi dashi ba amma haka yaƙi amsa, Inna Ma'u kuwa daɗine ya isheta, musamman ma ganin ana shigar da kayan abinci cikin gidanta.  Haka su Zieyaderh suka baro cikin ƙauyen zuciarta cike da kewan babanta.    Har bacci tayi a hanya kafun su iso, gaba ɗaya zaman mota ba daɗi ji take duk jikinta yayi mata wani iri.

Suna isa gida kowa ɗakinsa ya wuce, don gaba ɗayansu agajiye suke,  da ruwan zafi tayi wanka kana tabi lafiyar gado.

Sunday. 
Yawanci duk ranan weekend atare suke cin abinci akan dinning,  tun 8 tatashi tayi wanka,  riga da sket na 1million stones tasanya wanda suka amshi jikinta sosai, tayi kyau.  Wani ɗan madaidaicin mayafi ta sanya ta rufe jikinta, a kitchine ta samu Oummu cike da ladabi ta gaida ta,  fuska ɗauke da fari'a Oummu ta amsa mata,  yauma kamar koda yaushe itace ta shirya gaba ɗaya abincin akan dinning.   Ƙamshin turaren Almustapha daya shiga hancinta shi yasanyata ɗago da kai ta ɗan kalleshi, ƙasa tayi da kanta tare da gaidashi,   amsa mata yayi yana me jan kujera ya zauna, sosai yau ɗin tayi masa kyau acikin shigarta,  duk da cewa bai taɓa ganin kwalliya akan fuskarta ba amma gaskiya tana da kyau sosai.  

Oummu da Almustapha ne suke taɓa hira kaɗan kaɗan yayinda ita kuma take serving ɗinsu,   tunaninsa ne kwance aƙasan zuciyartaz hakanan taji wani iri da bataga ya fito ba, tunaninta ne ya katse sakamakon  wani daddaɗan sanyin da taji yana ratsa jikinta, gefe guda kuma ni'imtaccen ƙamshinsa dake zautar da'ita ne yashiga cakuɗa da numfashinta. 
Sanye yake da blue crazy jeans and Blue t-shirt mai kyau da tsada ƙiran company'n D&G,  sosai yayi kyau kwarjininsa yasake bayyana, yayinda gashin kansa kuwa sai shinning yake, kujera yaja ya zauna, dakansa yayi serving kansa, wajen haɗa tea, ahankali yake sipping tea ɗin yayinda kansa ke ƙasa, yau babu waya ahannunsa amma duk da haka yi yake kamar hankalinsa baya garesu,   gaba ɗaya wajen ya ɗauki shiru,  kowa abincinsa yakeci yayinda akabar mutane biyu daga cikinsu da saƙar zancen zuci,  gaba ɗaya hankalinta yana garesa, so take ta ɗago idanunta ta kallesa amma fargaba ya hanata.
Tissue Oummu ta ɗauka ta goge bakinta tare da dubansu su dukansu, cikin nutsuwa tace  "Ina da buƙatar hankulanku  agareni dukanku!"  Almustapha ne ya fara aje cokalin dake hannunsa tare da duban Oummu, itama Zieyaderh ɗago kanta tayi ahankali tana me kallon Oummu'n, shikam ko motsawa baiyiba, kana bai kuma daina shan tea ɗinsa ba.

Gyara zama Oummu tayi tare da cewa.
"Sooraj da Almustapha inaso nayi maganannan ne agabanku saboda ko ba komai kamar yayye kuke awajenta, sannan awajenta zataji maganar  amatsayin sabuwace, saɓanin ku da kuka taɓa jinta"   ɗan numfasawa tayi kana tace..
"Zieyaderh!"

Tun kafun ta kammala maganganun nata ƙirjin zieyaderh ke bugawa, asanyaye tace.   "Na'am!"

Tashi Oummu tayi daga inda take zaune, tare da jawo wata kujera ta zauna gab da Zieyaderh'n, hannayen Zieyaderh Oummu ta kamo cike da son gamsar da ita tace.
"Haƙiƙa kowacce uwa tanaso ɗanta ko ƴarta su samu abokan zama na gari, burin kowacce uwa adunia shine ƴarta mace ta dace da mijin aure, haka ma kuma ɗanta namiji ya dace da macen aure,  tamkar ƴa haka na ɗaukeki Zieyaderh,  bazan taɓa son wani abu dazai cutar dake ba,  bazan miki dole ba, saboda kema kina da ra'ayi kamar kowa, halayyanki da kuma irin nutsuwarki yasanya naji ina kwaɗayin da ki ƙara zama acikin zuri'ata, duk da cewa munatare dake ayanzu, amma anan gaba ba lallaine mukasance tare ba, dole watarana aure zai ɗaukeki ya nesantaki damu, bazanyi baƙinciki ba idan kika samu adalin miji daga wani waje na daban, amma zanfi so ace daga cikin zuri'ata kika samu wannan adalin mijin, ba daga wani waje daban ba,  kamar yanda nace bazan miki dole ba, ba kuma umarni nake baki ba, saidai  ganin ya cancanta yasanya ni yin tunanin  haɗaki  aure da ɗana Almustapha!"

Dummmmmm tamkar ankwaɗa mata  katuwar guduma akan ƙirjinta haka taji, yayinda agefe guda kuwa  taji sauƙan kalaman Oummu acikin kunnuwanta tamkar almara, wani irin abune taji ya sarƙemata maƙoshi, take tasoma tari har  saida manya manyan  idanunta suka rikiɗe daga farare zuwa jajaye, da sauri Oummu ta ɗauko ruwa ta bata, cikin ikon Allah tanasha tarin ya ɗan lafa,  jingina bayanta tayi da jikin kujera tare dayin ƙasa da kanta, me Oummu ke faɗane? Kodai kunnuwanta ne basuji mata da kyau ba? Aure kuma da Almustapha? Waƴannan tambayoyin sune cike aranta, ganin komai take kamar ba da gaske ba.   Dafa shoulder ɗinta Oummu tayi cike da kulawa tace "Karki taɓa cutar da kanki Zieyaderh,  idan har kinaga hakan zai sa ki cutu to karki ɓoye ki sanardani, bazan taɓa miki dole ba, nayi hakanne kuma badon na cutar dake ba saidon ina kwaɗayin ganinki cikin zuri'ata, duk da nasan cewa banice na haifi Almustapha ba, amma inayi masa son da nake yiwa ɗana SOORAJ, kuma ina masa kwaɗayin zamowarki mata a garesa!!"

Hawayene suka cika idanun Zieyaderh, har takai ga sun soma sauƙa akan hannunta, wani irin bugawa zuciyarta keyi,  ita kanta batasan awani irin hali take ciki ayanzun ba, gaba ɗaya kalaman Oummu sunzama tamkar wani sinadari na bayyanar da raunin zuciyarta.

Ganin hawaye na É—iga daga idanun Zieyaderh yasa Oummu cewa.
"Ya isa daina kukan, idan kingama cin abincin kije ki kwanta, komai ya wuce nafahimci halin dakike ciki!" tana gama faɗan haka ta miƙe tare da soma ƙoƙarin barin wajen.  Da sauri Zieyaderh ta riƙo hannun Oummu, cak Oummu ta tsaya tare da juyowa,   ɗago  manya manyan idanunta tayi bakinta na rawa tace.
"Kiyi haƙuri Oummu ba ina kukane saboda banason abunda kikazomin dashi ba,  nayarda ke uwace agareni, saboda haka NA AMINCE!" taƙare maganar ƙirjinta na mata wani irin suka, yayinda gaba ɗaya gaɓɓan jikinta sukayi weak, so take tafashe da kuka me sauti, so take ta kalli koda ɓangaren da yake ne kozataji sanyi, so take yace wani abu,  to amma metakeso yace ɗin, itama kanta batasani ba.  
Cike da farinciki Oummu tashafa kanta cikin ƙaunar biyayya irin nata tace.
"Nagode sosai Zieyaderh nakuma ji daɗi da baki watsamin ƙasa a idona ba, haƙiƙa ke yarinyar kirkice, Insha Allahu Kuma zakiyi alfahari da wannan haɗin, kije ɗaki ki huta kinji!" Oummu ta ƙare maganar cike da lallashi. Babu musu kamar wacce ƙwai ya fashewa ajiki haka ta tashi daga zaunen da take, har yanzun bazata iya ɗaga idanunta ta kalli ko wanne daga cikinsu ba, cikin ƙwallan da suka sake cika idanunta ta haura sama daɗan sauri burinta taje tayi kuka kozataji sauƙi aranta. 

Tunda suka fara maganar har kawo iyanzu bai koda ɗago kansa ya kallesu ba,  sannan baidaina abun daya keyi ba, da kaɗan kaɗan yake sipping tea ɗin da tsabar zafi har tiriri yake, hayaƙin dake fita acikin kofin tea ɗin shine ya sanya gaba ɗaya fuskarsa ta ɗanyi zufa, sam baijin wannan zafin shayin akan harshensa hasalima tamkar wanda yakeshan ruwan randa haka yaji test ɗin shayin ya sauya a bakinsa.

Kallon Oummu dake tsaye tana murmushi  Almustapha yayi jikinsa asanyaye yace
"Oummu kinaga kamar ba matsala kuwa?"   Still murmushi Oummu tayi tare da dafa shoulder ɗinsa cikin kulawa tace.
"Babu wata matsala Almustapha ka kwantar da hankalinka, kaidai ka shirya bikinka yakusa zuwa Insha Allah"  Tana gama  faɗan haka ta wuce zuwa ɗakinta.
Murmushi Almustapha yayi tare da sanya hannu ya dafa saitin zuciyarsa, har acikin ransa yaji wani irin farinciki,  da sauri yatashi ya nufi ɗakinsa sam yama manta da Sooraj dake zaune agefensa. 

Shikaɗai ya rage zaune akan dinning ɗin, ahankali ya aje cup ɗin dake hannunsa, tare da ɗaukan tissue ya goge bakinsa,  miƙewa tsaye yayi kai tsaye ya wuce ɗakinsa,  yana shiga ya soma rage kayan jikinsa, baijin zai samu relief idan ba shower ya sakarwa kansa ba, bathroom ya shiga tare da kunna shower, tsayawa yayi saitin shower ɗin ruwa na dukan kai da jikinsa, ahankali yake fidda wani numfashi me zafi.
Chapter 49 · 0% Book details